JARUMIN barkwanci a Kannywood, Malam Sani Ibrahima, wanda aka fi sani da Ɗan Gwari, zai aurar da ɗan sa, Mannir.
Za a ɗaura auren Mannir Sani Ɗan Gwari da sahibar sa Khadija Lirwanu a ranar Juma’a, 2 ga Fabrairu, 2024 da misalin ƙarfe 2:30 na rana a masallacin Juma’a da ke layin Ladi Wudil, unguwar Rigasa, Kaduna.

Mujallar Fim ta ruwaito cewa Ɗan Gwari ya na gayyatar kowa da kowa zuwa wurin ɗaurin auren, kamar yadda ya faɗa a gajeren bidiyon da ya yi ya na tura wa tare da katin gayyatar.
Sannan ya buƙaci a taya ango da amarya addu’a, musamman ga waɗanda ba su samu damar halartar ɗaurin auren ba.
Allah ya kai mu ranar da rai da lafiya.
![]()







