KHADIJA Abdullahi Shehu Bichi, wadda aka fi sani da sunan Hajja Ce, marubuciya ce wadda a yanzu ta ke sahun gaba na marubutan onlayin. Ta kasance mai tsara labari wanda cikin lokaci ƙanƙane zai ɗauki hankalin mai karatu.
Shin wacece Khadija? Me ya sa ake ce mata Hajja Ce? Menene tunanin ta game da harkar rubutu da marubuta? Wace shawara za ta ba marubuta ‘yan’uwan ta, musamman ma ‘yan onlayin? Domin jin ko amsoshin waɗannan tambayoyin, mujallar Fim ta tattauna da Khadija, inda wa warware mana zare da abawa, kamar haka:
FIM: Da farko za mu so ki faɗa mana tarihin rayuwar ki.
HAJJA CE: To, da farko dai suna na Khadija Abdullahi Shehu Bichi. Ni ‘yar Nijeriya ce, ‘yar asalin Jihar Kano ce ni, haifaffiyar garin Bichi. Ina da aure da yara uku. Kuma ni Bahaushiya ce gaba da baya.
Na yi ‘primary school’ a garin Bichi. Na tafi GGSS Kwa na yi ‘Secondary School’ ɗi na tun daga JS har zuwa SS. Bayan na kammala na tafi na yi karatu na na NCE a FCE (T) Bichi inda na karanci ‘Home Economics’. Bayan nan na yi ‘Computer’ a Bichi ‘Computer Center and Information Technology’.
FIM: Ya aka yi ki ka samu sunan Hajja Ce?
HAJJA CE: Kamar yadda na ce maka, suna na Khadija, amma a ana kira na da Hajja kasancewar sunan kaka ta ne na ci.
A duniyar onlayin kuma aka fi sani na da Hajja Ce. “Hajja” da ma shi ne laƙani na, “Ce” ɗin kuma ya samo asali ne a wajen ‘course mate’ ɗi na. Idan na kira su a waya kafin su ce wacce zan ce “Hajja ce”, duk lokacin da zan yi waya kafin ka tambayi wacce zan ce “Hajja ce”, shi ne ina zuwa za ka ji su na “Hajja ce, Hajja ce! Ke dai kin huta, ba kya bai wa mutum wahalar sanin ko wacece.”
Bilkisu Abdullahi Shitu da Jamila Sabitu sai Hassana Muhammad Baba, su ne silar saka mini wannan suna. Ni kuma sai na yi amfani da shi a matsayin suna na da za a fi ganewa a jikin duk wani rubutu da zan yi.

FIM: A wacce shekarar ki ka shiga harkar rubutu?
HAJJA CE: Na fara rubutu 2016. Na fara rubutun kuma ta silar ƙanwa ta Sadiya Abdullahi Shehu Bichi (Stylish bch).
Ina karatu amma na bugaggun takarda, don har na haifi yarinya ta ta farko ba na harkar soshiyal midiya kowace iri. Hasali ina ganin ‘yan’uwa na da abokan arziki su na harkar, amma dai ni ba ta dame ni ba, sai daga baya ita ƙanwa ta ta ke cewa akwai littattafan Hausa a onlayin na zo na rinƙa karantawa. Na ce mata a’a ba na son na onlayin. To, daga ƙarshe dai maigida na shi ne ya buɗe mini ‘WhatsApp’ da kan sa, daga nan ƙanwa ta ta fara turo mini littattafan da ta ke rubutawa da kuma wanda su ka yi haɗaka wajen yi. Ina mamakin ya aka yi ta iya? Waye ya koya mata? Na kira ta a waya, ta zo gida na ta na dariya, ta ke cewa ai ni ma zan iya. Na ce, “A’a, wannan harkar ta masu baiwa ce ni kuma na san ba ni da ita sai ta karatun kawai.”
To daga nan dai ba ta bar gida na ba sai da ta gama tabbatar mani da cewa, “Yaya Hajja za ki iya.” Na yi, kuma ta ƙarfafa mani gwiwa cewa na yi daidai duk kuwa da cewar akwai gyara da yawa wanda sai a hankali a hankali sannan ta gama koyar da ni har ya zama cewa zan iya yin labari ni kaɗai ba tare da na gaya mata ba. Lokacin da Maman mu ta ga ana yawan kiran mu a waya a kan labaran mu sai ta ɗan ji tsoro, ta ce ita dai ba ta son abin da zai sa a ce ‘ya’yan ta sun yi abu kaza. Mu kuma, musamman ma ni da abin ya shige ni kai-tsaye, don sai da na zo na fi ƙanwar tawa yin rubutun, mu ka rasa ya za mu kwatanta mata harkar. Sai Allah ya sa aka nuno Fauziyya D. Sulaiman a Arewa 24, mu ka ce mata, “To kin ga irin rubutun da wannan matar ta ke yi shi mu ke yi.” Sai ta kwantar da hankalin ta, ta yi mana fatan alkairi tare da yi mana gargaɗin kare mutuncin mu da kuma mutuncin su a kan abin da za mu rubuta ɗin.
