INNA lillahi wa inna ilaihir raji’un! Allah ya yi wa fitaccen jarumin Kannywood, Alhaji Mato Yakubu, wanda aka fi sani da Mato Na Mato ko Malam Nata’ala, rasuwa.
Ya rasu a yau Lahadi a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Maiduguri (UNIMAIDTH) sakamakon ciwon daji da ya daɗe yana fama da shi.
Ɗimbin ‘yan fim sun kaɗu da jin labarin wannan babban rashin, kuma sun yi wa marigayin addu’ar samun rahamar Ubangiji.
Alhaji Mato ya yi fice a cikin shiri mai dogon zango na tashar Arewa 24 mai suna ‘Daɗin Kowa’, inda ya samu laƙanin Malam Nata’ala.
Idan kun tuna, a ranar 3 ga Satumba, 2025 mujallar Fim ta bada labarin yadda Ƙungiyar Masu Ƙare Haƙƙin Masu Harkar Fim (AVRS) da kuma Shugaban Jamhuriyar Nijar suka ba Malam Nata’ala tallafin kuɗi a kan rashin lafiyar sa. AVRS ta ba shi N250,000 ta hannun Makama Sani Mu’azu, wanda tsohon shugaban MOPPAN ne, aka kai tallafin a asibitin ga majinyacin a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Maiduguri.
Kamar yadda Sani Mu’azu ya bayyana a Facebook bayan bada tallafin, “Wannan aikin alheri ba shi ne na farko ba, illa shaida ne na yadda hukumar AVRS ke da jajircewa wajen tallafa wa masu fasaha da ke da buƙata.
“Hukumar ta taɓa ba da taimako ga mambobin da suka fuskanci matsalolin lafiya kamar su Mr. Sonny McDon da Ms. Jumoke George a ƙarƙashin jagorancin shugaban hukumar Mahmud Ali-Balogun.
“AVRS ta faɗaɗa tasirin ta na sanya tsarin ta a ko’ina a cikin ƙasar nan ta hanyar kare haƙƙin mallakar fasaha na membobin ta da kuma raba musu ribar hakki kowace shekara, AVRS ta zama ginshiƙi mai muhimmanci a masana’antar fasaha.”
Malam Nata’ala ya yi godiya ga ƙungiyar da su Sani Mu’azu, sannan ya yi kira ga abokan sana’ar sa ‘yan Kannywood da su yi ƙoƙari su yi rajista da AVRS.
Ya kuma jaddada muhimmancin haɗin kai wajen kare ayyukan su na ƙirƙira da kuma tabbatar da tsaron makomar kuɗaɗen su.
Malam Nata’ala ya ce, “Yayin da al’umma masu fasaha ke ci gaba da fuskantar ƙalubalen zamani na dijital, AVRS ta tsaya tamkar fitila, ta na kare haƙƙoƙi da muradun masu fasaha a ko’ina.”
Shi kuma Shugaban mulkin sojin Jamhuriyar Nijar, Janar Abdoulramane Tchiani, ya nuna jinƙan sa ga Natala’ala, inda ya ɗauki nauyin jinyar da yake yi.
Malam Natala’ala ya bayyana cewa shugaban na Nijar ya ɗauki nauyin jinyar a wani bidiyo da aka saki a soshiyal midiya, inda ya tabbatar da cewa shugaban Nijar ɗin ya kira shi ta waya don jin halin da yake ciki.
A cewar sa, Janar Tchiani ya tura masa da tallafin kuɗi don rage masa raɗaɗin rashin lafiyar da ya ke ciki. Sai dai jarumin ya ce ba zai bayyana adadin kuɗin ba a halin yanzu.
Tallafin daga shugaban Nijar ɗin na zuwa ne a daidai lokacin da masana’antar Kannywood take fuskantar ƙalubale, musamman ta fuskar tallafi da jinƙai ga jaruman ta da ke cikin matsaloli na lafiya ko tattalin arziki.
A daidai wancan lokacin, Malam Nata’ala ya sanar da duniya halin da yake ciki na rashin lafiya a soshiyal midiya, inda ya bayyana cewa duk sati uku sai an yi masa allurar N250,000, sakamakon ciwon daji da yake fama da shi.
Don haka ne ya roƙi al’umma da su taimaka masa, sakamakon ƙarfin sa ya ƙare, ya kuma gode wa masu taimakon sa, da kuma neman yafiya ga duk wanda ya yi wa laifi.
Allah ya jiƙan shi, ya sa ya huta, amin.
![]()







