• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Wednesday, May 6, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Nazarin littafin ‘Tarkon Mut’a’

by DAGA AMINA HASSAN ABDULSALAM (AHA)
June 24, 2021
in Taurari
0
Nazarin littafin ‘Tarkon Mut’a’
0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

MANUFA: Daɓɓaƙa harshe da adabin Hausa
LITTAFI: ‘Tarkon Mut’a’
MARUBUCI: Bashir Yahuza Malumfashi
WALLAFAWA: Gizago Publishing Enterprises
SHEKARA: 2019
ISBN: 978-2149-99-3
SHAFUKA: 91

BAYANIN MANYAN TAURAI (Characterisation):

i. Nana: Ɗaliba ce kuma budurwa. Ta na zaune da iyayen ta, ta faɗa soyayya da wani saurayi kyakkyawa. Zaƙin soyayya ya kai ta ga yin auren mut’a da saurayi ɗan Shi’a mai suna Ɗandangi.

ii. Ɗandangi: Kyakkyawan saurayi, ɗalibi ne ɗan ƙwalisa mai aƙidar Shi’a kuma ya ƙware a auren mut’a.

TAƘAITACCEN BAYANI (Plot Summary):

Tun daga gabatarwa za a fara hakaito wa mai karatu gundarin abin da labarin ya ƙunsa, wato auren mut’a, inda mai gabatarwa ya ke nuni da ƙyamar auren mut’a da ma masu yin shi.

JIGO (Thematic structure):

Babban jigon labarin dai shi ne auren mut’a. Marubucin ya nutsa sosai wajen bayyana ƙyama ga auren mut’a tare da kafa hujjoji don nazarin mai karatu. Ya yi amfani da Nana wajen gabatar da hujjojin illar auren mut’a da irin matsalar da mace ka iya fuskanta musamman idan jabun ‘yar mut’a ce.

Daga nan kuma ya haska mana Ɗandangi cikakken ɗan Shi’a mai al’adar auren mut’a. Marubucin ya wakilta Ɗandangi a matsayin matashi mai yaɗa baɗala ko ɗaɓɓaka zina da sunan auren mut’a da aka halarta musu don samun rabauta a nan  duniya da ma lahira.

Zahra’u (ƙaramar tauraruwar) ta na magana ne da muryar malaman sunna tare da hujjojin haramta auren sunna.

SALO (Style): An yi amfani da salo mai armashi da jan hankali. 

JERANTAWA (Sequence of events): Akwai kyakkyawar jerantawa tare da amfani da salon waiwaye (flashback). Marubucin ya kai makaranci ƙololuwar labari ba tare da zaren labarin ya kuɓuce masa ba.

MANUFAR LABARI:  A nawa ra’ayin, ba zan kira labarin da labarin nishaɗi kai-tsaye ba, domin babbar manufa ita ce faɗakarwa da tsawatarwa.

WARWARAR JIGO: An feɗe wa mai karatu tare da warware jigo cikin harshe mai sauƙi. Darasi ya bayyana a ƙarshe.

HUJJOJIN KARE MUT’A:A littafin, marubucin ya nuna cewa ‘yan Shi’a su na kare auren mut’a  da wasu madogarai ko hujjoji kamar haka:

1. A littafin su mai suna ‘Man La Yahduruhul Faƙih’, wai Imamin su na shida, Abu Abdullahi Jafar Sadik, ya ce, “Lallai mut’a addini na ce kuma addinin iyayen ta Ahlul Baiti…”

2. Daga cikin falalar mut’a akwai gafarta zunubai.

3. Wanda ya fita daga duniya bai yi mut’a ba zai zo ranar Alƙiyama ya na mai yankakkiyar daraja.

4. Mace ba za ta yi gado ba, ba za a kuma gaje ta ba, kuma ba a sakin ta. A asirce ake auren ta, ba waliyyi ba shaidu. Sannan za a yi jinga, zai iya kasancewa na awa ɗaya ko kwana ɗaya ko wata ɗaya  zuwa tsawon lokacin da su ka tsadance, d.s.s

5. Ana mut’a da matar aure ko bazawara amma budurwa sai in ta kai shekara goma (wannan ya fito ne a gabatarwar littafin).

