MAWAƘIN Kannywood, Abdullahi Abubakar, wanda aka fi sani da Auta Waziri, zai yi bankwana da kwanan sitidiyo.
Za a ɗaura auren Auta Waziri da abar ƙaunar sa Halima Mustapha (Marmah), ranar Juma’a, 6 ga Disamba, 2024 da misalin ƙarfe 1:00 na rana a masallacin Juma’a na SMC, Unguwar Dosa, Kaduna.
Za a gudanar da ƙasaitaccen walima a ɗakin taro na Umaru Musa ‘Yar’adua da ke dandalin Murtala Square, Kaduna.
Allah ya kaimu da rai da lafiya, ya kuma bada ikon zuwa.