ALLAHU Akbar! Mijin babbar furodusa a Kannywood kuma tsohuwar Shugabar Ƙungiyar Kwararru Masu Shirya Finafinai ta Nijeriya (MOPPAN), reshen Jihar Kaduna, Hajiya Fatima Ibrahim Ahmad (Lamaj), Alhaji Ibrahim Sa’idu Gamagira (Maje), ya rasu a daren jiya a Abuja.
Allah ya ɗauki ran shi a wani asibitin kuɗi mai suna Belam da ke Abuja, bayan jinyar tsawon watanni uku da ya sha fama da ita.

Marigayin, mai kimanin shekara 60 a duniya, ya rasu ya bar matar sa ɗaya da ‘ya’ya da dama.
Za a yi jana’izar sa da misalin ƙarfe 2:00 na rana a Babban Masallacin Ƙasa da ke Abuja.
Allah ya jiƙan shi da rahama, ya kuma albarkaci dukkan abin da ya bari, amin.