AN shiga kotu tsakanin furodusa Alhaji Adamu Bello (Ability) da jarumar Kannywood Hajiya A’ishatu Umar Mahuta a kan ƙarar nan da ya kai ta ta tuhumar zamba cikin aminci.
An yi zaman ne a yau Alhamis a ofishin alƙalin Kotun Majistare da ke Titin Ɗanwaire, a unguwar Barnawa, Kaduna.
Ba a cikin kotu alƙali ya saurari ƙarar ba, a cikin ofishin sa ne, inda a Ability da Mahuta kowannen su ya shiga tare da lauyan sa.
Kasancewar Mahuta ta ce ta zo da wani abu daga cikin kuɗin da ake zargin ta a kan su, sai alƙali ya umarce su da su tafi ofishin rijistara su yi magana a tsakanin su tare da lauyoyin su.
A ofishin sa, rijistara ya yi shimfiɗa kan maganar da za a yi, inda daga nan sai lauyan Ability ya yi wa Mahuta tambaya da cewa, “Hajiya, yaya ki ke so a yi? Su kuma sai su saurara, sai a kawo shawara.”
Sai ta ce, “In Allah yarda ma, next month by this time, gaba ɗaya ma za mu biya.”
Nan take ta kawo naira miliyan ɗaya ta bayar, sannan ta yi alƙawarin za ta ciko sauran kuɗin a ranar 19 ga Agusta ko ma kafin ranar.
Da aka ba Ability dama ya yi magana a kan abin da Mahuta ta ce, sai ya ce, “Abin da na ke gani, tunda ta yi ‘offering’ cewa by next month za ta biya balance ɗin, na yarda. Sai a rubuta.”
Dukkan ɓangarorin suka amince da hakan.
Sai kuma aka koma wurin alƙali aka sanar da shi halin da ake ciki, sannan aka sake komawa ofishin rijistara inda aka yi yarjejeniya a rubuce.
Daga nan kowa ya kama gaban sa.
A yau da safe dai mujallar Fim ta ba ku labarin cewa Ability ya kai Mahuta ƙara ne a ranar Litinin da ta gabata a kan wasu kuɗi naira miliyan huɗu da dubu ɗari uku (N4,300,000).
A ƙarar, ya bayyana cewa ya ba ta kuɗin ne bisa alƙawarin za ta sama wa ‘ya’yan sa gurbin zuwa Saudi Arebiya domin su yi aikin agajin alhazai a lokacin aikin hajjin bana, amma ta gaza yin hakan.
Ya ce da ya buƙace ta da ta dawo masa da kuɗin sa, sai ta fara yi masa ƙumbiya-ƙumbiya, ta na faɗin ai “kamfani” yake bi, ba ita ba, bayan kuma a asusun ta na banki ya saka kuɗin, kuma bai san da wani batun kamfani ba a lamarin.
Ability ya ce ya yi ƙarar ta ne bayan da hanyoyin sulhu da ya bi duk sun toshe, ciki har da saka furodusa Hajiya Fatima Lamaj don ta sa baki, da kuma takardar buƙatar biyan kuɗin da lauyan sa ya aika mata.
Ability ya ce abin da Mahuta ta aikata ya zama laifin zamba cikin aminci wanda ya saɓa wa sashe na 306 da na 273 na kundin dokokin Jihar Kaduna na shekarar 2017.
A yanzu dai da alamar an hau hanyar warware matsalar a tsakanin dattawan biyu na Kannywood mazauna Kaduna.
![]()







