LIKKAFAR Rahama Sadau ta yi gaba yayin da fitacciyar jarumar ta Kannywood da Nollywood ta samu shiga cikin wani fim ɗin Indiya mai suna ‘Khuda Haafiz’ kashi na 2.
Samuwar hakan wani cikar muradi ne ga Rahama, wadda ta fara harkar nishaɗantarwa ne da rawar Indiya a bukukuwa a Kaduna tun kafin ta shiga fim.
A yau ɗin nan jarumar ta wallafa wasu hotuna tare da wani fitaccen ɗan wasan Indiya mai suna Vidyut Jammwal, wanda shi ne jarumin fim ɗin na ‘Khuda Haafiz’.
Akwai alamun cewa a wajen ɗaukar fim ne aka ɗauki hotunan.
Da ma tun a jiya Rahama ta wallafa hotuna biyu a Instagram inda aka gan ta rungume da wata kyanwa, kuma ta rubuta cewa a lokeshin ɗin shirya fim ɗin ne.
A ƙasan hotunan, ta rubuta, “Hello Bollywood . . .” tare da saka alamonin fuska da ke bayyana farin cikin ta da wannan matsayi da ta hau.

Ta ƙara da cewa, “Ga mu nan tare da Vidyut Jammwal” a wajen ɗaukar shirin ‘Khuda Hafeez Chapter 2’, a rana ta 31.
Binciken da mujallar Fim ta yi ya gano cewa ‘Khuda Haafiz’ fim ne na gumurzu wanda ya fara fitowa a ranar 14 ga Agusta, 2020.
Ya na bada labarin wani matashi ne mai suna Sameer wanda su ke zaune cikin jin daɗi da matar sa Nargis. Kwatsam, rannan sai ɓarayi masu safarar mutane su ka sace ta, don haka aiki ya samu Sameer don ya ceto ta daga hannun su kafin ta salwanta baki ɗaya.
Daraktan fim ɗin shi ne Faruk Kabir kuma jaruman shirin sun haɗa da Vidyut Jammwal, Shivaleeka Oberoi, Annu Kapoor, Shiv Panditt, da Aahana Kumra.
Furodusoshin shirin su ne Kumar Mangat Pathak da Abhishek Pathak, sannan kamfanin Panorama Studios ne ya ɗauki nauyin shirya shi.
A yanzu kashi na biyu na fim ɗin ne aka saka Rahama Sadau a ciki.
Ana ɗaukar fim ɗin a garin Lucknow da ke jihar Utter Pradesh ta ƙasar Indiya.
Sai dai Rahama ba ta bayyana yadda aka yi ta shiga aikin wannan fim ba ko rol ɗin da aka ba ta ko kuma ma ranar da ta tafi Indiya; kawai dai an gan ta a lokeshin.
Mujallar Fim ta ruwaito cewa Rahama Sadau ta na daga cikin jaruman Kannywood ƙalilan da su ke jin yaren Indiya raɗau, wato irin su Ali Nuhu da Baballe Hayatu.

Ɗaruruwan mutane, musamman ‘yan fim na Kannywood da na Kudu, sun taya Rahama murnar samun shiga wannan fim, wanda ake gani a matsayin babban cigaba ba a gare ta kaɗai ba har ma ga ‘yan wasan Nijeriya gaba ɗaya.