ƊAYA daga cikin jagororin masana’antar shirya finafinan Hausa, Malam Ahmad S. Alkanawy, ya bayyana cewa sun ƙara farfaɗo da tsohuwar Gidauniyar Kannywood domin wasu dalilai da su ka haɗa da samar da ayyukan jin ƙai ga ‘yan masana’antar da ma sauran jama’a.
Gidauniyar, wadda ke ƙarƙashin shugabancin Alhaji Auwalu Isma’il Marshall, an kafa ta ne shekara 16 da ta gabata domin bayar da tallafi ga mabuƙatan cikin masana’antar, amma ta shafe shekaru wajen goma ba a jin ɗuriyar ta.
Alkanawy, wanda ya na ɗaya daga cikin shugabannin gidauniyar, ya faɗa wa mujallar Fim manufar dawo da ita, inda ya ce: “Gaskiya da man wannan gidauniyar ta na nan domin tun da aka kafa ta a 2006, ta yi abubuwa da dama na taimakon jama’a, musamman ‘yan fim, a wancan lokacin.
“To, a yanzu ganin yadda masana’antar ta bunƙasa da kuma halin da aka shiga mu ka ga ya kamata a tayar da ita domin aikin ta ya ci gaba.”
Daraktan kuma furodusa ya ƙara da cewa, “A yanzu za mu faɗaɗa ayyukan gidauniyar, ba sai masu ƙaramin ƙarfi ba har ma masu kuɗi za su yi wani aikin da zai kawo cigaba a masana’antar, to za mu shige masu gaba domin ganin sun yi nasara, domin nasarar su ta ɗmu ce kuma ta masana’antar ce duka.
“Sannan za mu taimaka wa matasan mu da su ke shigowa harkar, su na da basira, amma rashin kula da su sai su kasa yin amfani da basirar su a wajen da ya dace, hakan sai ya jawo su yi abin da za su zubar da ƙimar masana’antar.
“Sannan za mu taimaka wa marayu da masu ƙaramin ƙarfi na cikin ta hanyar kula da lafiyar su da sauran buƙatu na rayuwar su.
“Kuma su ma jama’a akwai shirin da mu ka yi na kai tallafi kamar gidajen marayu da asibitoci, da sauran su, domin ko a baya farkon wannan gidauniyar an ga yadda mu ka yi amfani da ita wajen samar wa mutanen Nijar gudunmawa a shekarar da su ka shiga wani hali na yunwa, don haka a yanzu ma mu na da shirin taimakon jama’a ta ƙarƙashin wannan gidauniyar ta duk hanyar da ta dace.”
Daraktan ya yi kira ga ‘yan fim da su bai wa gidauniyar haɗin kai domin cimma nasarar da ake buƙata.