SHARU Habu Taɓule shahararren sha’iri ne mai waƙar bege wanda ya yi fice wajen yin barkwanci a cikin waƙe. Bugu da ƙari, jarumi ne a masana’antar shirya finafinai ta Kannywood.
Tauraruwar sa ta haska sosai musamman saboda yadda ya ke gudanar da waƙoƙin yabon Annabi (s.a w.) da wani salo da ya ja hankalin mutane a soshiyal midiya.
Sharu Habu Taɓule, mai laƙabin ‘Ba ma kunyar rawa ko a gaban surukan mu ne’, ya tattauna da mujallar Fim kwanan baya a Kano inda ya bayyana cewa ya shigo harkar fim ne ba don faɗakarwa ba sai dai don sana’a. Matsayar sa ita ce ‘yan fim su daina kiran kan su masu faɗakarwa, a’a su masu sana’a ne kamar kowa.
A tattaunawar, sha’irin, wanda kuma jarumi ne da ya fito a wasu finafinai, ya faɗi yadda aka yi ya tsinci kan sa a Kannywood da irin ƙalubalen da ya fuskanta, da tunanin sa kan irin kallon da jama’a su ke yi masa.
FIM: Da farko, za mu so mu ji tarihin ka a taƙaice.
HABU TAƁULE: Assalamu alaikum. Suna na Sharu Habu Taɓule mai laƙabin ‘Ba ma kunyar rawa ko a gaban surukan mu ne’. An haife ni a unguwar Ciromawa Ƙofar Wambai, kusa da Lungun Sharifai. A nan na tashi na yi makarantar Islamiyya na yi firamare mai suna Festival. Bayan na kammala, na koma makarantar sakandiren Kuka da ke Kwakwaci, wanda daga nan kuma mu ka fara gwagwarmaya ta kasuwanci tunda mu mun gaji dukanci wanda a haka aka raine mu.

FIM: Ya aka yi aka tsinci kan ka a cikin wannan fage na yabo da kuma nishaɗantar da al’umma?
HABU TAƁULE: To a gaskiya ni da man da ina yaro na taso ina da son nishaɗi tun a unguwa. Sannan a lokacin nan na yi rashin ji wanda a da idan ma ana so a sa yara su yi shiru ina yi musu tatsuniya da sauran nau’in wasan yara duk a wannan lokacin nan ina kwatantawa. Kuma ya zamana na yi fice a wannan lokaci.
Na kuma tsunduma cikin nishaɗantarwa ne sakamakon waƙoƙin yabon Annabi da na ke, wanda tun ana waƙar ba a sa mata kiɗa mu na yi mu na tafa hannun mu, daga nan na fara har zuwa yau.
FIM: Wane abu ne Habu Taɓule ya yi wanda ya sa duniya ta san shi duba da cewa wasu yanzu ne su ka san Habu Taɓule?
HABU TAƁULE: A gaskiya ni ba sabon mawaƙi ba ne; na jima ina yi kuma Allah ya tashi bayyana ni a wannan lokaci aka kuma san ni. Ni ba mawaƙi ba ne na iya yabo, har da faɗakarwa da nishaɗantarwa, abin da ya kai har ana gayyatar mu zuwa gidan suna da ɗaurin aure domin mu nishaɗantar da jama’a. Ba na mantawa, wata rana na zo haka ina yin majalisi, ina yin rawa, sai wasu manyan mutane haka su ke ɗan riƙe baki su na faɗin ko ba ni da kunya ne? To, da jin haka sai a cikin waƙar da na ke sai na ce, “Ai ba ma kunyar rawa ko a gaban surukan mu ne!” To wannan abin da na faɗa sai ya jawo ce-ce-ku-ce a gari: ya za a yi a ce mutum zai yi rawa ko da kuwa a gaban surukan sa? Saboda an san yadda surukai su ke da kunya kuma a ce ya na iya yin rawa a gaban su! To wannan abin sai ya ba wa mutane sabon saƙo da na zo da shi.
