TSOHON Shugaban Ƙungiyar Masu Shirya Finafinai ta Arewa (AFMAN), Alhaji Hamisu Lamiɗo Iyan-Tama, ya yi ƙarar wani mutum da ke sharhi a Facebook a kotu kan zargin ya ɓata wa ‘yan fim suna.
Wanda ake zargin, Imam Aliyu Indabawa, ya yi wani rubutu ne a kafar ta sada zumunta kan ‘yan fim, ya na mai iƙirarin cewa su na ɓata tarbiyyar mutane, don haka bai kamata ‘yan siyasa su yi masu kyautar alheri ba.
Sakamakon rubutun nasa, Iyan-Tama, wanda fitaccen jarumi ne kuma mai shirya finafinai, ya shigar da ƙara a Babbar Kotun Jihar Kano da ke garin Kano.
A takardar ƙarar mai lamba K/2421, wadda mujallar Fim ta samu kwafen ta, kotu ta buƙaci Indabawa da ya bayyana a gaban ta ko ya tura lauyoyin sa a safiyar ranar 13 ga wata.
Sai dai mujallar Fim ta lura da cewa an yi kwaɓa a wajen rubuta kwanan wata a kan sammacin.
Jim kaɗan bayan an kai masa sammaci a ranar Lahadi, 4 ga Satumba, 2022, Indabawa ya yi bayani a Facebook mai taken “‘Yan Fim Su Na Ƙoƙarin Ganin Baya Na”, inda ya ce: “Yanzun nan aka yi sallama da ni bayan na fito ne sai mutumin ya ce daga kotu ne aka aiko shi waje na da sammaci. Ya ba ni wasu takardu cewa wai wani mutum mai suna Hamisu Lamiɗo Iyan-Tama ne ya yi kara ta, saboda na yi rubutu kan ‘yan fim na ce su na lalata tarbiyya, wanda shi ma ɗan fim ne, sannan kuma na yi rubutu na nuna rashin jin daɗi na san da wani Sanata mai suna Barau Jibril ya raba wa ‘yan fim motoci, babura, kyamarori, kwamfuyutoci da kuɗaɗe alhalin mabuƙata suna mutuwa a asibiti saboda rashin kuɗin magani, wasu na mutuwa saboda yunwa. Sannan ina goyon bayan Gwamna Ganduje ina adawa da Barau Jibril san da shi Barau din ke takun saka da Baba Ganduje a ƙungiyar su ta G7 Wannan shi ne kaɗai laifi na.
“Bin tafarkin Annabi (SAW) na umarni da kyakkyawa da hani da mummuna da yaki da rashin tarbiya ya zama laifin da har ake kokarin a ga bayan mai aikata shi.
“Zan bibiyi takardar sammaci insha Allahu, tana da yawa sosai. Zan san matakin da ya dace na dauka.
“Allah ya shiga lamuran mu.”
Masu abota da Indabawa a Facebook da dama sun yi tsokaci kan maganar; wasu na goyon bayan sa, wasu kuma na cewa abin da furodusan ya yi shi ne maganin ire-iren su.
Wani mai sharhi, Nuhu Magaji Hassan, ya ce: “Allah ya fi su, ka na tare da Allah, ba za su iya cutar da kai ba in-sha Allah. Ba shi ma da kunya ne wallahi, don ba ƙarya ba ne abin da ka faɗa, in da ya na da kunya da ɓuya ma ya kamata ya riƙa yi ba ƙoƙarin kai ƙara a kotu ba.”
Shi kuwa Abdulrahman M. Bello, cewa ya yi: “Har yaushe ɗan fim ya yi wannan gatan da har wai za a kai ƙarar wanda ya yi rubutu kan gaskiya? Tabbas, ‘yan fim na lalata tarbiyya kuma da yawan su ba mutanen arziki ba ne. Kuma wallahi ba za mu ci gaba da zura ido waɗannan abubuwan na faruwa ba.”
A nasa ɓangaren, wani mai sharhin, Comrade Jamilu Wahada, ya rubuta a shafin wanda ake ƙarar cewa: “Sharri ka yi musu. Ya dace su ɗauki matakin shari’a a kan ka. Ina ruwan ka da harkar su ta wasan Hausa? Mai ra’ayi shi ne zai yi kallo ko ya saurara.
“Wannan zalunci ne da rashin adalci da ɓatanci ka ce ‘yan wasan Hausa su ne su ka lalata tarbiyyar al’umma. Ita tarbiyya daga gida ake koyar ta; idan ka ga mutum ya lalace, sakacin waɗanda Allah ya ɗora ikon kula da tarbiyya ne, amma ba wai ‘yan wasan Hausa ba.
“Idan za ka yi musu adalci, tun kafin shigowar wasan Hausa ƙasar Hausa tarbiyya ta ke a lalace. Rashin adalci ne zai sa ka ce su ne su ke lalata tarbiyyar al’umma.”

Da ya juya ga ‘yan fim, sai Wahada ya ce masu: “Ku ɗauki mataki a kan sa saboda kada wani ya sake yi muku irin wannan cin zarafin. Idan ku ka bari har minbarin Juma’a za a hau a yi maku sharri da ƙage; yawo sai ya gagare ku; gara ku yi wa tufkar hanci.”
Ya ƙara faɗa wa wanda ake ƙarar cewa: “Hani da kyakkyawan aiki, wa za ka saka wa za ka hana? Kai malami ne ko kai hukuma ne da za ka dinga yi wa mutane sharri da ƙage? Ba daidai ba ne, ba abin da ka ke yi.”
Shi kuma Buhari Ya’u Gumel, cewa ya yi irin su Iyan-Tama “su ne maganin marar kunya ɗan bana-bakwai.”