FITACCEN furodusa a Kannywood, Alhaji Adamu Muhammad Bello, wanda aka fi sani da Ability, ya maka shahararriyar jarumar Kannywood mai fitowa a matsayin uwa, Hajiya A’ishatu Umar Mahuta, a kotu kan zargin zamba cikin aminci.
Ability ya shigar da ƙarar ne a madadin sa da wasu mutum uku a Kotun Majistare da ke unguwar Barnawa, Kaduna, a shekaranjiya Litinin, 15 ga Yuli, 2024.
Sammacin ƙarar tare da warantin kama mai laifi, wanda mujallar Fim ta samu kwafen sa, ya nuna cewa Ability ya yi ƙarar Mahuta ne a kan laifin zamba da karɓar kuɗi.
An nuna cewa neman sammaci da warantin ya yi daidai da sashe na 55, 95, 102 da 103 ACJL 2017 na dokokin Jihar Kaduna (application for criminal summon and warrant of arrest pursuant to sections 55, 97, 102 and 103 of the ACJL 2017 Kaduna State).
A sammacin, furodusan ya faɗa wa kotun cewa shi ya na zaune ne gida mai lamba 20, Lere Street, Unguwar Dosa, Kaduna, don haka kotun ta na da hurumin sauraren ƙarar.
Ya ƙara da cewa su ma masu ƙara na biyu, na uku da na huɗu su na cikin hurumin wannan kotu.
Ya ce ita ma Mahuta ta na zaune ne a Malali, Kaduna, don haka ita ma ta na cikin hurumin kotun.
Ya ce an san Mahuta a matsayin jarumar fim, “kuma mun sa juna.”
Ya ci gaba da ba kotu labarin abin da ya faru kamar haka: “A wani lokaci a cikin Fabrairu, 2024 wadda ake tuhumar, da niyyar zamba da cin amanar masu ƙorafin da nufin samun damar aiki ga masu shigar da ƙara na biyu, na uku da na huɗu, ta hanyar mai shigar da ƙara na ɗaya, a ƙasar Saudi Arebiya, kuma cikin yaudara ta sa masu ƙorafin su yarda da ita.”
Ya ce Mahuta ta karɓi kuɗi daga hannun sa har naira miliyan huɗu da dubu ɗari uku (4,300,000) ta hanyar amfani da asusun ta na Bankin Access.
Ya ce haka Mahuta ta jawo masu wahala da ba za su iya jurewa ba.
Ya ce sun yi ƙoƙarin bin duk wata hanya da za su iya tunkarar Mahuta, amma a cikin yaudara sai ta kauce wa hakan.
Ya ce Mahuta ta na guje masa kan laifi, don haka wannan ya hau kan rantsuwa daidai da sashe na 55 na dokar ACJL, 2017.
Ya ce abin da Mahuta ta aikata ya zama laifin zamba wanda ya saɓa wa sashe na 306 da 273 na kundin dokokin Jihar Kaduna na shekarar 2017.
Ability ya ce su na so kotu da ta bayar da sammacin kama Mahuta saboda idan ta samu sammacin kotun, to za ta iya guduwa zuwa inda ba za a iya ganin ta ba, wanda zai iya haifar da jinkiri ga lamarin.
Daga ƙarshe kuma ya buƙaci kotu da ta binciki lamarin tare da hukunta Mahuta idan aka same ta da laifi tare da bayar da umarnin a biya shi diyya a ƙarƙashin sashe na 39 na dokar finalkod ta Jihar Kaduna ta 2017.

A wata hira da ya yi da wakilin mu, Ability ya labarta wa mujallar Fim dalla-dalla yadda lamarin ya faru. Ya ce, “Hajiya A’isha Mahuta ta kira ni ta ce min sun samu dama ƙasar Saudiyya na neman yara waɗanda za su ɗauka aiki don taimakon alhazai, saboda haka ko ina da sha’awa?
“Na ce ina da sha’awa mana, ni da ke da yara. Sai ta ce shi kenan za ta yi min hanya.
“Ta ce yara nawa na ke da su? Na ce mata ina da yara huɗu, daga baya na ce mata yaran nan sun kai biyar. A cikin su akwai yaran shago na, ‘ya’ya na na ciki na guda biyu ne na ba ta, ɗaya kuma mai kula min da gona ne.
“Matar nan ta ce kowane mutum ɗaya zai biya miliyan ɗaya da dubu ɗari biyu da hamsin (1,250,000). Amma in sun tafi Saudiyya za a biya su kuɗaɗe masu yawa, kuma za su samu damar yin aikin hajji. Na ce ba damuwa. Abba, haka na ɗauki kuɗin nan na ba matar nan.
“Ta zo ta ce za a je a yi ‘medical checkup’ a Abuja, mu ka biya dubu ɗari-ɗari kowane yaro. Aka biya dubu talatin kuɗin mota zuwa da dawowa.
“Sai na ce mata, ‘Hajiya, tunda ba yara na ba ne duka, in kun je duk abin da ya shafi yara na, kada ki magana da su, ki kira ni ki magana da ni’. Ta ce min to.
“Bayan sun sauka, ko awa ɗaya ba su yi ba sai ta ce masu kowanen su ta na so ya ba da dubu ɗari da ashirin da biyar (N125,000) cin hanci, in ba haka ba, ba za su samu ba. Sai su ka kira ni su ka ce ga abin da matar nan ta ce.
