MARUBUTA littattafan Hausa sun yi kwamba a bikin Anisa Sa’eed, ɗiyar shahararriyar marubuciyar nan Hajiya Halima Abdullahi K/Mashi wanda aka yi jiya a Kano.
Jiya ɗin ita ce rana ta farko ta bikin, wadda aka yi wa laƙabi da Ranar Uwa, wato Mother’s Day.
An yi bikin a ɗakin taro na Mash Event Centre da ke Unguwar Gurungawa da ke Ƙaramar Hukumar Kumbotso a cikin garin Kano, kuma an fara shi ne da misalin karfe 6:30 na yamma.
Farkon buɗe taron dai manyan baƙi marubuta mata su ne su ka fara baje kolin rawar su a matsayin su na ƙawayen uwar amarya. A lokacin kuma ita uwar amarya ta shiga tsakiyar su su na zagaya ta su na yi mata liƙi.
Rawar dai ta manyan mata ce, don haka su ke yin ta cikin ƙasaita irin ta isassun mata.
An dai yi ruwan kuɗi a wajen liƙi tamkar ba ka ce ana cikin matsin tattalin arziki ba.

Bayan sun gama, sai kuma amarya da ango su ka shigo wajen taron inda nan ma amarya da ƙawayen ta su ka cashe a wajen, kafin daga baya aka bar amarya da ango su ka yi tasu rawar ana bin su da liƙi.
Bayan nan an raba abinci ga mahalarta taron inda aka ci abinci na alfarma tare da abin sha.

An dai yi taron bikin an kammala lafiya, kuma za a ci gaba da shagalin bikin har zuwa jibi Lahadi inda a ranar ne za a ɗaura auren Anisa Auwal Abdullahi a masallacin Mu’azu Abubakar da ke Shagari Close, Unguwar Rimi, Kaduna.
An faɗa wa mujallar Fim cewa a Kano ne amaryar za ta tare.
An tashi daga bikin da misalin karfe 9:40 na dare.


Manyan marubuta maza da mata da su ke ciki da wajen Jihar Kano sun halarta, ciki har da Bilkisu Yusuf Ali, Sadiya Garba Yakasai, Zuwaira Dauda Kolo, Amina Hassan Abdussalam, Fauziyya D. Sulaiman, Lubabatu Ya’u Ɓaɓura, Hadiza Nuhu Gudaji, Umma Sulaiman ‘Yan’awaki (Aunty Baby), Fa’iza Muhammad Sajo, Rabi Talle Maifata, Ummi Sani Fanisau, Ibrahim M. Indabawa, Abdullahi Jibril Ɗankano (Larabi), Lawan Muhammad PRP, El-Ameen Daurawa, Zubairu Balannaje, Adamu Yusuf Indabo, da sauran su.






![]()