FIM: Kin taɓa buga littafi ne ko sai na onliyin ki ke yi?
HAJJA CE: Na fara rubutu ne a onlayin, ban taɓa bugawa ba, sai dai a kullum maigida na ya na ƙarfafa mani gwiwar cewa na buga ɗin. Kuma in-sha Allahu ina da burin yin hakan da ikon Allah.
FIM: Ko kin samu canjin rayuwa da ki ka shiga harkar rubutu?
HAJJA CE: Gaskiya abubuwa da yawa sun canza lokacin da na fara rubutu. Ta dalilin rubutu na san mutane fiye da tunani na. Sannan na ƙaru da abubuwa fiye da baya kafin na zama marubuciya wanda har yanzu ina kan ganin bambanci sosai da sosai.
FIM: Kenan dai a yanzu kin maida harkar rubutu sana’ar ki?
HAJJA CE: Uhmmm! A da na ɗauki harkar rubutu a matsayin sha’awa. Amma a yanzu ka san komai ikon Allah ne, to a yanzu na ɗauki rubutun da na ke yi a matsayin sana’a sosai ma. Sana’a ba wai wacce zan ce dole sai da ita zan rayu ba, a’a, kawai wata hanya ce da Allah ya ƙara buɗa mani da ban yi zato ko tsammanin zan samu alkairi a cikin ta ba.
FIM: Akwai wasu nasarori da ki ka samu a cikin harkar rubutu?
HAJJA CE: Alhamdu lillah, nasarori mu na kan samu har yanzu tunda ba daina rubutun na yi ba. A harkar rubutun nan na samu nasarori sosai kuma kullum cikin nasara na ke a cikin ta. Alhamdu lillahi.
FIM: Wane burin ki ke da shi a game da rubutu?
HAJJA CE: Ɗan’adam da buri aka san shi, ba ya daina ɗaukar buri har sai ƙasa ta rufe masa idanun sa. Ina da buri wanda da ikon Allah nan gaba kaɗan Allah zai cika mani shi. Alhamdu lillahi, Allah ya cika mani buri na sosai ma a harkar rubutu. Ya cika mani har wanda ma ban yi zato ko tsammanin su ba. Sai kuma na gaba idan mu na da rai da rayuwa in-sha Allah.
FIM: Ta ɓangaren matsaloli fa, ko akwai su?
HAJJA CE: Murubuta su na fuskantar matsaloli da yawa a wannan lokacin, ba na onlayin ɗin ba ba na bugaggun ba. Su na fuskantar rashin mutunci, rashin ganin daraja, rashin ganin ƙima da kuma wulaƙanci a wajen makaranta da kuma marubutan da za ka ajiye alƙalamin rubutun su, ma’ana waɗanda su ka daina yin rubutun a yanzu.
A da, ana ɗaukar marubuci madubi abin dubawa, ana ɗaukar sa mutum mai mutunci da daraja. Amma a yanzu musamman tun lokacin da aka ce an maida wasu labaran na kuɗi, sai ya zama babu abin cin mutunci sama da shi. A yanzu idan ka na rubuta labarin kuɗi ana yi maka kallon matsiyaci wanda sai da kuɗin littafin ya ke samun wasu abubuwan na rayuwa.
Yanzu marubuci ya riga ya sa a ran sa cewa ko da yaushe zai iya hawa onlayin ya ci karo da rubutun da aka ci masa mutuncin da tun da ya zo duniya ba a taɓa yi masa ba. Shi kuma littafin kuɗi kamar mai sayar da leshi ko atamfa ko kayan kicin ne. Ka kasa ka na jiran mai zuwa ya saya. Amma an maida marubuci tamkar wani wanda ba shi da aikin yi. Haƙiƙa marubuta su na fuskantar matsalolin da ban san yadda zan bayyana maka ita ba.
FIM: Menene saƙon ki na ƙarshe?
HAJJA CE: To saƙo na na ƙarshe zuwa ga ‘yan’uwa na marubuta shi ne: mu tsarkake zuciyar mu da alƙalamin mu, mu san abin da mu ke rubutawa mu kuma san inda mu ke yaɗa shi. Mu yi haƙuri domin komai sai an yi haƙuri ake cimma gaci. Mu tuna akwai mutuwa, za mu tafi mu bar wannan abin da mu ke rubutawar a doran ƙasa. Ba mu san dubban mutanen da za su karanta ba. Duniya kullum daɗa taɓarɓarewa ta ke. Alfaharin me za ki yi idan kin bar ɓarna?
Ina roƙan Allah ya daidaita tunanin marubuta, ya ci gaba da kimtsa masu abubuwan alkairi, ya dafa masu, ya kuma yi riƙo da hannuwan mu da zuciyoyin mu.
FIM: Madalla, mun gode.
HAJJA CE: Ni ma na gode.