• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Monday, June 2, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Rarara ya kai agajin ciyarwa ga sama da mutum dubu goma a garin su

Nan da wata shida talauci zai zama tarihi, inji shi

by ABBA MUHAMMAD
August 19, 2024
in Labarai
0
Rarara ya kai agajin ciyarwa ga sama da mutum dubu goma a garin su

Dandazon masu karɓar tallafin. A ƙaramin hoto, Rarara yana ba wani dattijo damen kuɗi

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

 

Dandazon masu karɓar tallafin. A ƙaramin hoto, Rarara yana ba wani dattijo damen kuɗi

SHAHARARREN mawaƙi Alhaji Dauda Adamu Abdullahi (Rarara) ya yi rabon kayan abinci da kuɗi ga mutanen ƙauyen su na Kahutu da ke Ƙaramar Hukumar Ɗanja a Jihar Katsina.

Mawaƙin ya yi rabon kuɗi kimanin miliyan hamsin (N50,000,000) da kayan abinci ga sama da mutum 10,000 a wani gagarumin gangamin jama’a da aka yi a garin a shekaranjiya Asabar, 17 ga Agusta, 2024.

Rarara ya ba kowane mutum ɗaya kayan abinci da kuɗin cefane N5,000.

A wannan karon, mahaifiyar mawaƙin, Hajiya Halima Adamu, ta halarci filin da aka yi taron tare da jikokin ta, inda ta yi amfani da wannan damar ta yi wa jama’a godiya game da irin addu’o’i da gudunmawar da suka ba ta a lokacin da ‘yan bindiga su ka yi garkuwa ita kwanan baya.

Mata sun yi cikar ƙwari a wajen rabon tallafin a Kahutu

Lokacin da ya ke jawabi a wurin rabon, Rarara ya yi kira ga dukkan waɗanda su ka halarci taron da cewa, “Duk wanda ya zo wurin nan zai samu, har da waɗanda ba a gayyata ba. Don haka kowa ya ba da haɗin kai don a yi abin a kan lokaci.”

Haka kuma ya ce al’umma su ƙara haƙuri, nan da wata shida talauci zai zama tarihi a ƙasar in-sha Allahu.

Sannan ya ƙara da cewa, “Duk wanda ka gani a wurin rabon nan, shi ma ba haka ya so ba, domin shi ma ya na so a ce ya bayar ga mabuƙata.”

Hajiya Halima Adamu, mahaifiyar Rarara, tana miƙa godiya ga jama’a

Mujallar Fim ta ruwaito cewa a cikin wannan shekarar, Rarara ya yi irin wannan rabon aƙalla sau biyar daga watan azumi zuwa yanzu.

Da yawa mutane su na ganin irin wannan taimakon da mawaƙin ya ke yi wa al’umma ya na ɗaya daga cikin abin da ya sa har yanzu ya ke jan zaren sa a harkokin sa ta kowane ɓangare.

Rarara dai ya yi suna wurin taimakon al’umma, ba mutanen ƙauyen su kawai ba, har ma a cikin masana’antar Kannywood da kuma sauran jama’a na wasu jihohin.

Tarin buhunan kayan abinci da Rarara ya raba a lokacin taron

Duk da cewa ana cikin wani hali na matsin rayuwa a ƙasar nan, amma mawaƙin bai gaza ba wurin taimako.

A cikin ‘yan siyasar da ya ke hulɗa da su da kuma manyan masu arzikin ƙasar nan, ana iya cewa babu wanda ke kwatanta abin da mawaƙin ke yi.

Wani mutum rungume da tallafin da ya samu a taron

Loading

Tags: Dauda Abdullahi Kahutu RararaKahututallafi
Previous Post

Minista ya buƙaci kafafen yaɗa labarai na duniya su riƙa ruwaito gaskiya kan Nijeriya

Next Post

Ƙungiyar Kannywood Family ta yi tankaɗe da rairaya a kan ‘yan damfara

Related Posts

Ƙungiya ta ja kunnen gwamnatin Kano kan dakatar da finafinan Kannywood 22
Labarai

Ƙungiya ta ja kunnen gwamnatin Kano kan dakatar da finafinan Kannywood 22

May 20, 2025
Hukuma ta rufe gidajen gala a Kano har sai bayan Ramadan
Labarai

Gwamnatin Kano ta dakatar da haska finafinan Kannywood 22 a intanet da talbijin 

May 19, 2025
Sabuwa, matar Ɗanmaraya Jos, ta rasu
Labarai

Sabuwa, matar Ɗanmaraya Jos, ta rasu

March 28, 2025
Tsohon jarumin barkwanci, Ƙarƙuzu, ya kwanta dama
Labarai

Tsohon jarumin barkwanci, Ƙarƙuzu, ya kwanta dama

March 25, 2025
Kannywood ba ta taɓa ƙyama ta saboda addini na ko ƙabila ta ba — Prince Daniel
Labarai

Kalli inda Prince Daniel ya ce an ƙi shi a Kannywood saboda addini (bidiyo)

March 25, 2025
Kannywood ba ta taɓa ƙyama ta saboda addini na ko ƙabila ta ba — Prince Daniel
Labarai

Kannywood ba ta taɓa ƙyama ta saboda addini na ko ƙabila ta ba — Prince Daniel

March 25, 2025
Next Post
Ƙungiyar Kannywood Family ta yi tankaɗe da rairaya a kan ‘yan damfara

Ƙungiyar Kannywood Family ta yi tankaɗe da rairaya a kan 'yan damfara

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!