JARUMI a Kannywood, Malam Tijjani Faraga, ya bayyana irin halin kaɗuwa da ya shiga saboda rashin mahaifiyar sa da ya yi, wato Hajiya Rabi’atu Usman.
Da ya ke tattauna wa da mujallar Fim kwana uku bayan rasuwar mahaifiyar tasa, Malam Tijjani ya ce: “Gaskiya ban taɓa rashin wani ɗan’adam da ya kai mahaifiya ta ba. Tun lokacin da ta rasu a rikice na ke, gaskiya, domin mata ce da duk abin da ya same ni ko na je ne, abu ɗaya ta ke yi, ta ce mani, ‘Ɗaga hannu a yi addu’a’. Duk abin da ya dame ni ita na ke faɗa wa, kuma idan ta yi addu’a cikin hukuncin Allah sai in ga sauƙin abin.”
Hajiya Rabi’atu, mai kimanin shekara 89, ta rasu ne a ranar Juma’a, 14 ga Oktoba, 2022 a gidan ta da ke Unguwar Rogo cikin garin Jos, Jihar Filato, da misalin ƙarfe 12:45 na rana.
An yi mata sallah da misalin ƙarfe 2:05 a babban masallacin garin Jos.
Tijjani Faraga shi ne ɗan ta na huɗu.
Haka kuma ita babbar yaya ga Babban Limamin garin Jos, Sheikh Lawal Adam.
Wasu daga cikin ‘yan fim da su ka je masa ta’aziyya sun haɗa da Abdu Kano (Ƙarƙuzu), Rabi’u Rikadawa, Al-Amin Buhari, Usman Mu’azu, Salisu Officer, Murtala Madobi, Abubakar S. Shehu, Sani Ranjeet, Tanimu Akawu, Hamza Talle Maifata, Waziri Bado, Oshere, Habun Hajiya, Yusuf Khalid, Maijidda Abbas, Teema Makamashi da A’isha Aliyu.
Allah ya jiƙan Hajiya Rabi’atu da rahama.
Comments 2