RASUWAR jarumin Kannywood Umar Yahaya Malumfashi a daren shekaranjiya ta girgiza ‘yan fim da ma jama’ar gari, saboda ta zo kwatsam, ba zato ba tsammani. In ban da mujallar Fim ta yi hira da shi a bakin gadon sa na jinya a makon jiya, mutane ba su ma san ba ya da lafiya ba. Ashe ciwon ajali ne.
Da labari ya ɓulla cewa ya rasu, sai jama’a duk ta yi la’asar, aka shiga yi masa addu’ar samun rahama. ‘Yan fim sun yi ta ɗora hoton sa a soshiyal midiya, ciki har da hotunan da su ka ɗauka tare da shi.
Da yawan su sun bayyana alhinin su ga mujallar Fim kan wannan babban rashi da mu ka yi.
Tsohon ɗan wasa wanda ɗan ajin su marigayin ne a fagen wasan kwaikwayo, Alhaji Isa Bello (Ja), ya shaida wa mujallar Fim cewa: “Babu shakka, rashin Umar Yahaya Malumfashi abu ne da ya shafi kowa da kowa, a matsayin sa na mai faɗakarwa, domin ya bayar da gudunmawar da ba za a manta da shi ba.
“Ni Umar Yahaya Malumfashi amini na ne, kuma har mun zama ‘yan’uwa, domin da iyali na da nasa mun haɗa su zumunci.
“Mutum ne shi da ba ya wasa da addini; duk inda ya samu kan sa lokacin sallah ba ya wuce shi, don mun daɗe tare da shi tun farkon zuwan sa Kano. Don haka ni a matsayi na na wanda ya ke da kusanci da shi, zan iya cewa ni aka yi wa rashi.
“Ina fatan Allah ya jiƙan sa, ya kyautata makwancin sa, kuma Allah ya albarkaci abin da ya bari.”

Shi ma tsohon ɗan wasa Malam Umar B. Hankaka, ya tofa albarkacin bakin sa dangane da rabuwar Umar Yahaya Malumfashi, in da ya faɗa wa wakilin mu cewa: “Gaskiya rashin Bankaura abu ne da ba zai yiwu a mayar da shi ba. Na san shi mu na tare da shi sama da shekaru talatin, tun mu na abokai, har mu ka zama ‘yan’uwan juna saboda kusancin da ke tsakanin mu. Kuma da yake kusan unguwar mu ɗaya da shi, duk iyalan mu su na zumunci.
“Mu dai tsakanin mu da shi sai addu’ar Allah ya yi rahama a gare shi.”
A tasa ta’aziyyar, jarumin barkwanci Aminu Baba Ari ya bayyana rasuwar Bankaura da cewa wani babban rashi ne a gare shi saboda kawun sa ne.
Ya ce: “Umar Yahaya Malumfashi uba ne a gare ni, domin ƙanen mahaifiya ta ne, don haka ba harkar fim ce ta haɗa ni da shi ba. Uba na ne.
“Kuma duk cikin dangin mu babu wanda ya kai shi zumunci. Duk inda ‘yan’uwa su ke sai ya je. Har dangin mu da su ke Jihar Gombe ya fi kowa zuwa.
“Mu na yi masa addu’ar Allah ya yafe masa zunuban sa.”
Haka su ma abokan aikin marigayin da ke Kaduna sun tofa albarkacin bakin su game da wannan babban rashi da Kannywood ta yi.
Da ta ke zantawa da mujallar Fim, tsohuwar jaruma Hajiya A’ishatu Umar Mahuta, ya ce a sanadiyyar marigayin ne ta fara harkar dirama.
Ta ce, “Wallahi ba ƙaramin rashi mu ka yi ba. Saboda ga ni na da shi na ƙarshe, ranar da Rarara ya kira mu, sai abokin tafiya Balarabe Ciroma, na ce masa Umar Malumfashi ban gan ka ba. Har mun kusa tashi sai ga shi. To da ma ni da shi, ɗan’uwa ne da ɗan’uwa. Kuma ni kai na ma shi ne sanadin fara fim ɗi na, tun 1988.
“To, sai ya ce min, ‘Ke ‘yar’uwa ga ɗan ki ku gaisa.’ Sai na ce masa, ‘Me ya same haka?’ Sai ya ce min, ‘Wallahi olsa na ke fama da ita.’ Sai na ce, ‘Rabon ma ka zo ka ɗan samu wani abu shi ya sa ka fito.’ Ya ce, ‘Wallahi.’ Ya ce, ‘Yanzu za ku koma?’ Na ce, ‘Yanzu za mu koma.’
