• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Wednesday, July 30, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Hotuna: Shin Adamar Kamaye ta yi ‘wuf!’ ne? Hira da jarumar

by MUHAMMAD LAWAN RANO
September 12, 2021
in Labarai
0
Hajiya Zahra'u Saleh da Mudassir Muhammad

Hajiya Zahra'u Saleh da Mudassir Muhammad

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

WASU hotuna da su ka karaɗe soshiyal midiya a yau sun haifar da raɗe-raɗin cewa jarumar nan ta Kannywood, Hajiya Zahra’u Saleh, wadda aka fi sani da Adama matar Kamaye, ta yi miji.

A hotunan, an ga Zahra’u tare da wani matashi a tsarin miji da mata, wanda hakan ya sa ake zaton ko jarumar ta samu yaron mijin aure ne samfurin zamani, wato ‘wuf!’ 

Bayan ɓullar hotunan, mutane sun ta yi wa Zahra’u addu’ar sanya alheri, yayin da wasu ke tambayar idan jarumar cikin diramar ‘Daɗin Kowa’ ɗin ta yi aure ne a asirce.

To amma ba haka abin ya ke ba, kamar yadda mujallar Fim ta binciko.

Don tabbatar da gaskiyar labari, mujallar Fim ta ji ta bakin Hajiya Zahra’u Saleh, inda ta ce, “Wannan hotunan na biki ne wanda amarya da ango su ke ɗauka kafin biki, wato ‘prewedding’, amma kuma a cikin fim.

Wannan kallon ba na ‘wuf!’ ɗin gaske ba ne, inji Adamar Kamaye

“Wallahi ba aure na yi ba. Wannan hotunan fim ɗi na ne wanda zai fito kwanan nan mai suna ‘Matar Yaro’. To sakamakon haka ne ya sa mu ka fara motsa jam’iyya da yaɗa manufar mu ta cikin wannan hoto da mu ka ɗauka sannan mu ka fara sakin sa duniya ta gani.”

Ta ƙara da cewa, “Fim ɗin zai kasance mai dogon zango kuma ni ce wacce na ɗauki nauyin shirya abu na da kai na.”

Jarumar ta yi farin cikin jin yadda ake ta yi mata fatan alheri. Ta ce, “Na ji matuƙar daɗi ganin yadda mutane su ka fara karɓar wannan fim tun kafin ya fito kasuwa. To hakan ya na nuna alamun kwalliya za ta biya kuɗin sabulu. Don haka su jira, nan ba da jimawa ba fim ɗin zai fito.”

Game da yadda masoyan ta su ke yi mata fatan ta yi aure, ta ce la shakka ta kusa yin auren.

Zahra’u ta ce, “Kamar yadda kowa ya ke ta magana, da man kuma ai duk ɗan aure ba ya ƙin aure, kuma shi aure ai lokaci ne, idan Allah ya kawo shi, aure da likkafani ai ba a tanadin su, ko da kuɗi ko babu idan Allah ya ƙadarta dole za ka yi shi.

Jaruman ‘Matar Yaro’, Zahra’u da Mudassir, sun yi hotunan ne don tallata shirin

“Don haka ina nan da niyyar yin auren ma; kawai dai a jira lokaci.”

Wakilin mu ya gano cewa sunan jarumin da su ka yi hotunan da shi shi ne Mudassir Muhammad, kuma an ce ɗan asalin garin Dutsin-ma ne na Jihar Katsina.

Copyright © Fim Magazine. All rights reserved
www.fimmagazine.com

Loading

Tags: Adamar KamayeaureDadin Kowahausa filmsKannywoodMatar YaroMudassir MuhammadZahra'u Saleh
Previous Post

Ta dalilin waƙa ta mutum uku sun musulunta – Habu Taɓule

Next Post

Rasuwar Ahmad Tage asara ce ga Kannywood, inji MOPPAN da ‘yan fim

Related Posts

Wani mai suna Bashir Abdullahi ya damfare ni miliyan bakwai da rabi, inji Halisa
Labarai

Wani mai suna Bashir Abdullahi ya damfare ni miliyan bakwai da rabi, inji Halisa

July 28, 2025
Gaskiyar magana kan ji-ta-ji-tar ‘mutuwar’ Aminu Ala
Labarai

Gaskiyar magana kan ji-ta-ji-tar ‘mutuwar’ Aminu Ala

July 28, 2025
Labarai

KADIFF 2025: Uganda ta fi yawan finafinai a bikin baje-kolin na Kaduna – Israel Kashim Audu

July 25, 2025
Labarai

Karya dokar liƙi: Kotu ta ɗaure G-Fresh da Hamisu Breaker tsawon wata biyar-biyar

July 24, 2025
‘Yan Kannywood sun kaɗu da rasuwar Abdoulfatah Omar
Labarai

‘Yan Kannywood sun kaɗu da rasuwar Abdoulfatah Omar

July 23, 2025
Allah ya yi wa mahaifiyar darakta Salisu Mu’azu rasuwa
Labarai

Allah ya yi wa mahaifiyar darakta Salisu Mu’azu rasuwa

July 17, 2025
Next Post
Marigayi Ahmad Aliyu Tage

Rasuwar Ahmad Tage asara ce ga Kannywood, inji MOPPAN da 'yan fim

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!