• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Tuesday, July 1, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

MOPPAN: Maikano ya yi wa Sarari raddi kan sukar da ya yi masa

by DAGA IRO MAMMAN
January 16, 2020
in Labarai
0
Abdullahi Maikano Usman: "Na ga ɓatanci iri daban-daban"

Abdullahi Maikano Usman: "Na ga ɓatanci iri daban-daban"

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram
TSOHON shugaban haɗaɗɗiyar ƙungiyar masu shirya finafinan Hausa ta Nijeriya, wato ‘Motion Picture Practitioners Association of Nigeria’ (MOPPAN), Alhaji Abdullahi Maikano Usman, ya sanar da shugaban ƙungiyar mai ci yanzu cewa zargin sa da ya yi na kasa taɓuka komai a zamanin mulkin sa kuskure ne. 
 
Maikano ya faɗa wa shugaban na yanzu, Dakta Ahmad Muhammad Sarari, cewa akasin abin da ake zargin sa da shi, a gaskiya ya yi abubuwa muhimmai waɗanda su ka ciyar da ƙungiyar gaba.
 
Maikano ya faɗi haka ne a cikin wata takarda da ya aika wa mujallar Fim ta i-mel a matsayin martanin sa ga Sarari kan zargin sa da kasawa da ya yi.
 
Idan kun tuna, a shekaranjiya Talata ne mujallar Fim ta buga labarin yadda Sarari ya ragargaji Maikano bayan sababbin zaɓaɓɓun shugabannin MOPPAN sun kammala taron su a Kano.
 
An zaɓi Sarari da sauran shugabannin MOPPAN ne a taron ƙungiyar da aka yi a ‘yan watannin baya a Dutse, babban birnin Jihar Jigawa, inda Sarari ya kayar da Maikano a zaɓen da aka yi.
 
Ga raddin da Maikano ya yi wa Sarari, kamar haka:
 
“Amsa Zuwa Ga Sarari
 
“Ina godiya ga Allah Maɗaukakin Sarki da ya ba ni iko na shugabanci ƙungiyar mu ta MOPPAN, sannan ina gode wa Allah da ya ba ɗan’uwa na Dr Sarari shugabanci a yanzu. Lokacin da ya ci zaɓe na yi sujudushushukar na gode wa Allah, sannan ni ne mutum na farko da ya taya shi murna. 
 
“Na ga ɓatanci iri daban-daban lokacin yaƙin neman zaɓe amma ban tanka kan ko ɗaya ba. Amma na ga abin da shugaba ya rubuta a ‘Kannywood Vanguard’ da kuma hirar da ya yi da ‘yan jaridu lokacin da ya cika kwanaki ɗari a kan karagar mulki. 
 
“Ina maka murna, amma zan ɗan yi gyara kan abin da ka ce domin akwai kurakurai. Na yi maka uzuri amma wajibi mu yi gyara.
 
“Ka ce babu takarda mai ɗauke da sunan ƙungiya. Idan ka na nufin ‘letter headed paper’, to ai da takardar na rubuta maka canjin ‘signatories’ na banki na aiko maka ka je aka canza ‘signatories’ a banki kamar yadda doka ta tanada. 
 
“Har ila yau, da  takardar mu ka rubuta neman izinin kai ziyara wajen Shugaban Ƙasa kuma ya amince, wanda a nan ne ya umurci a ba masu sana’a irin tamu kuɗaɗe waɗanda ake ta bi a halin yanzu. Da ma sauran rubuce-rubuce da mu ka yi. 
 
“Ka ce ‘yar takarda aka ba ka lokacin da aka yi maka ‘handover’. Ina tunatar da kai cewa ka buga mini waya ka na buƙatar ko da ‘yar takarda ce na rubuta maka na ‘handing over’. Ka amince kan cewa Sakatare-Janar ne ya kamata ya rubuta amma ni na taimaka na rubuta.
 
“Ina tuna maka cewa ba ma ‘yar takarda ba, shafi goma sha huɗu na rubuta maka na ‘handover’ sannan na faɗa maka cewa Sakatare-Janar zai rubuta bayani dangane da sakatariya domin shi ne shugaban sakatariya kuma haƙƙin sa ne. 
 
“Zan tsakuro kashi biyu ckin goma na bayanin da ‘handover’ ɗin ya ƙun sa.  
 
“1. Kiwon Lafiya: Na yi bayani ƙoƙarin da shugabanci na ya yi har aka ƙaddamar da tsarin kiwon lafiya ga mambobin ƙungiya ranar 17/4/18 sannan kuma da wurin da mu ka tsaya da kuma yadda za a ci gaba.
 
“2. Taron Ƙara Wa Juna Sani: Mun shirya taron ƙara wa juna sani mai taken ‘Film Making Opportunities and Challenges for the Film Maker’ wanda shugaban mu na farko, Malam Abdulkareem Muhammad, ya gabatar da ƙasida, haka ma shugaban NFC da na NFVCB da kuma jami’i daga bankin BOI wanda bankin na BOI ya taimaka mana  da kuɗi wanda sai da na cika Naira dubu ɗari daga cikin aljihu na sannan mu ka gudanar da taron. Shugaba Sani Mu’azu ya taimaka wajen tabbatar da wannan taro. Na yi bayanin yadda MOPPAN za ta ci gaba da cin moriyar BOI. 
 
