• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Sunday, April 5, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Miji na ɗan Aljanna ne – furodusa a Kannywood, Fatima Lamaj

by DAGA ABBA MUHAMMAD
November 21, 2023
in Labarai
0
Hajiya Fatima Lamaj (a tsakiya) yayin da su jarumin Kannywood Abubakar Hunter ke addu'a

Hajiya Fatima Lamaj (a tsakiya) yayin da su jarumin Kannywood Abubakar Hunter ke addu'a

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

* Ya riƙe zumunci da ‘yan’uwa, ya riƙe marayu, da inji yayar shi

TSOHUWAR Shugabar Haɗaɗɗiyar Ƙungiyar Masu Shirya Finafinai ta Nijeriya (MOPPAN), reshen Jihar Kaduna, Hajiya Fatima Ibrahim Ahmad (Lamaj), ta ce ta na kyautata tsammanin mijin ta, marigayi Alhaji Ibrahim Sa’idu Gamagira (Maje), ɗan Aljanna ne.

Lamaj ta faɗi haka ne bayan kammala addu’ar uku da aka gudanar na rasuwar mijin ta a yau Talata.

Kamar yadda mujallar Fim ta bada labari, Alhaji Ibrahim, wanda ake yi wa laƙabi da Maje, ya rasu ne a ranar Asabar da ta gabata a asibiti a Abuja inda ya yi jinya.

Bayan an rufe shi a maƙabartar Gudu da ke Abuja, sai iyalin sa da ‘yan’uwan sa su ka dawo gidan sa a Kaduna inda aka ci gaba da zaman makoki.

Dandazon jama’a a wurin addu’ar uku a gidan marigayin

A hirar ta da mujallar Fim kan wannan abin ciki da ya faru, Hajiya Fatima ta ce, “Babu abin da zan ce wa Ubangiji sai dai godiya. Miji na ya cika da imani, kuma mun rabu da shi lafiya cikin farin ciki, mun yafe wa juna, ya neme ni gafara, kuma da ma bai min komai ba.

“Samun miji irin nawa, gaskiya da wuya! Allah ya ba ni miji nagari, kuma Shi ya karɓe shi daga wuri na, to ban isa in ja da ikon Allah ba.

“Abin da na ke masa fata shi ne rahama daga Ubangiji. Kuma a bisa dukkan alamu miji na ɗan Aljanna ne, domin kai ma Abba ka shigo gidan nan ka ga al’ummar da su ka zo zaman ta’aziyyar shi da addu’a. Wannan ba ƙaramin abin farin ciki ba ne.

Hajiya Fatima Ibrahim Lamaj (a dama) tare da Hajiya Uwani Daudu a lokacin addu’ar uku

“Duk da na san ina cikin ƙunci, ina cikin baƙin ciki na rasa miji na, to amma ina yi wa Allah godiya da Allah ya ba shi irin wannan jama’a.

“Kuma maigidan ka, Ibrahim Sheme, ya halarci jana’iza a Abuja. Duk da cewa ‘weekend’ ne – ba mutane a garin – amma alhamdu lillahi an samu fiye da abin da ake nema a ce an raka mamaci.

“Ina mai yi masa fatan rahama. Allah ya jiƙan sa, ya raya abin da ya bari. Allah ya ba mu haƙurin jure rashin nan.

“Har abada ba za mu iya mantawa da Ibrahim ba, domin Ibrahim mutum ne. Mutum ne wanda ya ke riƙe alƙawari, domin ya san muhimmamcin alƙawari, ya san darajar al’umma, kuma ya riƙe jama’a da maƙwabta.

“Ibrahim ba ya nuna bambanci; ba ruwan shi da wannan ɗakin mu ɗaya, wannan ba ɗakin mu ɗaya ba. Wallahi haka miji na ya ke.”

Ana zaman makokin rasuwar Alhaji Ibrahim (Maje)

A nata ɓangaren, yayar mamacin, Hajiya Uwani Daudu, cewa ta yi: “Alhamdu lillahi! Saboda duk abin da ya faru, babu abin da za mu yi sai dai mu gode wa Allah. Abin da za mu ce, rayuwar Ibrahim sai alhamdu lillah.

