SHUGABAN Ƙungiyar Masu Shirya Finafinai ta Nijeriya (MOPPAN), Alhaji Maikuɗi Umar (Cashman), tare da Mataimakin sa na Arewa maso Yamma, Alhaji Bala Kufaina, sun ziyarci Babban Daraktan Hukumar Tace Finafinai ta Nijeriya (NFVCB), Dakta Shu’aibu Hussaini, a ofishin sa da ke Abuja.
Ziyarar ta kasance wani yunƙuri na faɗaɗa haɗin gwiwa domin bunƙasa masana’antar finafinai ta Kannywood.
A yayin tattaunawar, shugabannin MOPPAN sun miƙa takardar neman agajin kayayyakin aiki da kuma shirya taron ƙara wa juna sani, wanda zai ba da damar tattauna batutuwan da za su inganta harkokin masana’antar.
Wannan mataki yana daga cikin shirin MOPPAN na daidaita masana’antar da cigaban zamani, tare da inganta ayyukan da ke da alaƙa da finafinai.
Bugu da ƙari, sabon shugaban MOPPAN ya fara aiwatar da tsare-tsaren haɓaka masana’antar da inganta ƙwarewa a fannin shirya finafinai, kamar yadda ƙungiyar ta bayyana.