DA safiyar yau Laraba aka gudanar da jana’izar fitaccen jarumin Kannywood, Alhaji Umar Yahaya Malumfashi (Bankaura), wanda Allah ya yi wa rayuwa a daren jiya.
Bankaura, wanda ake yi wa laƙabi da Ka-fi-gwamna, ya rasu ne a wani asibiti mai suna Pinnacle Special Hospital, Kano, bayan ya shafe tsawon watanni ya na fama da rashin lafiya.
An gudanar da jana’izar a gidan sa da ke unguwar Hotoro Tsamiyar Boka da misalin ƙarfe 9 na safe.
Taron jana’izar ya samu halartar jama’a masu yawan gaske daga ciki da wajen masana’antar Kannywood.
An kai shi makwancin sa a maƙabartar Tarauni.

Cikin fitattun jaruman da su ka halarta akwai Alhaji Isa Bello Ja, Alhaji Hamisu Lamiɗo Iyan-Tama, Malam Alhassan Kwalle, Malam Aminu Baba Ari, da Malam Ado Ahmad Gidan Dabino.
Marigayin dai tsohon ɗan wasan kwaikwayo ne na talbijin da rediyo sama da tsawon shekara arba’in, sannan tsohon ma’aikaci ne a Hukumar kula da Shige da Fice ta Nijeriya (Customs) inda ya yi ritaya a cikin 2020.
Iyalin sa sun faɗa wa mujallar Fim cewa ya rasu ya na shekara 66, ya bar mace ɗaya da ‘ya’ya 15 – mata huɗu, maza goma sha ɗaya.
Bayan an yi jana’izar, mujallar Fim ta ji ta bakin ɗaya daga cikin ‘ya’yan sa, wato Abubakar Umar Yahaya, kan wannan babban rashi da mu ka yi.
Abubakar ya ce: “To, gaskiya mu a matsayin mu na ‘ya’yan sa mun samu kulawa sosai, irin kulawar da mahaifi nagari ya ke yi wa ‘ya’yan sa. Ya ba mu tarbiyya, ya ba mu ilimi, ya koyar da mu zumunci a cikin ‘yan’uwa, da sauran mutane na kusa da shi.
“Kuma ya haɗa kan mu a matsayin mu na ‘ya’yan sa duk da yake mun kasance ‘ya’yan mata uku ne mu ‘ya’yan sa Ya koya mana haɗin kai da girmama juna.

“Mu na fatan Allah ya jiƙan mahaifin mu, don mun yi rashin da ba za mu taɓa mantawa da shi ba.”
A game da irin ciwon da baban nasu ya yi, Abubakar, wanda ya na cikin waɗanda su ka yi zaman jinyar sa, ya ce ya sha fama da rashin lafiya wanda ya kai shi ga kwanciya na tsawon wata shida kafin Allah ya karbi abin sa.
Da mujallar Fim ta tambaye shi yanayin rashin lafiyar, sai ya ƙara da cewa: “Tun a watan Ƙaramar Sallah ya ke kwance daga lokacin da jikin sa ya matsa masa. Da farko an je asibiti ba a gano abin da ya ke damun sa ba, sai aka dawo gida aka ci gaba da magani.
“Sai kuma daga baya aka sake yin bincike, sai aka gano wani ƙari ne ya fito a mafitsarar sa, don haka sai aka shirya za a yi masa aiki. Sai kuma aka gano shi wannan ƙarin idan ya na mataki na 40 ne za a iya cire shi, to shi kuma nasa ya kai har 200 da wani abu, don haka su ka ce sai an fara yin wani aiki a mataki na farko sannan za a yi na biyun da shi ne za a cire.
“To kuma an yi na farko, kafin a kai ga yin na biyun, sai Allah ya yi masa cikawa.”
To, mu ma a mujallar Fim mu na addu’ar Allah ya jiƙan sa, ya kyautata makwancin sa, amin.

