A GOBE Lahadi Ƙungiyar Marubuta ta Nijeriya (ANA), reshen Jihar Kano, da Ƙungiyar Gamayyar Marubutan Arewacin Nijeriya, wato ‘Northern Nigerian Writers Summit’ (NNWS), za su yi wani babban taro domin karrama shahararren malamin nan kuma marubuci, Sheikh Dakta Yusuf Ali.
Ustaz Sheikh Yusuf Ali, wanda shi ne Sarkin Malaman Gaya, ya rasu ne a Kano a daren Lahadi, 6 ga Nuwamba, 2023 bayan ya yi fama da rashin lafiya. Shekarun sa 73 a duniya.
A wannan taron tunawa da malamin da za a yi, za kuma a baje kolin wasu daga cikin fasahar sa a ɓangaren adabi.
Manyan baƙi masu jawabi su ne Farfesa Ibrahim Garba Satatima, Farfesa Bello Sa’id, Malam Ɗanjuma Katsina, Farfesa Aliyah Adamu Ahmad.
Jagoran zaman shi ne Sheikh Ibrahim Khalil.
A saƙon gayyata da ta wallafa a Facebook, babbar ‘yar shehin, Sayyada Bilkisu Yusuf Ali, ta ce: “Ina gayyatar ‘yan’uwa da abokan arziki gurin wannan babban taro da ke nuna ƙauna da karramawa.”
Ta ƙara da cewa, “Hakika wannan karramawa ce mafi girma da na taɓa gani a duniyar rubutu! Madalla, Allah ya fi mu yabawa!”
Katin gayyatar da kungiyoyin su ka buga ya nuna cewa za a fara taron da ƙarfe 10 na safe a Laburaren Murtala Muhammed da ke Kano.
A lokacin da Sheikh Yusuf Ali ya rasu, mujallar Fim ta ba ku labarin cewa Ƙungiyar Gamayyar Marubutan Arewacin Nijeriya ta nuna alhini tare da jimami kan rashin da aka yi.

A sanarwar da babban sakataren ƙungiyar, Malam Khalid Imam, ya bayar a ranar 12 ga Nuwamba, 2023, ƙungiyar ta ce, “Malam Yusuf Ali ya bayar da gudunmawa matuƙa wajen ilimintarwa da faɗakar da al’umma, musamman ta shirye-shiryen sa a kafofin yaɗa labarai na ciki da wajen ƙasar nan.
“Shahararren shirin sa na fatawa mai taken ‘Ilimi Kogi’ ya cancanci a ambace shi.
“Malamin, wanda marubuci ne musamman na waƙoƙin Hausa kuma makaranci ne na duk littattafan adabi da sauran ilimai, ya cancanci dukkan marubuta da masu zumunci da adabi su yi alhinin rashin sa.”
![]()







