MASU shirya Bikin Baje Kolin Finafinai na Duniya na Kaduna (Kaduna International Film Festival) sun bayyana cewa ‘yan Kannywood ba su shigar da finafinan su sosai ba a gasar da za a yi a bikin, kuma hakan abin damuwa ne.
Bayanin hakan ya fito ne daga bakin shugaban shirya bikin, Mista Israel Kashim Audu, lokacin da ya ke tattaunawa da mujallar Fim.
Wannan shi ne karo na 4 na bikin, kuma za a rufe karɓar finafinan da za su shiga gasar a ranar Juma’a, 18 ga Yuni, 2021.
A cewar Mista Audu, “Yanzu haka ana cikin karɓar finafinai, amma 18 ga wannan watan za a rufe amsa, daga finafinan Nollywood, Kannywood da sauran ‘woods’ duka za a rufe karɓa.
“Amma magana ta gaskiya, mu na buƙatar ƙarin finafinan Kannywood, domin duk shekara mu na samun ƙarin mutane daga Nollywood, amma in za mu iya samun ƙari daga Kannywood a cikin kwanakin nan don su bada finafinan su zai taimaka.”
Ya ce ƙasashe da dama ne za a su shiga baje kolin.

“A wannan shekarar mun samu finafinai daga Uganda, Italiya, Indiya, Afrika ta Kudu da ma wasu ƙasashen,” inji shi.
Ya ƙara da cewa akwai kuma jami’ai daga gwamnatin Jihar Kaduna da ofishin shugaban Majalisar Wakilai ta Tarayya, kwamishinoni, manyan ‘yan siyasa, malaman addinai, sarakuna, furofesoshi, da matar tsohon Sufeto-Janar na ‘yan sanda da kuma sauran jama’a da za su halarci bikin.
Ya ce, “Don haka mu na neman ƙarin jama’a da su zo su shiga wannan bikin baje koli.”
Ana gudanar da bikin a duk shekara a garin Kaduna.
Shugaban gasar ya ce za a gudanar da bikin na bana ta yanar gizo da kuma zahiri.
A kan batun tsaro, ya ce sun shirya sosai domin akwai ‘yan KASTELEA, NCDC da sauran jami’an tsaro.
Za a yi bikin daga ranar 24 zuwa ranar 28 ga Agusta, 2021.
Audu ya yi kira ga ‘yan Kannywood da babbar murya da su zo su bada gudunmawar su a wannan biki, kada a bar su a baya.
Ya ce, “Mu na godiya ga dukkan waɗanda su ka ba mu gudunmawa. Mu na kuma maraba da kowa da kowa.”
![]()








Slm Sau tari matsalar da aka kasa ganewa game da kannywood shine duk lokacin da aka zo da wani bakon abu komai kyawunsa duk muhimmancinsa idan ba a saka mutanen su ciki ba basu karbar shi sosai