• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Wednesday, May 6, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Kai ma ji kawai ka ke ko ka na fahimta?

by DAGA MUHAMMAD LAWAN RANO
June 18, 2021
in Tsokaci
0
Kai ma ji kawai ka ke ko ka na fahimta?
0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

IDAN har akwai wani babban ƙalubale da zan iya cewa mawaƙan Hausa na fuskanta, ba zai wuce daga masu sauraron su ba. Da yawa mu na ɗauka cewa domin nishaɗi kawai ake waƙa. Ko da yake ba iya mawaƙa ba ne ke fuskantar wannan kalar ƙalubalen ba, hatta marubuta da sauran mutane masu hikima na wannan ƙarni.

Wannan ya sa mu ke zaɓen dumɓaye ko na tumun dare a mafi akasarin lokuta. Ba Alan Waƙa ba ne kawai ke son nusar da masu sauraro haka, hatta shi ma Nura M. Inuwa a sababbin fayafayen da ya saki a 2021 ya kwata makamancin haka, amma shi saɓanin Ala ɗin tuna wa masu sauraro cika alƙawarin da ya ɗauka ya ke.

 Mu ɗauki misalin waƙar ”Yar Amana’ da Nuran ya yi, inda a ƙarshen wani baiti ya ke cewa:

“Nan na ke tsayawa na bar ku sai da safe.”

A tsari, a duk lokacin da mutane biyu za su rabu da cewa sai da safe, to su na kyautata zaton cewa za su kuma haɗuwa. Kwatsam, bayan kamar shekaru uku ko biyu da waƙar sai ga Nura ya dawo da wata sabuwa mai taken ‘Ga Mu Cikin Lokacin Ki’ inda a ƙarshen baitin farko sai ya ke tuna mana wancan baitin bankwana da ya yi wa amarya a waƙar ”Yar Amana’, kafin haka da yake amarya ya ke waƙewa kuma da amaren ne su ka yi waccan sallamar, sai ya ke tuna musu (duk wata amarya) a baitin farko kafin na ƙarshen. Ga abin da ya ce:

“Fari na yo baituka na ki haɗa kaya a kai ki…”

Na tabbata da yawa za su iya tuna waƙar ‘Amarya Ki Haɗa Kaya’. Sai kuma ya ci gaba da cewa:

“Sai ya zamo na yi ruwa tsaki a cikin sha’anin ki,”Har na yi alƙawari na zan dinga baituttukan ki,”Kowa ya tabbata a san da na yo ‘Yar Amana’.”

Idan ma domin nishaɗi ka ke sauraron waƙa, ina ganin zai fi idan ya kasance ka na fahimtar saƙon da ke cikin waƙar. Sannan za ka fi jin gamsuwa ko burgewa.
 Akwai wani ɓoyayyyen al’amari da na gano wanda na san zai ba ka mamaki ainun idan ka farga da shi. Akwai wani daɗaɗɗen saƙon Sani Sabulu da Hamisu Breaker ya isar a wata waƙar sa, ‘Jirgin Masoya’, inda ya ke cewa:

Marigayi Alhaji Sani Sabulu Kanoma

“Wayyo ni rayuwa idan da masoyi ta na yawan daɗi,”Idan an rabo da juna wahala za ta tashi mai faɗi,”A ɗan ba ka tablet a ba ka ruwa amma ba su ma daɗi,”Zancen mazan jiya kan so ni ko na ce da ku taɗi…”

A wata tsohuwar waƙa da Sani Sabulu ya rera za ka fahimta cewa wancan baitin nasa ne Breaker ya aro shi ne ma ya sa domin kare haƙƙin mallaka ya ambace shi da cewa “zancen mazan jiya”.

Ga abin da Sani Sabulu ɗin ya ce shi ma:

“Na gane masoyi daɗin zama garai don haka ba na son mu yi fushi da shi.

“In an rabu sai a kama zazzaɓi a ba da tablet da ‘yan ruwa a sha.

“A yi allura ba ta magani.”

Na tabbatar idan da za a fahimci ire-iren waɗannan saƙonnin na wasu waƙoƙin, to sai ma sun fi burgewa fiye da yadda mutane ke son jin yawan kiɗa a waƙa ba wai saƙon waƙar ba.

Manufar nuni cikin nishaɗi shi ne tura saƙo ta hanyar waƙe wanda a wannan zamani aka mayar da abin kiɗa mai daɗi cikin nishaɗi. Ta haka ne ya sanya yara masu tasowa a wannan ƙarnin ke kallon waƙoƙi a matsayin hanya ɗaya da za ta nishaɗantar da ɗan’adam, ba wai hanyar isar da saƙon da ake son turawa a cikin ta ba.

Su kan su mawaƙan yanzu sun yi abin nan na inda baki ya karkata nan ya fi fitar da yawu, tilas ta sanya wasu juyewa daga abin da aka dasa su a kai domin kauce wa gudun zamani na in ba ni yi ba ni wuri.

* Muhammad Lawan Rano shi ne wakilin mujallar Fim a Kano

Akwai wani ɓoyayyyen al’amari da na gano wanda na san zai ba ka mamaki ainun idan ka farga. Akwai wani daɗaɗɗen saƙon Sani Sabulu da Hamisu Breaker ya isar a wata waƙar sa, ‘Jirgin Masoya’, inda ya ke cewa:

“Wayyo ni rayuwa idan da masoyi ta na yawan daɗi,”Idan an rabo da juna wahala za ta tashi mai faɗi,”A ɗan ba ka tablet a ba ka ruwa amma ba su ma daɗi,”Zancen mazan jiya kan so ni ko na ce da ku taɗi…”

Loading

Tags: Aminu Alan WakaFim MagazineHamisu Breaker DorayiHausa musicKannywoodMujallar FimSani Sabulu Kanoma
Previous Post

Babu finafinan Kannywood sosai a bikin bajen kolin finafinai da za a yi a Kaduna – Mashirya bikin

Next Post

Jam’iyyu 18 ke fafutikar neman kujerar gwamnan Anambra – INEC

Related Posts

Aure Da Saki A Fim: Gangan Ko Gaske?
Tsokaci

Aure Da Saki A Fim: Gangan Ko Gaske?

March 7, 2025
‘Arewa Republic’. Kun gani ba?
Tsokaci

‘Arewa Republic’. Kun gani ba?

February 10, 2025
Rukuni huɗu na masu kallon fim ɗin Hausa
Tsokaci

Rukuni huɗu na masu kallon fim ɗin Hausa

February 7, 2025
Barka Da Zagayowar Ranar Haihuwar Ka Miji Na
Tsokaci

Barka Da Zagayowar Ranar Haihuwar Ka Miji Na

September 1, 2024
Dakta Aliyu U. Tilde
Tsokaci

Arewa: Tsakanin Ilimi Da Sana’a

June 12, 2024
Gwamna Abba Kabir Yusuf
Tsokaci

Shawara ga Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf

June 10, 2024
Next Post
INEC ta sa ranakun zaɓen gwamnonin Ekiti da Osun

Jam'iyyu 18 ke fafutikar neman kujerar gwamnan Anambra – INEC

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!