“Ni dai wannan shi ne gani na da shi na ƙarshe. Kawai jiya da dare sai aka kira ni, yaron sa ya na kuka, ya ce baban su Allah ya yi masa rasuwa. So, in Allah ya kai mu za mu je a yi sadakar uku da mu.
“Allah ya jiƙan shi, Allah ya sa ya huta. Ku kuma Allah ya saka maku da alkhairi. Wallahi mutuwar sa ta girgiza ni sosai.”
Aminin marigayin, Malam Musa Muhammad Abdullahi, wanda shi ne ya gabatar da marigayin ya fara fim, cewa ya yi, “An yi babban rashi, kuma cike gurbin Umar Malumfashi sai an yi aiki ƙwarai a fagen harkar finafinai. Saboda ni ina tare da shi a nan Kaduna tun wuraren 1980s, kafin ya shiga Kwastan. Mu na tare da shi, mu na ta turka-turka. A taƙaice ma dai, shigowar sa harkar ina daga cikin wanda ya fara gabatar da shi a harkar finafinai, lokacin ina ‘ Arts and Culture’.
“Kuma haka aka yi ta tafiya, har ya je Kano, ya shiga Kwastan.
“To a taƙaicen taƙaitawa, ni da na samu kai na a cikin shirin ‘Kwana Casa’in’, wanda na ke ‘playing role’ na Auta Baita, shi ne silar zuwa na ‘Kwana Casa’in’ na Arewa 24. Saboda lokacin da aka nemi a cike gurbin Matawalle, aka zauna ‘management meeting’ aka ce ana neman mai yawancin shekaru kamar Matawalle, shi Umar shi ya kawo suna na, ya ce akwai Musa Muhammad Abdullahi daga Kaduna. Nan da nan aka aiko min da ‘invitation’, aka aiko min da ‘script’ na yi ‘audition’, har Allah ya sa dai ana bugawa yanzu kafin Allah ya karɓi ni ma nawa kwanan.
“Saboda haka babu abin da zan ce wa Umar Malumfashi sai Allah ya jiƙan sa, ya gafarta masa, ya raya iyalan sa, ya kuma daidaita duka zuri’ar sa, ya kuma sa Aljannar Firdausi ta zama makoma a gare shi.”
Shi ma jarumi Rabi’u Mohammed Rikadawa (Dila), wanda yanzu aka fi sa ni da Baban Ɗan Audu, ya ce, “Rasuwa sai a yi wa mamaci addu’ar Allah ya jiƙan shi, Allah ya gafarta mashi, Allah kuma ya yafe masa kurakuran sa.
“Ni kusan ‘the last time’ da mu ka haɗu da shi, a Kano, lokacin da aka yi wani taro na 13×13. A lokacin ina Dutse mu na shutin fim ɗin ‘Labari Na’, ‘season 5’, sai na shigo taron a gurguje haka, an kusa tashi. Na fito zan yi sallah, ga shi ya zo, sai ya ce min, ‘Ɗan’uwa ya aka yi?’ Na ce, ‘Ya ka ke?’ Ya ce, ‘Lafiya lau.’ Sai na ce masa, ‘Na ga kamar ba ka jin daɗi.’ Sai ya ce, ‘Wallahi ina fama da zazzaɓi. Ka gan ni ba na jin daɗi.’ Sai na ce, ‘Bari in yi sallah in dawo, sai mu yi magana.’
“To, na tafi, kafin in yi sallah in dawo shi har ya fita. Wannan shi ne rabuwar mu da shi. Ko lokacin da na ji ba shi da lafiya, ka san ina ayyukan kala-kala, in kaɗa Abuja, in kaɗa can, in kaɗa Kanon, to ni duk duk lokacin da ake batun rashin lafiyar nasa, wallahi ban shiga Kano ba, amma ina da ƙudirin in na shiga zan je in neme shi har inda ya ke.
“Kwatsam, sai ga Nasiru Gwangwazo ana ƙoƙarin ɗan haɗa abin da za a taimaka, har na yi magana da Nasiru Gwangwazon a kan wannan abin. To kuma kwatsam sai ga shi wannan abu ya faru.
“Sai dai kawai mu yi addu’ar Allah ya jiƙan shi, ya kuma gafarta masa.

“Gaskiya ya ba da gudunmawa a industiri iyakacin abin da zai iya. Kuma mun yi ayyuka da shi kala-kala.
“Da ya ke ya na da ƙwarewa, ka sani tun zamanin su Ƙasimu Yero, duk inda ka kawo shi a rol ba za ka yi wahalar tanƙwara shi ba, saboda da ma ya na da ƙwarewa.”