“Ibrahim mutumin kirki, mutum mai alƙawari, mai son ‘yan’uwan shi, mai riƙe marayu, gidan shi cike ya ke da marayu.

“Don haka babu abin da za mu ce masa sai dai Allah ya saka masa da alkhairi.

“Wahala da ɗawainiyar da ya yi da marayu, ‘yan’uwa, talakawa da maƙwabta, kai hatta wanda bai sani ba Maje ya tsinci yaro saurayi ya na saida rake, ya maida shi makaranta, ya kai shi jami’a, ya yi bautar ƙasa, ya sama masa aiki. To wannan me za ka ce wa mutum? Sai ka ce Allah ya saka masa, Ubangiji ya gafarta masa, ya kuma sa Aljanna ce makomar sa.”

An gudanar da addu’ar sadakar ukun ne da misalin ƙarfe 10:00 na safe a gidan marigayin da ke unguwar Rigachikun a Kaduna.

Jama’a da dama sun halarci addu’ar, kama daga ‘yan’uwa, abokan aiki, ‘ya’ya, jikoki da abokan aikin matar sa a Kannywood irin su Abubakar Hunter, Zaharaddin Mando, Murtala Aniya, Ɗanladiyo Mai Atamfa, Jamilu Ɗan Masu Kuɗi, Khaleed Gamagira, Usman Pepe, Saifu Lamaj, Sani Amalo, Hajiya A’isha ZIAU, da Saratu Iliyasu.

Allah ya jiƙan Alhaji Ibrahim Sa’idu Gamagira (Maje), ya kuma albarkaci dukkan da ya bari, amin.

Ɗimbin masu ta’aziyya a gidan marigayin

Loading

Previous Post

An yi jana’izar daraktan Kannywood Aminu S. Bono a Kano

Next Post

Shari’ar Zamfara: Ko gobe a ja daga, ba mu tsoron yin gaba-da-gaba da zaɓen inkwankilusib – Gwamna

Related Posts

Rasuwar dattijon Kannywood, Nura Shareef, ta girgiza ‘yan fim
Labarai

Rasuwar dattijon Kannywood, Nura Shareef, ta girgiza ‘yan fim

February 22, 2026
Daraktar fim ta ƙi karɓar awad saboda kisan gillar da Isra’ila take yi a Gaza
Labarai

Daraktar fim ta ƙi karɓar awad saboda kisan gillar da Isra’ila take yi a Gaza

February 21, 2026
Fitaccen furodusa Kunle Afolayan ya yi haɗin gwiwa da Jamhuriyar Benin kan shirya finafinai
Labarai

Fitaccen furodusa Kunle Afolayan ya yi haɗin gwiwa da Jamhuriyar Benin kan shirya finafinai

February 19, 2026
An naɗa Farfesa Tengya matsayin sabon shugaban Cibiyar Koyon Finafinai ta Ƙasa
Labarai

An naɗa Farfesa Tengya matsayin sabon shugaban Cibiyar Koyon Finafinai ta Ƙasa

February 15, 2026
Alƙali ya ci Samha Inuwa tara ko ta je kurkuku wata 6
Labarai

Alƙali ya ci Samha Inuwa tara ko ta je kurkuku wata 6

February 13, 2026
Hukumar EFCC ta kama jarumar Kannywood, Samha Inuwa, saboda goge majina da takardun naira
Labarai

Hukumar EFCC ta kama jarumar Kannywood, Samha Inuwa, saboda goge majina da takardun naira

February 3, 2026
Next Post
Shari’ar Zamfara: Ko gobe a ja daga, ba mu tsoron yin gaba-da-gaba da zaɓen inkwankilusib – Gwamna

Shari'ar Zamfara: Ko gobe a ja daga, ba mu tsoron yin gaba-da-gaba da zaɓen inkwankilusib - Gwamna

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!