JARUMI a Kannywood, Abba El-Mustapha Inuwa, ya bayyana cewa ya kammala karatun sa na digiri na biyu, wato ‘Masters’, a Jami’ar Bayero ta Kano.
A rubutun da ya yi a soshiyal midiya a safiyar wannan rana ta Laraba, ɗan wasan ya yi godiya ga Allah kan wannan matsayi da ya hau, ya ce: “Ina mai farin cikin sanar da masoya na cewa na kammala karatu na na ‘Masters’ kuma tuni na karɓi sakamako na a hannu.”
El-Mustapha ya ce ya samu digirin ne a fannin Tsare-tsaren Cigaban Jama’a da Gudanarwa, wato ‘Public Policy and Administration’.
“Rabbee zidnaa ilman nafee’an. Sai godiya,” inji shi.
Mujallar Fim ta ruwaito cewa a shekarun baya jarumin ya taɓa shiga harkar siyasa har ya tsaya takarar Majalisar Wakilai a Ƙaramar Hukumar Gwale da ke Kano a ƙarƙashin jam’iyyar PDP amma daga baya ya janye.
Daga nan ya ba da sanarwar barin wasu harkoki nasa domin ya koma karatu, inda ya tafi ya samo digirin farko, kuma ya ci gaba zuwa samun nasarar kammala digiri na biyu.
![]()







