• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Sunday, July 20, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Jarumin barkwanci Yamu Baba ya zama angon Hauwa’u

by ABBA MUHAMMAD
April 28, 2024
in Ranar Murna
0
Jarumin barkwanci Yamu Baba ya zama angon Hauwa’u

Yamu Baba da Hauwa'u

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

JARUMIN barkwanci a Kannywood, Ibrahim Abubakar Ibrahim, wanda aka fi sani da Yamu Baba, ya yi bankwana da kwanan shago a jiya Asabar.

An ɗaura auren sa da sahibar sa, Hauwa’u Musa Abubakar, da misalin ƙarfe 11:00 na safe a gidan Alhaji Ibrahim Mai Taya da ke Layin Ɗanmaraya, a Jos, Jihar Filato, a kan sadaki N300,000.

Sani Ahmad, ango Yamu Baba, Tynking Mai Gashi da Ahmad Shanawa a wurin ɗaurin auren

Waɗanda su ka halarci ɗaurin auren sun haɗa da Nazifi Zuma, S. Nigger, Kina Gombe, Abdul Zero, Abdul D. One, Sabon Oji, Sadiq Sani Sadiq, Sani Ahmad, Kawu Ɗan Sarki, Ɗan Musa Gombe, Umar Big Show da Mubson Zamani.

Amarya Hauwa’u da ango Ibrahim

Kafin ranar bikin an gudanar da shagulgula kamar haka:

  • Talata, 23 ga Afrilu – Ƙwallon ƙafa a tsakanin ‘yan Kannywood da ‘yan ƙwallon Plateau United.
  • Laraba, 24 ga Afrilu – Ranar Hausawa a tsohon Gidan Zu.
  • Alhamis, 25 ga Afrilu – Yaumul Rasul.
  • Juma’a 26 ga Afrilu – Bikin Ranar Jarumai (Artistes Day) a Plateau Hotel.

Bayan an ɗaura auren, an yi ƙasaitaccen dina da misalin ƙarfe 7:00 na dare a Lamonde Hotel, Jos.

Mata ‘yan fim da su ka halarci bukukuwan da aka yi sun haɗa da Jamila Nagudu, Momee Gombe, Suhailat Ishaq, Asma’u Wakili, Khadija Muhammad, Amina ‘Yar Fillo, Ummulkhairi, Teema Yola, Safiya ‘Yar Ghana, Zainab Sambisa, Safiya Macijiya, Hafsat Bauchi da Asmy Kogin Zuma.

Isma’il Umar, Shamsu Ɗan’iya, Umar Big Show da Abdul D. One a wurin dina.

Aminin ango, Tynking Mai Gashi, ya yi wa dukkan waɗanda su ka halarci bikin godiya da ban-gajiya, inda ya ce, “Amincin Allah ya tabbata ga duk al’ummar Manzon Allah (s.a.w).

“Da farko ina miƙa saƙon gaisuwa ga duk jama’ar da su ka samu damar zuwa taron bikin abokin mu Yamu Baba. Mu na godiya matuƙa kuma mu na wa kowa fatan alkhairi a cikin rayuwar sa.

Sani Ahmad, Asmi Wakili da Teema Yola su na cashewa a wurin dina

“Sannan kuma mu na yi wa kowa fatan komawa gida cikin ƙoshin lafiya da kwanciyar hankali kamar yadda kowa ya zo cikin ƙoshin lafiya da farin ciki.

“Tabbas godiya ita ce kawai abin da za mu iya saka wa masoyan mu da kuma iyayen mu da su ka ba da gudunmawa wajen ba mu tarbiyya da duk wata dama domin inganta rayuwar mu da kuma tabbatar da farin ciki a rayuwar mu.

Ango da amarya a wurin dina

“Kuma don girman Allah idan akwai wanda aka yi wa ba daidai ba ko kuma ya ji kamar an yi masa rashin adalci, mu na masu ba wa kowa haƙuri kuma mu na masu neman afuwa da yafiyar kowa da kowa. Allah ya sa mu dace duniya da lahira baki ɗaya, amin.”

Abdul D. One na waƙe ango da amarya

Loading

Tags: dinaɗaurin aureKannywoodYamu Baba
Previous Post

Shekaru goma bayan sace ‘yan matan Chibok: Nijeriya ba za ta ƙara biyan kuɗin fansa ba

Next Post

Rarara ya ja hankalin mawaƙa da su kama wata sana’ar bayan waƙa

Related Posts

Furodusa a Kannywood, Shu’aibu Yawale ya aurar da ‘ya’ya biyu
Ranar Murna

Furodusa a Kannywood, Shu’aibu Yawale ya aurar da ‘ya’ya biyu

July 18, 2025
Furodusa a Kannywood, Rabi’u Koli da A’isha sun zama ɗaya
Ranar Murna

Furodusa a Kannywood, Rabi’u Koli da A’isha sun zama ɗaya

July 16, 2025
Ranar Murna

Furodusa a Kannywood, Rabi’u Koli zai yi aure ranar Asabar

July 10, 2025
Al-Ameen, Haidar na shirin Daɗin Kowa, ya zama angon Walida
Ranar Murna

Al-Ameen, Haidar na shirin Daɗin Kowa, ya zama angon Walida

June 29, 2025
Haihuwa ta 14: Mawaƙi Abubakar Yarima ya samu Muhammad Sani
Ranar Murna

Haihuwa ta 14: Mawaƙi Abubakar Yarima ya samu Muhammad Sani

June 19, 2025
Jarumin Kannywood, Abdul M. Shareef zai auri jaruma Maryam Malika
Labarai

Jarumin Kannywood, Abdul M. Shareef zai auri jaruma Maryam Malika

June 12, 2025
Next Post
Rarara ya ja hankalin mawaƙa da su kama wata sana’ar bayan waƙa

Rarara ya ja hankalin mawaƙa da su kama wata sana'ar bayan waƙa

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!