• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Monday, June 2, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Kidinafas sun sako mahaifiyar Rarara bayan mako uku da sace ta

by ABBA MUHAMMAD
July 17, 2024
in Labarai
0
Kidinafas sun sako mahaifiyar Rarara bayan mako uku da sace ta

Rarara da mahaifiyar sa bayan ta kuɓuta

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

ƁARAYI masu garkuwa da mutane, wato kidinafas, sun sako Hajiya Halima Adamu, mahaifiyar shahararren mawaƙin siyasa Alhaji Dauda Adamu Abdullahi Kahutu (Rarara), bayan ta shafe tsawon kwana ashirin cur a hannun su.

Da safiyar yau Laraba, Rarara ya wallafa hotuna huɗu da bidiyo a soshiyal midiya inda aka gan shi tare da mahaifiyar tasa suna zaune a kan gado, ya rungume ta kamar ya na rarrashin ta, ita kuma da alama ta jigata, har gyangyaɗi ya na neman kwashe ta.

A ƙasan hotunan, Rarara ya rubuta: “Alhamdu lillah! Alhamdu lillah!! Alhamdu lillah!!! Cikin yarda da amincin Ubangiji mun samu dawowar Mama cikin aminci.

“Ina matuƙar godiya ga Ubangiji na, ina godiya ga ‘yan’uwa da abokan sana’a ta, ina godiya ga masoya na na duniya baki ɗaya.

“Haƙiƙa ba ni da bakin godiya a gare ku. Allah ya saka da alkhairi, ya bar zumunci.

“Allah ya ba da lada, na gode, na gode, na gode da kulawa.”

Ɗimbin mutane sun taya shi murnar dawowar Hajiya gida, tare da yi mata fatan alheri.

Rarara da mahaifiyar sa, Hajiya Halima Adamu

Idan ba ku manta ba, mujallar Fim ta ba da labarin yadda ɓarayi masu garkuwa da mutane su ka kutsa kai da misalin ƙarfe 1 na daren Alhamis , 27 ga Yuni, 2024, cikin gidan su Rarara da ke garin Kahutu a Ƙaramar Hukumar Ɗanja cikin Jihar Katsina, su ka yi awon gaba da dattijuwar mai shekara 75.

Wata majiya ta faɗa mana cewa: “Ɓarayin sun zo ne a ƙafa ba tare da wata hayaniya ba, domin kuwa ba su yi harbi ko ɗaya ba, kuma su ka gama komai cikin mintina ƙalilan. Tsohuwar ba ta yi wata gardama ba lokacin da su ka ce mata ta tashi su tafi.

“Duk da yake ɓarayin sun samu wasu mutanen a gidan, sai su ka ɗauki mahaifiyar Rarara ita kaɗai.

“Ba a yi ƙoƙarin tare su a gidan ba saboda su na ɗauke da bindigogi.

“Watakila sun ɓoye baburan su a nesa sannan su ka taka da ƙafa zuwa cikin gari.

“Mu na addu’ar za a dawo mana da ita lafiya ƙalau domin ta na taimakon mu sosai a garin nan.”

Washegari, rundunar ‘yan sandan Jihar Katsina ta ce ta kama mutum biyu da ake zargin su na da hannu wajen sace tsohuwar.

A cikin wata sanarwa da kakakin rundunar, ASP Abubakar Sadiq Aliyu, ya fitar a Katsina, rundunar ta ce mutane biyun da aka kama bisa zargin saka hannu wajen sace mahaifiyar mawaƙin su na amsa tambayoyi a rundunar, ya ce daga baya za a ba da sanarwa kan cigaban da aka samu a kan lamarin.

Tun da farko sai da ASP Abubakar Sadiq Aliyu ya ce difi’o na Ƙaramar Hukumar Ɗanja ne ya jagoranci jami’an tsaro zuwa wajen da lamarin ya faru domin kama waɗanda ake zargi da aikata laifin.

Daga nan ‘yan sandan ba su ƙara cewa uffan ba.

Mujallar Fim ta samu labarin cewa mutane biyun da aka kama ‘yan cikin garin Kahutu ne masu ba ɓarayi labarin sirri kan jama’a, kuma da aka kama su sun amsa laifin su, sai dai sun ce wai ba su san inda ɓarayin su ka tafi da Hajiyar ba.

‘Yan ta’addar sun nemi a biya naira miliyan ɗari tara (N900,000,000) kuɗin fansar tsohuwar.

A makon jiya har ji-ta-ji-ta aka yaɗa cewar mahaifiyar ta Rarara ta rasu a hannun kifinafas ɗin.

Kawo yanzu ba mu samu cikakken bayani kan yadda aka samu nasarar dawowar Hajiya Halima gida ba ko kuma an biya kuɗin fansa ne kafin a sako ta.

Wakilan mun sun yi ƙoƙarin samun mawaƙin ko wani hadimin sa ta waya don samun ƙarin bayani, amma hakan bai yiwu ba saboda rashin samun su a wayar.

Katsina dai ta na ɗaya daga cikin jihohi huɗu da aika-aikar ‘yan bindiga ta fi ta’azzara a arewacin Nijeriya. Sauran su ne Zamfara da Sokoto da Kaduna.

Kwanan nan, a daidai lokacin da ‘yan bindigar ke riƙe da mahaifiyar Rarara, gwamnonin jihohin yankin Arewa-maso-yamma su ka yi babban taro a Katsina inda aka tattauna kan ta’addancin da ke wanzuwa a yankin, da nufin fitar da jaki daga duma.

Loading

Tags: ɓarayiDauda Abdullahi Kahutu RararaJihar Katsinakidinafasrashin tsarota'addanci
Previous Post

Abin da ya sa na koma yin waƙa da kayan kiɗan gargajiya – Aminu Ala

Next Post

Zargin zamba: Furodusa Adamu Ability ya maka jaruma A’ishatu Mahuta a kotu

Related Posts

Ƙungiya ta ja kunnen gwamnatin Kano kan dakatar da finafinan Kannywood 22
Labarai

Ƙungiya ta ja kunnen gwamnatin Kano kan dakatar da finafinan Kannywood 22

May 20, 2025
Hukuma ta rufe gidajen gala a Kano har sai bayan Ramadan
Labarai

Gwamnatin Kano ta dakatar da haska finafinan Kannywood 22 a intanet da talbijin 

May 19, 2025
Sabuwa, matar Ɗanmaraya Jos, ta rasu
Labarai

Sabuwa, matar Ɗanmaraya Jos, ta rasu

March 28, 2025
Tsohon jarumin barkwanci, Ƙarƙuzu, ya kwanta dama
Labarai

Tsohon jarumin barkwanci, Ƙarƙuzu, ya kwanta dama

March 25, 2025
Kannywood ba ta taɓa ƙyama ta saboda addini na ko ƙabila ta ba — Prince Daniel
Labarai

Kalli inda Prince Daniel ya ce an ƙi shi a Kannywood saboda addini (bidiyo)

March 25, 2025
Kannywood ba ta taɓa ƙyama ta saboda addini na ko ƙabila ta ba — Prince Daniel
Labarai

Kannywood ba ta taɓa ƙyama ta saboda addini na ko ƙabila ta ba — Prince Daniel

March 25, 2025
Next Post
Zargin zamba: Furodusa Adamu Ability ya maka jaruma A’ishatu Mahuta a kotu

Zargin zamba: Furodusa Adamu Ability ya maka jaruma A'ishatu Mahuta a kotu

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!