• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Thursday, May 14, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Za a ƙaddamar da wasan kwaikwayo kan rayuwar Sarki Khalifa Sanusi II a ranar 6 ga Agusta

by DAGA ALI KANO
August 1, 2022
in Labarai
1
Tambarin wasan daɓe na 'Emir Sanusi: Truth in Time'

Tambarin wasan daɓe na 'Emir Sanusi: Truth in Time'

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

WANI kamfanin shirya finafinai da ke Legas mai suna ‘Duke of Shomolu Productions’ ya bayyana cewa a ranar 6 ga Agusta, 2022 zai ƙaddamar da wasan kwaikwayo na daɓe wanda ya shirya kan rayuwar tsohon Sarkin Kano, Khalifa Muhammadu Sanusi II.

Wasan, mai taken, ‘Emir Sanusi: Truth in Time’, za a ƙaddamar da shi ne a ɗakin taro na Shehu Musa ‘Yar’Adua Centre da ke Abuja.

Khalifa Sanusi II shi ne Sarkin Kano na 14 a daular Fulani, kuma zai halarci taron da kan shi.

‘Yan wasa su na atisayen wasan ‘Emir Sanusi: Truth in Time’

A sanarwar da kamfanin da ya shirya diramar ya bayar, ya bayyana sarkin da cewa, “Mutum ne mai tsage gaskiya komai ɗacin ta, kuma ba ya da tsoro, mai zummar kawo sauyi irin na zamani, mai son ganin an inganta rayuwar ƙananan yara mata, sannan kuma malami ne.”

Ya ƙara da cewa shi wannan wasan kwaikwayo da aka shirya, “zai yi magana ne kan yanayin rayuwar sarauta ta Sarkin da kuma kakan sa a daidai lokacin da ake adawa da shi kamar yadda wasu mutum biyu da su ka yi aiki na kurkusa da su su ka bayyana.”

Haka kuma masu shirya wasan sun ce wannan shi ne karo na farko da babban mutum kamar Khalifa Muhammadu Sanusi II zai hau kan dandamalin wasan kwaikwayo ya amsa tambayoyi a birane biyu a wata fitowa ta musamman da ɗan wasa Yemi Shodimu ya tsara.

Wasan zai nuno rayuwa da dirama da ƙulle-ƙullen da aka yi wajen tuɓe Sarki Sanusi daga sarautar sa, kuma an samu ingantattun bayanai kai-tsaye daga dogaran sarkin.

Fitaccen marubuci kuma masanin harkar wasan kwaikwayo ɗin nan, Farfesa Ahmed Yerima, shi ne ya rubuta diramar, kuma Mofoluwake Oriyomi Edgar ya ɗauki nauyi tare da tallafin Ahmed Mohammed Ahmed, Babangida Sule Junior, Fatima Wali-Abdurrahman da Kola Karim.

Manyan kamfanoni da bankuna sun bada tallafi wajen shirya wasan.

Mai Martaba Sarkin Kano na 14, Alhaji Muhammadu Sanusi II

Za a nuna wasan kwaikwayon a lokaci ɗaya a Cibiyar Shehu Musa Yar’Adua da ke Abuja da ƙarfe 4 da ƙarfe 6 na yamma a ranar 6 ga Agusta da kuma MUSON Centre da ke Legas a ranakun 6 da 7 ga Agusta, 2022.

Kuɗin tikitin shiga kallo N5,000 ne, sai na manya N20,000 da kuma na musamman N50,000 kowane mutum.

Loading

Tags: dramaEmir of KanoEmir Sanusi: Truth in TimeHistoryMUSON CentreplayProf Ahmed YerimaSarkin Kano Muhammadu Sanusi IIShehu Musa Yar'Adua Centre.
Previous Post

Mun dawo da Gidauniyar Kannywood saboda wasu dalilai – Alkanawy

Next Post

Matsalar tsaro: Rarara ya shirya taron yi wa ƙasa addu’a

Related Posts

Rasuwar dattijon Kannywood, Nura Shareef, ta girgiza ‘yan fim
Labarai

Rasuwar dattijon Kannywood, Nura Shareef, ta girgiza ‘yan fim

February 22, 2026
Daraktar fim ta ƙi karɓar awad saboda kisan gillar da Isra’ila take yi a Gaza
Labarai

Daraktar fim ta ƙi karɓar awad saboda kisan gillar da Isra’ila take yi a Gaza

February 21, 2026
Fitaccen furodusa Kunle Afolayan ya yi haɗin gwiwa da Jamhuriyar Benin kan shirya finafinai
Labarai

Fitaccen furodusa Kunle Afolayan ya yi haɗin gwiwa da Jamhuriyar Benin kan shirya finafinai

February 19, 2026
An naɗa Farfesa Tengya matsayin sabon shugaban Cibiyar Koyon Finafinai ta Ƙasa
Labarai

An naɗa Farfesa Tengya matsayin sabon shugaban Cibiyar Koyon Finafinai ta Ƙasa

February 15, 2026
Alƙali ya ci Samha Inuwa tara ko ta je kurkuku wata 6
Labarai

Alƙali ya ci Samha Inuwa tara ko ta je kurkuku wata 6

February 13, 2026
Hukumar EFCC ta kama jarumar Kannywood, Samha Inuwa, saboda goge majina da takardun naira
Labarai

Hukumar EFCC ta kama jarumar Kannywood, Samha Inuwa, saboda goge majina da takardun naira

February 3, 2026
Next Post
Dandazon jama'a a wajen taron na yau

Matsalar tsaro: Rarara ya shirya taron yi wa ƙasa addu'a

Comments 1

  1. Tahir Z. Uthman says:
    4 years ago

    TSUNTSUN DA YA KIRA RUWA SHI RUWAN KAN DOKA.
    SHI YANA SON AYIMASA BIYAYYA AMMA SHI YA RAINA KOWA.
    IN DA GASKIYA AYI MANA BAYANIN KUDI NAWA MARIGAYI ADO BAYERO YA BARI, KUMA YA AKAYI DADU?
    IN YANA DA GASKIYA YA FADA MANA SO NAWA AKA ZAUNA DASHI DON SULHUNTA TSAKANINSHI DA GANDUJE KUMA WAKE BADA HAKURI DA CEWA BA ZAI SAKAKE TAKALAR WANI BA?
    MU MUN DADE DA SANIN KAREN BANA SHIKE MAGANIN ZOMON BANA. KUMA ME LAYA YA KIYAYI ME ZAMANI👍🤝🙏

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!