“3. Taron NOUN: Haɗin gwiwa tsakanin MOPPAN da NOUN ƙarƙashin Farfesa Abdalla da kuma taimakon Malam Ibrahim Sheme.
 
 
“4. Ma’aikatar Kiwon Lafiya ta Najeriya: Na yi bayanin ziyarar MOPPAN da ƙoƙarin da mu ka yi na dawo da haɗin gwiwa tsakanin MOPPAN da ma’aikatar. Na kuma bada shawarar yadda za a iya ɗorawa, idan shugabancin ka ya ga dacewar yin hakan.
 
“5. Jawabai: Dukkan jawaban da na yi a matsayi na na Shugaba na wancan zamani a duk inda mu ka ziyarta da kuma ‘programmes’ da mu ka gudanar waɗanda za su sanar da kai abubuwan da su ka wakana.
 
“A cikin bayanan naka, ka faɗi cewa mun tarar da ofis amma mun bar MOPPAN ba ta da ofis. Shugaba, ina sanar da kai cewa a taron EXCO ɗin mu na farko Sakatare-Janar ya yi wa kowa bayani cewa ofis ɗin da MOPPAN ta ke amfani da shi, shi Sakataren ne ke biyan kuɗin haya. Yadda na sami ofis ɗin MOPPAN kenan. 
 
“A shekarar farko MOPPAN ta biya kuɗin haya sannan a shekara ta biyu ni ne na bayar da naira dubu ɗari kuɗin haya daga aljihun kamfani na, wanda har yanzu kungiya ba ta dawo mini da kuɗi na ba. Sakatare-Janar na ba ‘cheaque’ ɗin.
 
“Ka yi magabar yanar gizo. EXCO ɗi na ta amince da a ba Sakataren Yaɗa Labarai kuɗin da ya buƙata domin buɗe wa MOPPAN ‘website’, kuma an ba shi ta hanyar ‘cheaque’, kuma na san ya yi iya ƙoƙarin sa duk da yake dukkan EXCO ba su gamsu ba.
 
“Daga ƙarshe, ina tunatar da mu cewa duk abin da mutum zai faɗi, to ya faɗi gaskiya. 
 
“Shugaba, ina yi maka fatan alheri. Ina roƙon Allah ya sa a samu ƙarin cigaba a wannan ƙungiya tamu a zamanin ka, sannan shi ma shugaban da zai zo gaban ka Allah ya yi masa ko ya yi mata jagora, ya ƙara ɗaukaka mana wannan ƙungiya tamu abin alfaharin mu. 
 
“Kamar yadda shugaban mu na farko Malam Abdulkareem Muhammad ya ke cewa, ‘MOPPAN is greater than an individual’. 
 
“Zan yi amfani da wannan dama na jaddada ƙudiri na na taimaka wa MOPPAN gwargwadon hali a duk inda na sami kai na. 
 
“Ina kuma yi maka da sauran ‘yan ƙungiya albishir ɗin wani alheri da ke tafe da yardar Allah maɗaukakin Sarki.  Allah ya taimake ka da dukkan masu wannan sana’a tamu, ya kuma ɗaukaka darajar  masana’antar tamu. Allah ya kuma jiƙan magabatan mu.
 
Naka, Abdullahi Maikano Usman.
 
Alhamdu lillah.”

Loading

Tags: MOPPAN
Previous Post

Sarari: Za mu gyara lalacewar da MOPPAN ta yi a mulkin Maikano

Next Post

Rashida Lobbo: Aure na yi a Thailand, shi ya sa na bar Kannywood

Related Posts

Ƙungiyoyin harkar fim, KAFIGAN da MOPPAN, sun yi wa Rahama Sadau ta’aziyyar rasuwar mahaifin ta
Labarai

Ƙungiyoyin harkar fim, KAFIGAN da MOPPAN, sun yi wa Rahama Sadau ta’aziyyar rasuwar mahaifin ta

June 23, 2025
Mahaifin Rahama Sadau mutumin kirki ne da son jama’a, inji Yerima Shettima
Labarai

Mahaifin Rahama Sadau mutumin kirki ne da son jama’a, inji Yerima Shettima

June 22, 2025
Yadda mahaifin mu ya rasu kwana ɗaya bayan ya dawo daga Makkah – Abba, yayan Rahama Sadau
Labarai

Yadda mahaifin mu ya rasu kwana ɗaya bayan ya dawo daga Makkah – Abba, yayan Rahama Sadau

June 22, 2025
Mahaifin Rahama Sadau ya rasu kwana 1 bayan ya dawo daga aikin Hajji
Labarai

Mahaifin Rahama Sadau ya rasu kwana 1 bayan ya dawo daga aikin Hajji

June 22, 2025
Masanin harshe, Korao Hamadou ya gabatar da haruffan rubutun Hausa na asali a taro a Kano
Labarai

Masanin harshe, Korao Hamadou ya gabatar da haruffan rubutun Hausa na asali a taro a Kano

June 20, 2025
Kotu a Kano ta tsare Tsulange, matashin da ke tare titi yana wanka da yin shigar banza
Labarai

Kotu a Kano ta tsare Tsulange, matashin da ke tare titi yana wanka da yin shigar banza

June 20, 2025
Next Post
Auren soyayya: Rashida Lobbo tare da Abubakar

Rashida Lobbo: Aure na yi a Thailand, shi ya sa na bar Kannywood

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!