ALLAH ya yi wa mahaifin matashiyar jarumar Kannywood, Maryam Tasi’u, wadda aka fi sani da Habeebty ko Maryam Malumfashi, rasuwa.
Malam Tasi’u Sulaiman ya rasu ne da misalin ƙarfe 8:30 na dare a ranar Laraba a Babban Asibitin Ƙwandala da ke garin Malumfashi a Jihar Katsina.
Marigayin, mai kimanin shekara 56 a duniya, ya rasu ne bayan ya yi fama da gyambon ciki (ulcer).
Dattijon ya rasu ya bar matan aure biyu da kuma ‘ya’ya 17, maza 10, mata 7.
Maryam Habeebty tana ɗaya daga cikin sababbin jaruman da tauraron su ke haskawa a wannan zamanin.
Ta na cikin jaruman da ke jan fim ɗin ‘A Cikin Biyu’, shiri mai dogon zango na jaruma A’isha Ahmad Idris (A’ishatul Humaira) da ake nunawa a tashar talabijin ta Arewa 24.
Allah ya jiƙan shi da rahama.