Ina iya tuna wani bawan Allah kuma surukin mu ne, sai mu ka zo ƙofar gidan sa mu na majalisi. Mutane su ka fito kallo da iyaye da kowa don a ga wai zan iya yin rawar kuwa a gaban surukan nawa? Ai kuwa sai su ka ga rawar da na ke ma ta fi kalar kowacce irin rawar da na ke yi saboda su tabbatar da cewa ba da wasa ake ba! To, ka ji yadda na samu ɗaukaka a waƙa sanadiyyar wannan waƙar da na ke yi ta ‘Ba na kunyar rawa ko a gaban surukai na ne’.
FIM: A kwanan nan an ga hotunan ka da ‘yan Kannywood a tallar wani fim. Shin ko mecece alaƙar ka da wannan masana’anta ta Kannywood?
HABU TAƁULE: Kamar yadda na gaya ma, Allah shi ne mai yin yadda ya so a san da ya ga dama. Lokacin da na fara wannan harkar ta nishaɗantar da jama’a, na ɗan sassamu ƙalubale kala-kala da yawa: wani ya zage ni, wani ya ce mani mahaukaci, wani fa shashasha zai ce mani, wani ma babban banza ya ke kira na. To amma idan Allah ya tashi ɗaukaka ka ba ya shawara da kowa.
Sannan alaƙa ta da ‘yan Kannywood shi ne kusan duk wasu ƙungiyoyi da su ka dinga kyara ta ni ba inda ban samu tsangwama ba sai a Kannywood. Allah ya sa ni tun a da ina sha’awar su domin ina kallon su, ina bibiyar su, kuma ni masoyin su ne. To da Allah ya tashi juyin sa, ni ma sai ‘yan Kannywood su ke ƙauna ta, duk abin su sai su jawo ni su sa ni a ciki. Ka ga kuwa duk mutumin da zai yi abu ya saka ka, ya za a yi kai ba za ka shiga cikin abin sa ba? To, daga nan sai na shiga cikin Kannywood dumu-dumu.

Bugu da ƙari, har yanzu a cikin Kannywood ba wanda mu ka taɓa haɗuwa da shi fuska da fuska ya nuna ba ya ƙauna ta ko ya kyari abin da na ke yi. Su ne waɗanda su ka fara riƙe ni hannu biyu-biyu. Misali irin manyan jarumai tsofaffi da matasa, musamman Iyan-Tama, ya zo mu ka zauna ya gaya mani wasu maganganu waɗanda na ji daɗin su ƙwarai da gaske. Ina yi masa fatan alkairi da sauran su.
A ɓangaren yin fim kuma, na yi finafinai da dama waɗanda ba za su ƙirgu ba. Wasu sun fito, wasu kuma su na kan fitowa, kuma kala-kala daban-daban. Na barkwanci ne da dama har ma da masu dogon zango, su na nan fitowa.
Sannan masoya na su tara a gaba, za su ci gaba da ganin finafinai na nan ba da jimawa ba sabbi.
FIM: Zuwa yanzu waɗanne irin nasarori ka samu waɗanda ba za ka iya mantawa da su ba?
HABU TAƁULE: Nasarori ga shi mu na kan samu ma. Zan ce a kwanan nan akwai wata ƙungiya da ta taso tun daga babban birnin tarayya Abuja, ta yo wakilcin wasu manyan mutane kamilai, wasu sun haife ni, wasu ma sun yi jika da ni, su ka zo garin Kano don su girmama ni. Wannan abu ya faranta min rai kuma nasara ce babba a gu na. Sannan aƙalla zuwa yanzu na karɓi ‘awards’, wato lambar girmamawa sama da ɗari kama daga na ‘yan Kannywood, Kaduna, Abuja, Lagos da dai sauran guraren da ban ambata ba. Ka ga wannan ma nasara ce; ban da kuma alkairai iri-iri har ma da addu’o’in mutane da su ke yi min a ko da yaushe.
Sannan ba zan manta ba, akwai wani babban likita a Asibitin Aminu Kano wanda ya na ba wa marasa lafiya shawarwarin abin da za su dinga yi don samun lafiyar su. A ciki sai ya gaya musu cewa, “Akwai wani mawaƙi da ya fito mai suna Sharu Habu Taɓule, ku dinga yawan kallon bidiyon sa domin samun nishaɗi da sauran su.”
Na kuma haɗu da manyan mutane kama daga fannin siyasa, kasuwanci da sauran su.
