MA’AIKATAR Al’adu da Watsa Labarai ta Saudi Arebiya ta bayyana cewa ta bada lasisi a karo na farko ga wani kamfanin Amurka mai suna AMC domin ya rika gudanar da gidajen sinima a kasar.
Ministan Al’adu da Watsa Labarai, Awwal Alawwad, ya fada cikin wata sanarwa a ranar Laraba, 4 ga Afrilu, 2018 cewa kamfanin AMC zai bude gidan sinima na farko a Saudiyya a Riyadh, wato babban birnin kasar, a ranar 18 ga Afrilu.
Ya kara da cewa, “Bada wannan lasisi na farko wata dama ce ta bude hanyoyin samar da kasuwa ga masu shirya finafinai.”
Alawwad ya kara da cewa kasuwar finafinai a Saudiyya babba ce domin kuwa yawancin al’ummar kasar matasa ne ’yan kasa da shekara 30 wadanda kuma su ka zaku su rika kallon finafinan su a gida.
Tun a watan Disamba ne hukumomin Saudiyya su ka bada sanarwar cewa za su sake soke dokar da su ka sa kan gidajen sinima shekaru 35 da su ka gabata.
A cewar ministan, Saudiyya na sa ran cewar za a gina kimanin sinimu guda 350 masu dauke da dakunan kallo guda 2,500 kafin shekara ta 2030.
Wannan mataki ya na daga cikin tsare-tsaren kasar na shirin Mahangar Shekarar 2030 wanda Yarima Mai Jiran Gado Muhammad bin Salman ya kaddamar da nufin sama wa ’yan kasuwa damar yin huldodi a kasar tare da habaka tattalin arzikin kasar.
Shi dai Yarima Muhammad bin Salman, dan shekara 32, shi ne ake kyautata zaton ya sa aka cire dokar nan da ta hana mata tuka mota da kan su a kasar, wanda zai fara aiki daga watan Yuni mai zuwa.
Kwanan nan kuma ya bayyana cewa saka hijabi bai zama tilas ba in dai za su rika yin shigar da su ke ganin ta kare mutuncin kan su.
Rufe gidajen sinima da aka yi, da hana mata tuki, da kuma tilasta saka hijabi a shekarun baya duk dokoki ne da aka kafa a bisa fatawoyin wasu malaman kasar.
Masu lura da al’amuran yau da kullum sun ce soke wadannan dokoki wani mataki ne da Saudiyya ke dauka don sauya kallon da ake mata na kasa mai tsattsauran ra’ayin addini.
![]()







