A YAU Talata wata kotun magistare a Kano ta soke shari’ar da gwamnati ke yi da fitaccen mawaƙin Kannywood Naziru M. Ahmad sakamakon bada haƙuri da ya yi.
Hukumar Tace Finafinai Da Ɗab’i ta Jihar Kano ce ta gurfanar da mawaƙin a kan tuhumar ya fitar da wasu waƙoƙi biyu a bara ba tare da izinin ta ba.
Idan kun tuna, kwanan nan aka sake gurfanar da Naziru (mai laƙabin Sarkin Waƙar Sarkin Kano Muhammadu Sanusi) a kotu bisa zargin ya karya sharuɗɗan belin da kotu ta ba shi a bara.
Magoya bayan sa sun danganta kes ɗin da cewa duk siyasa ce shugaban hukumar, Alhaji Isma’il Na’abba (Afakallah) ya ke yi, amma Afakallah ɗin ya musanta hakan.
Da aka koma kotu a yau, lauyan gwamnati, Barista Wada A. Wada, ya gabatar da takardar ban-haƙurin Naziru ga alƙali, kuma ya sanar da shi cewa bisa ga wannan takarda yanzu an yi sulhu, gwamnati ba ta da sauran ja, kuma ta na so a soke shari’ar.
A takardar, wadda mujallar Fim ta samu kwafe ɗin ta, Naziru ya ce: “Tare da girmamawa, ni Naziru M. Ahmad wanda ake zargi da taka dokar Ma’aikatar Tace Finafinai da Ɗab’i ta Jahar Kano kan sakin wasu kundin waƙoƙi guda biyu da na fitar ba tare da sahalewar hukumar ba kuma har ta kai mu ga zuwa kotu, ni Naziru M. Ahmad ina so na miƙa saƙon ban-haƙuri a kan abin da ake tuhuma ta da shi da kuma yin nadama a kan abin da na gudanar ya janyo.
“Mu na roƙon Allah ya taimake mu ya kuma zaunar mana da Jahar Kano lafiya da ma ƙasa baki ɗaya.
“Kazalika ina dai ƙara miƙo saƙon ban-haƙuri.”
Jin buƙatar lauyan gwamnati, sai Mai Shari’a Aminu Muhammad Gabari, ya tambayi Naziru sahihancin wannan takarda, inda shi kuma wya amsa da cewa ba shakka shi ne ya rubuta ta da hannun sa.
Nan take alƙalin ya soke shari’ar, kuma ya sallami Naziru.
Wata majiya ta shaida wa mujallar Fim cewa kafin a cimma wannan mataki sai da Naziru ya buƙaci a kai shi wajen Gwamnan jihar, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, domin ya bada haƙuri don a yafe masa.
An yi zaman da mawaƙin da gwamna tare da wasu muƙarraban gwamnati, inda Nazirun ya bada haƙuri kuma ya nemi afuwa, tare da jaddada wa gwamna cewa abin da ya aikata kuskure ne.
A nan aka yi matsayar cewa an yafe masa, amma ya je ya rubuta takardar afuwa a rubuce ya kai wa kotu.
Majiyar mujallar Fim ta ce an faɗa wa alƙalin a ofishin sa matsayar da aka cimma a gaban gwamna.
“Shi ya sa da aka shiga kotun ba a yi wani daɗewa ba aka fito,” inji mai ba mu labarin, wanda ya halarci zaman kotun a yau.
Sai dai bayan an fito daga kotun, mujallar Fim ta tuntuɓi aminin Naziru, wato fitaccen jarumi Mustapha Sharu (Nabraska), don jin abin da zai ce kan wannan lamari.
Nabraska gatse ya yi wa Afakallah, ya na faɗin: “Shi wanda ya so a ba wa haƙurin ba mu ba shi ba, wato shi mai neman sunan, wato Afakallah. Sai mu ka yi amfani da wannan damar mu ka ba wa gwamnatin Kano haƙuri.”