WASU ‘yan jarida sun koka kan yadda su ka yi tunanin an ci zarfin ɗan jarida a cikin fim mai dogon zango mai suna ‘Labari Na’.
A cikin kashi na 11 a zango na uku an nuna ɗan jarida na neman ba’asi a wajen fitaccen mawaƙi Naziru M. Ahmad (Sarkin Waƙa) dangane da rayuwar Sumayya (Nafisa Abdullahi) wanda ya jaddada ita ya kamata a tuntuɓa kasancewar rayuwar ce. A yayin da ɗan jarida ya dage wajen bibiyar labari sai Naziru ya nemi a ba wa ɗan jaridar kuɗin mota don ya yi na mota, alamun ba zai iya samun amsar tambayar da ya ke nema daga gare shi ba.
Masu da’awar an wulaƙanta ɗan jarida a wannan shirin sun yi ta kiran lambar daraktan fim ɗin, Malam Aminu Saira, don jin ta bakin sa.
Marubucin wannan shiri, Nasir Gwangwazo, tsohon ɗan jarida ne da ya ɗauki tsawon shekaru ya na aikin jarida a babbar jaridar ‘Leadership A Yau’, wanda har matsayin babban edita ya riƙe, kuma yanzu haka ma shi ne editan jaridar ‘Manhaja’ da kamfanin Blueprint ke wallafawa. Shin zai yi wani abu ne don muzanta aikin sa da ya ke cin abinci da shi? Ba mamaki ya san akwai ‘yan jarida da su ke zubar da mutuncin aikin su wajen yawon maula da roƙo, shi ne ya rubuta hakan don jan hankalin su a kan riƙe mutuncin kan su.
Ko a kwanakin baya an samu taƙaddama tsakanin ‘yan jarida a Kano inda wani babba daga cikin su ya soki masu irin wannan hali na yi wa ‘yan siyasa maula da tumasanci. Kuma kamar yadda a kowane sashi na rayuwa a kan iya samun nagari da na ƙwarai, su ma ‘yan jarida ba mala’iku ba ne da za a ce babu nagari da na banza a cikin su.
Kamfanin Saira Movies ne ya shirya fim ɗin ‘Malika’ a shekarun baya da har gobe babu wani fim a masana’antar Kannywood da ya fito da ƙima da darajar aikin jarida sama da shi. An nuna babban jarumi da ake yi wa laƙabi da Sarkin Kannywood a matsayin ɗan jarida mai tsattsauran ra’ayi a kan kiyaye dokokin aikin jarida. Fim ɗin, marubuci kuma ɗan jarida Maje El-Hajeej Hotoro ya rubuta shi, kuma shi ma Maje babban ɗan jarida ne, wanda ya ke da gogewa a kan aikin jarida. Shin ko sauran ‘yan jarida sun yi masa rubutun yabo a kan wannan gagarumin aiki?
‘Malika’ ya yi tashe da shaharar da ya kamata ‘yan jarida su yi kishin aikin su wajen yaɗa shi ko yin rubutun yabo ga kamfanin a matsayin ƙarfafa gwiwa, amma babu wata rubutacciyar shaidar yin hakan, sai yanzu su ka ga an yi musu ba daidai ba. Shin me ‘yan jarida su ke so? Ba a ba wa wasu ‘yan jarida na goro ne ko kuwa su ba sa ganin aikin alheri ne sai an taɓa su?
* Abdussalam Barista Hotoro ya rubuto ne daga Kano
Copyright © Fim Magazine. All rights reserved.
www.fimmagazine.com
![]()