“Sai na kira ta a waya na ce mata, ‘Hajiya…’ Ta ce, ‘Na’am’. Na ce, ‘Ni da ke mun yi magana duk abin da ya samu yara na, in ki na son wani abu, in dai ba abin da ya shafi aiki ba ne, in dai wani abu ne daban ki kira ni ki faɗa min, ni na san abin da zan yi.’
“Kawai sai ta daka min tsawa: ‘Ni ba za ka hana ni in yi magana da ‘clients’ ɗi na ba, ‘clients’ ɗi na ne, don haka ka bar ni in yi magana da su!’
“Sai na ce, ‘Ni ban hana ki magana da su ba, cewa na yi in ana neman wani abu a wurin su, ni ki min magana’.
“Sai ta ce, ‘Ni dai na faɗa maka, ba zai yiwu in zo da mutane a nuna za a yi min iko da su ba’. Sai ta kashe waya.
“Abba, tun da ta kashe wayar nan, har su ka gama zaman su a Abuja, akan an masu ‘medical’, an yi menene, an yi menene, haka su ka dawo Kaduna, wallahi sai da su ka yi wata uku a gida ba ta neme ni ba, ba ta ce min komai ba, ni ma ban neme ta ba.
“Aka zo aka fara shirye-shiryen tafiya aikin hajji. Daga baya ana sauran sati biyu a fara tashi, sai na ke bincikar me ke faruwa ne?
“Tunda ni na ƙi kiran ta, ni na kai mata aiki, ita ya kamata ta kira ni ta min bayanin an yi kaza, an kaza, wallahi ba ta yi.
“Daga baya da na yi bincike, sai na ji labarin ashe da Saudiyya ta ba da ‘offer’ ɗin, sai su ka canza ‘list’ ɗin yaran gaba ɗaya, sai su ka nemi wasu mutanen da su ka biya miliyan biyar-biyar wanda za su yi aikin hajji.
“Hukumar Alhazai ta ji labari, ta faɗa wa Saudiyya. Aka yi bincike, aka gano kujerun nan an sayar. Shi ya sa aikin hajji da aka yi bana, in dai ka je a matsayin ‘official’ ne, ba ka isa ka saka kayan aikin hajji ba, har ka shiga harami da sauran su ba, kuma wannan dalilin ne.
“Ka ga har aka tafi aikin hajji aka dawo, matar nan ba ta kira ni ba har yau ɗin nan da na ke magana da kai, ta ce min, ‘Yara ba su samu damar tafiya ba, don Allah ka yi haƙuri, kuɗin ka ga yadda za a yi, ga yadda za a yi’.
“Wallahi matar nan ba ta kira ni ta yi magana da ni ba. Sai na yi mata WhatsApp, na ce, ‘Tunda yara na ba su samu damar tafiya aikin nan ba, ina so a dawo min da kuɗi na.’
“Sai ta maido min da cewa kuɗi ba ya na hannun ta ba ne, ya na hannun kamfani ne.
“Sai na ce, ‘Wane kamfani? Ai ni ban san wani kamfani ba, kuma ni ban ba kamfani kuɗi ba, ke ce na ba kuɗi ta “account” ɗin ki. In akwai wani kamfani, wannan damuwar ki ce, ni ba damuwa ta ba ce.’
“Na ce, ‘Na ba ki sati biyu, ina buƙatar kuɗi na.’ Matar nan ba ta yi ‘replying’ ɗi na ba.
“Na sako Hajiya Lamaj a ciki. Lamaj ta yi magana da Hajiya A’isha ya fi sau goma a kai na. Maganar ƙarshe sai ta ce, ‘Ya ce sati biyu ko? In-sha Allahu kuɗin ba za su kai sati biyu ba zan biya shi kuɗin shi’.
“Lamaj ta kira ni ta ce, ”Ta ce sati biyun da ka ba ta ba zai kai ba za ta biya ka kuɗin ka’. Abba, har yanzu ba maganar kuɗin nan!
“Na zo na sa lauya ya rubuta mata ‘demand notice’. Na ba yara na ce su kai mata. Ka san da ta karɓa ta sa hannu, sai ta ce, ‘Yaushe ne shiga kotun?’
“Sai yara su ka zo su ka ce min, ‘Mun ba ta takarda ta sa hannu, sai ta ce mana yaushe ne shiga kotun?’
“Sai na ce, ‘Ku kuma me ku ka ce mata?’ Sai su ka ce, ‘Mun ce ta duba bayanan da ke cikin takardar za ta gani.’
“Bayan awa ɗaya da ba ta wannan takardar, sai lauyan ta ya kira lauya na, ya na cewa sun ga wasiƙa, amma ya na so lauya da lauya su yi magana a kan lamarin. Sai lauya na ya kira ni, na ce, ‘Ba matsala, ku zauna mana.’
“Lauya na ya tambaye shi yaushe za su zauna? Ya ce masa gobe. Yau dai sati biyu kenan lauyan ta ya ƙi yarda su zauna. Wannan shi ne abin da ya faru.”
Wakilin mujallar Fim ya kira Hajiya A’ishatu Mahuta don jin nata ɓangaren. Amma sai ta ce, “Ai ni ba wani abu tsakani na da shi, ba da ni ya ke ba, da kamfani ne.”
Daga nan ba ta ƙara cewa komai ba, sai ta kashe wayar ta.