1. Duniyar duka ta yi yo haske,
Ɗan’uwa na kar ko ka waske,
Yau ta ke ranar bikin meti.
2. Sa gilashi daina yin wargi,
Kau da kai ko sun yi yo zagi,
Mu yi murna har mu yo fati.
3. Kirsimeti biki ne na sallah,
Sanadin saukar shi ne Isah,
Wanda zai dawo ko ba latti.
4. Almasihu Manzo ne na Allah,
Kuma bawa ne wurin Jallah,
Da ya zo don tsarkake zati.
5. Tsarkakakke ne shi kun gane,
Babu aibi shi na daban ne,
Rabbi shi ya nufar da yin saiti.
6. Ɗa ga ‘yar Imrana ne haƙƙa,
Ba uba a gare shi la shakka,
Mai wasici da kauda yin datti.
7. Ya yi magana tun ya na jego,
Ya faɗa masu ban da yin ƙago,
Sharruka ko yarfe har fenti.
8. Yau ta ke ranar zuwan nashi,
Zan yi waƙa sai ku min amshi,
Ta zuwan murnar Kirismeti.
9. Ko’ina ka bi za ka ɗan gane,
Wagga rana ai ta daban ne,
Don zuwan Isah mu yo fati.
10. Me ya sa ne zan ƙi yin murna,
Da zuwan babban da na auna,
Ba kama tasa wanga ƙarnati.
11. Kirsimeti bikin gaba ɗai ne,
Don ko Isah shi na kowa ne,
Ba shi zargin wanda ke fati.
12. Me ya sa ma zai yi yo zagi?
Babu kyau a yawaita yin zargi,
Gun Kirista har Musulmati.
13. Kai Musulmai mu tashi du’a’i,
Har Kirista mu kau da bala’i,
Don Arewa ta zamma kan saiti.
14. Kau da gaba har da ƙin juna,
Duk mu bauta wa Rabbi Sarki na,
Ban da haushi ko ko yin ƙwarti.
15. Yadda Jallah ya ƙagi imani,
Kuma Shi ne ya ƙagi shaiɗani,
Zai hisabi a kan dukan baiti.
16. Ban da zalunci ga junan mu,
Ku Kirista har Musulman mu,
Mu riƙe junan mu kan saiti.
17. Zan tsaya haka don ina hanya,
Na sani wasu za su tambaya,
Yaya sunan wanda ke baiti?
18. Ɗan Musumai ne ku ɗan gane,
Da ya san daraja ta addine,
Ba shi zagin karuwan titi.
19. Ɗan Bala jika wurin Garba,
Ni ne Ahmadu ɗa ga ‘yar Baba,
Can a Maiduguri na ke baiti.
*Muhammad Bala Garba
25 ga Disamba, 2021