Kazalika akwai ma ta wanda ba Musulmai ba ne, ta dalilin waƙar da na yi wa Faɗima ‘yar Manzon Allah su ka musulunta su uku, wanda a garin Jos an sami mace ɗaya sannan a Legas an sami maza biyu.

Sannan ta dalilin waƙa an yi min sarautu guda uku; an min Sarkin yaƙin Sarkin Yaƙin Ringim, sannan akwai wata sarauta da aka min wanda ko naɗin ma ba a yi ba sai nan gaba. Wannan ma ai ka ga nasara ce babba.
FIM: Bayan nasarori da aka samu, dole akwai ƙalubale. Shin wane ƙalubale Habu Taɓule ya samu a cikin wannan tafiya tasa?
HABU TAƁULE: Ƙulubalen da na fuskanta bai wuce wanda na gaya ma a baya ba: mutane su na ce mani, “Da girman ka ka ke rawa!” Ko a ce da ni, “Ai bai kamata ka shiga siyasa ba,” ko wasu ka ji su na cewa, “Kai fa yabon Annabi ka ke yi!” To shi mai yabon Annabi ba a so ya ci miya mai daɗi? Sannan shi ba a so ya shiga siyasa? Ai ni a gu na mutum ya na da ‘yancin yin duk abin da ya ga dama in dai bai saɓa wa shari’ar Muslunci ko wani tsarin dokar ƙasa ba.
Akwai kuma lokacin da malamai za su kira ni su ce mani ai wannan abin da na ke yi bai dace ba da girma na. Kuma lokacin da ina ƙasida ba wanda ya taɓa kira na ko ya ba ni shawara a kai, sai yanzu da na maida abin sana’a. Yanzu kamar Kannywood ai sana’a ce, shi ya sa in ɗan Kannywood ya ce mani wai faɗakarwa mu ke sai ya ɓatan rai ma; a’a sana’a ka ke yi. Don haka mu na gaya wa mutane mu a Kannywood sana’a mu ke yi, ba tarbiyya ba. Ba wani zancen tarbiyya amma a cikin sana’ar ka; za ka yi abin da ya dace ka taimaki Musulunci, ka taimaki yaran ka har ma ka taimaki aƙidar ka. Amma dai sana’a ce. Fim sana’a ce Ina ƙara jaddadawa: rawa ma sana’a ce! Don haka ni da na shigo fim ba faɗakarwa na zo yi ba, sana’a na shiga zan yi.
FIM: A duk lokacin da ka haɗu da masoyan ka, wanne abu ne su ka fiye tambayar ka a kai kuma ka gaji da amsawa?
HABU TAƁULE: Yauwa! Tambayar da na gaji da amsa ta ita ce tambayar wai idan na ce da in ƙi faɗi ma gara a ce ma na ma ce me ya sa ka ke faɗin haka? Sai kuma tambayar da ita ma ake yawan yi min, ita ce wai yaran nan na baya na wanda idan ina rawa na tafi zan faɗi biyan su na ke, sannan ba na tsoron su kauce na faɗi? Wani kuma fata ya ke ina ma ya na cikin waɗanda su ke riƙe ni idan zan faɗi saboda abin ya na burge shi! To, ka ji tambayoyin da na ga ji da amsa su.

FIM: Me za ka ƙarƙare da shi a ƙarshe?
HABU TAƁULE: Abin da zan ƙarƙare da shi shi ne bai wuce na yi kira ga matasa ba da su tashi su yi karatu sannan su kama sana’a, don a duniya na tsani in ga matashi ya na shaye-shayen ƙwayoyi. Abin ya na ɓata mani rai. A har kullum ina da burin ganin matasa su na neman kuɗi, wato sana’a; o in ga mutum ya duƙufa da karatu, abin ya na faranta min rai. Allah ya shiryi matasan mu, ya yi musu albarka, ya kuma zaunar mana da ƙasar mu lafiya, amin.
SANARWA DAGA EDITA: Duk mai buƙatar ya tuntuɓi Sharu Habu Taɓule sai ya kira shi ta wannan lambar: 07033355001
Copyright © Fim Magazine. All rights reserved.
www.fimmagazine.com
![]()