Sannan kuma idan aka nutsa cikin labarin, akwai inda Ɗangwaggo ya kulluɓe (Taƙiyya) Zahra’u ya aure ta, sai daga baya ya bayyana aƙidar sa. Sun fara rigima ne a kan cewa:

(a) Ta ba wa abokin sa aron farjin ta, Shi ma abokin zai ba da aron farjin matar sa.

(b) Ya buƙaci saduwa da ita ta dubura.

(c) Ya kuma sake buƙatar ta amince ya yi mut’a da ƙanwar ta wacce ta zo yin kwanaki a gidan.

(d) Maƙwabci zai iya ba da ajiyar matar sa idan tafiya ta kama shi,  a yi abin da za a yi da ita.

(e) Sannan ɗan da aka haifa ta auren mut’a ya fi albarka.

TAMBAYOYI:

(1) An bayyana mana cewa Nana ta sami juna biyu amma Ɗandangi ya ƙi amincewa da cikin bare su yi aure na da’imun. Don haka sun je zubar da ciki a wani asibiti inda hatsaniya ta kusan ruftawa da su a asibitin. A garin tsira da rai, mota ta kaɗe su, cikin Nana ya zube amma Ɗandangi ya rasa ƙafafun sa. 

A nawa ra’ayin, hukuncin ya yi bambaraƙwai, domin akwai waɗanda ba sa Shi’a bare mut’a amma a gidan karuwai su ke kwana don ɗaure wa zina ƙugu. Kyautuwa ya yi a ce ya kamu da cututtukan zina, hakan zai fi tsoratarwa.

2. Kowane ɗan Shi’a na hakika ya yi amanna da auren mut’a amma ban taɓa jin luwaɗi na daga aƙidar su ba. Ko akwai hujjar hakan ko kuwa wai wai ne daga bakin mutane?

(3) Duk ɗan Shi’a ya na kiran kan sa Musulmi, to me ya sa marubucin ya ke ta kiran aƙidar Shia da “addini”?

* Amina Hassan Abdulsalam (AHA) marubuciya ce da ke Kano

Loading

Tags: Adabin HausaAmina Hassan Abdulsalam (AHA)Auren mut'aBashir Yahuza MalumfashiHausa booksMut'a marriageNigerian ShiitesShi'aShiite marriage
Previous Post

Mahaifiyar jarumi AS Muhammed ta kwanta dama

Next Post

Rajistar masu zaɓe: INEC ta ƙaddamar da gidan yana yayin damuwa kan tsaro

Related Posts

Abin da ya sa aka daina gani na a Kannywood – Ummi Duniyar Nan
Taurari

Abin da ya sa aka daina gani na a Kannywood – Ummi Duniyar Nan

August 24, 2025
Jaruma Hauwa Musa Adam
Taurari

Ina son zama mai taimakon al’umma — jarumar Kannywood Hauwa Musa Adam

August 14, 2025
Na fi so in fito a matsayin masifaffiya a fim, inji Fa’iza Abdullahi
Taurari

Na fi so in fito a matsayin masifaffiya a fim, inji Fa’iza Abdullahi

December 25, 2024
Fim ɗi na mai suna ‘Baban Ladi’ na ja sosai, inji sabon furodusa Razaki jarumin ‘Daɗin Kowa’
Taurari

Fim ɗi na mai suna ‘Baban Ladi’ na ja sosai, inji sabon furodusa Razaki jarumin ‘Daɗin Kowa’

November 25, 2023
Sayyada Raihan Imam Ahmad (Ƙamshi)
Taurari

Fim riga ce ta arziki – Raihan Imam Ƙamshi

November 20, 2023
Saratu Abubakar
Taurari

Yadda ɗaukaka ta sa na ke rufe fuska – Saratu Abubakar

October 1, 2023
Next Post
Rajistar masu zaɓe: INEC ta ƙaddamar da gidan yana yayin damuwa kan tsaro

Rajistar masu zaɓe: INEC ta ƙaddamar da gidan yana yayin damuwa kan tsaro

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!