• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Wednesday, May 6, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Hotunan ‘aure’ a Kannywood: Me ya sa mutane ba su ganewa?

by DAGA ABBA MUHAMMAD
September 28, 2022
in Tsokaci
0
Umar Gombe da Hauwa Ayawa a hoton da su ka ɗauka don latsa mutane

Umar Gombe da Hauwa Ayawa a hoton da su ka ɗauka don latsa mutane

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

HAR kullum jama’ar gari masu bibiyar ‘yan fim ba su iya gane wasu abubuwa da aka saba yi a masana’antar Kannywood. Yau kusan shekara uku zuwa huɗu da ake ɗaukar hotunan kafin aure (prewedding pictures) na ‘yan fim idan akwai buƙatar a yi amfani da su a wani fim ko kuma irin shagalin da Ibrahim Sharukhan ya ke haɗawa don tallar ayyukan sa na mai gabatar da biki (MC) da kuma tallata wurin taron sa (event centre). Kuma da ma shi ne wanda ya fara yin irin waɗannan hotunan a Kannywood.

A kwana-kwanan nan, mujallar Fim ta ba da labari a kan hotunan mawaƙi Ado Gwanja da jaruma Momee Gombe, waɗanda aka yi ta yaɗa cewa za su yi aure. Daga ƙarshe mujallar ta tuntuɓi Gwanja, inda ya shaida mata cewa a fim ne.

A baya mun yi ire-iren waɗannan labaran a kan jaruman da aka ga sun yi irin waɗannan hotuna. Mun ba da labarin na Sadiq Zazzaɓi da Maryam Booth, Ali Nuhu da wata waddda ba ma ‘yar fim ba ce, wanda a lokacin an fi gaskata nasu domin ba a san fuskar ta ba. 

Kamar da gaske! Hauwa Ayawa da Umar Gombe

A cikin kwanakin nan kuma, an fara yawo da irin waɗannan hotuna da ake yi na kafin aure na jarumi Umar Gombe da jaruma Hauwa Ayawa (Azima ‘Gidan Badamasi’).

Yanayin yadda su ka ɗauki nasu hotunan ba kamar na sauran ba ne, domin duk wanda ya ga hotunan zai ɗauka auren za su yi.

Da farko ban so yin wannan rubutun ba, saboda a tunani na zuwa yanzu mutane sun gane yadda abin ya ke, tunda an sha yi, ba sau ɗaya ba, ba biyu, ba uku ba.

Sai dai kuma yawan kiran waya da na ke samu ana tambaya ta gaskiyar lamari a kan hotunan, ya sa na yi rubutun domin mutane su tabbatar da cewa hotunan ba na auren gaske ba ne. Har ta kai ga wani darakta da abokin sa, wanda shi mawaƙi ne, su ka yi takakkiya su ka same ni don jin gaskiyar abin da ke faruwa.

Hoto domin tallata shirin ‘Gidan Badamasi’

Su dai waɗannan hotuna, an ɗauke su ne domin shirin ‘Gidan Badamasi’ da ake nunawa a tashar Arewa 24, wanda a ranar Alhamis, 6 ga Oktoba, 2022 za su fara nuna sabon shirin. Ko shi daraktan shirin, Falalu A. Ɗorayi, da ya wallafa hotunan, cewa ya yi, “Allah ya sanya alkhairi Umar Gombe & Hauwa Ayawa, komai lokaci ne,” sai kuma ya rubuta: “6 October, 2022,” wadda ita ce ranar da za su fara nuna sabon shirin.  Wannan ita ce gaskiyar lamari a kan hotunan.

Loading

Tags: Ado GwanjaAli NuhuArewa 24Azima Gidan Badamasifake newsFalalu A. ƊorayiHauwa Ayawahotunan kafin aureKannywoodlabarin ƙaryaMomee Gombeprewedding picturesUmar Gombeyaudara
Previous Post

Yadda aka yi jana’izar Umar Yahaya Malumfashi Bankaura

Next Post

Mutuwar Bankaura: Mun yi rashi mai wuyar cikewa a Kannywood – Isa Ja

Related Posts

Aure Da Saki A Fim: Gangan Ko Gaske?
Tsokaci

Aure Da Saki A Fim: Gangan Ko Gaske?

March 7, 2025
‘Arewa Republic’. Kun gani ba?
Tsokaci

‘Arewa Republic’. Kun gani ba?

February 10, 2025
Rukuni huɗu na masu kallon fim ɗin Hausa
Tsokaci

Rukuni huɗu na masu kallon fim ɗin Hausa

February 7, 2025
Barka Da Zagayowar Ranar Haihuwar Ka Miji Na
Tsokaci

Barka Da Zagayowar Ranar Haihuwar Ka Miji Na

September 1, 2024
Dakta Aliyu U. Tilde
Tsokaci

Arewa: Tsakanin Ilimi Da Sana’a

June 12, 2024
Gwamna Abba Kabir Yusuf
Tsokaci

Shawara ga Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf

June 10, 2024
Next Post
Marigayi Alhaji Umar Yahaya Malumfashi

Mutuwar Bankaura: Mun yi rashi mai wuyar cikewa a Kannywood - Isa Ja

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!