SANANNEN jarumin Kannywood, Alhassan Kwalle, ya bayyana dalilin sa na aikata kwan-gaba-kwan-baya dangane da batun shugabancin Ƙungiyar Jarumai ta Jihar Kano, wanda ya aje sannan kuma yanzu ya dawo.
Idan kun tuna, a kwanan baya mujallar Fim ta kawo labarin yadda shugaban ya bayyana wa duniya cewa shi ya haƙura da shugabancin ƙungiyar tasu.
A cikin tattaunawar da mu ka yi da shi a lokacin, ya yi kukan cewa shugabancin da ya ke yi babu wani abu cikin sa sai rigima da yawan kai ƙararraki.
A cewar sa, a shekarun da ya shafe a kan shugabancin, ‘yan ƙungiyar sun bar shi shi kaɗai ya na ta wahala, kullum ya na Hukumar Hisbah da ofishin ‘yan sanda wajen raba rigingimun ‘yan fim.
Sai dai bayan cin zaɓen gwamna da kafa sabuwar gwamnatin Abba Kabir Yusuf da aka yi a Kano, an ji Alhassan Kwalle ya na cewa har yanzu shi ne shugaban ƙungiyar ta jarumai.
Ganin haka sai mujallar Fim ta nemi jin ƙarin bayani daga gare shi game da wannan al’amari, shi kuma ya yi bayani kamar haka: “To, abin da ya faru bayan sanar da ajiye muƙamin na na shugabanci, daga baya a sakamakon samun canjin gwamnati da aka yi, abubuwa sun taso na cigaba, kuma sai ya zamo ana buƙatar mu a ciki, wanda da yawa a ɗaiɗaiku da kuma ƙungiyoyin namu da kuma iyayen gidan mu na siyasa su ka ga lallai bai kamata a ce an yi wannan abubuwa ba tare da sa hannun mu a cikin sa ba.
“To wannan dalili ya sa mu ka ga akwai buƙatar lallai mu haɗa kai da sauran ƙungiyoyin mu domin ganin mun taimaki wannan masana’anta tamu wajen daidaita sahun al’amuran don su tafi yadda ake buƙata.
“Wannan dalili shi ne mafi girma a kan abin da ya dawo da ni a kan wannan muƙami nawa.”