• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Friday, June 6, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Rasuwar Nura Mustapha Waye ta sa mutanen da ba su magana da juna sun shirya, inji Lawan Ahmad

by DAGA ABBA MUHAMMAD
July 9, 2022
in Labarai
0
Marigayi Nura Mustapha Waye a wajen wani taro

Marigayi Nura Mustapha Waye a wajen wani taro

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

AN bayyana cewa mutuwar fitaccen daraktan fim ɗin nan mai dogon zango na ‘Izzar So’, marigayi Malam Nura Mustapha Waye, ta sa mutane aƙalla takwas waɗanda ba su ko ga maciji da juna a Kannywood sun shirya saboda kaɗuwa.

Haka kuma an bayyana marigayin a matsayin mutum mai tsoron Allah, wanda a kullum burin sa shi ne a aikata abin da ya dace da sunnar Annabi Muhammadu (s.a.w.).

Babban furodusan fim ɗin, Lawan Ahmad, shi ne ya bayyana haka a tattaunawar da ya yi da mujallar Fim, kwanaki kaɗan bayan rasuwar daraktan.

Mutuwar Nura, wadda ta faru a wani asibiti a Kano a safiyar Lahadi, 3 ga Yuli, 2022, babban rashi ne wanda ya ɗaga hankalin ‘yan fim da ma sauran jama’ar gari. Babu ma kamar shi jarumi Lawan Ahmad, wanda kusan shi ne wanda ya fi kowa kusanci da marigayin, musamman a cikin shekaru kamar biyu da su ka gabata da su ke shirya ‘Izzar So’ tare.

A hirar da ya yi kan wannan abin baƙin ciki da ya faru, Lawan ya faɗa wa wakilin mu yadda ya ji dangane da rasuwar aminin nasa. Ya ce, “Wannan babban rashi dole in yi haƙuri a kai, domin duk yadda na ke son Nura Allah da ya halicce mu da ni da shi ya fi ni son shi, saboda haka kowane irin baƙin ciki na ji dole in yi haƙuri. Saboda a cikin Alƙur’ani Allah ya faɗa cewa, ‘Fasbir sabran jamila’, ‘duk abubuwan da su ka faru da ku, ku yi haƙuri, haƙuri mai kyau’.

Nura masoyin Manzon Allah (s.a.w.) ne. Lawan Ahmad ne a hagu

“Saboda haka idan aka jarabce ka da arziki ko akasin haka, abin da ya kamata ka yi shi ne ka yi haƙuri, saboda idan Allah ya ba ka arziki shi ma jarabawa ne, don ana so a ga me za ka yi da shi in Allah ya ba ka. 

“Idan aka jarabce ka da akasin haka kuma, shi ma ka yi haƙuri ka gani ko za ka ci wannan jarabawar. Wannan shi ne.”

Da wannan mujallar ta tambaye shi ko abin da zai riƙa tunawa da marigayin, sai ya ce, “Abin da ke faɗo min a rai game da Nura, wallahi duk lokacin da Nura ya ga za ka yi wani abu na saɓo sai ya hana ka. Idan kuma ka riga da ka yi ne, wallahi ya riƙa yi maka faɗa kenan, sai ya ce maka abin nan da ka yi ba daidai ba ne komi ƙanƙantar sa. 

“Kullum ba shi da wani aiki da ya wuce kare maganar Allah (s.w.t.) da kuma kare maganar Annabi Muhammadu (s.a.w.). Wannan abin dai da ka ga ana yaɗawa a soshiyal midiya, ba shi da wani aiki fiye da wannan abin. 

“Kuma Nura ba shi da abokin faɗa, domin ko gulma ba ya yi. In kuma ka ga Nura ya yi maka maganar wani, ka tabbata wanin ya yi masa abin da ya ɓata masa rai, sai ya zo ya same ni ko wani da zai iya faɗa wa, ya ce ‘wane ya yi mani abin da ban ji daɗi ba’, in ba da haƙuri ne in ce ya yi haƙuri ne, in kuma na zuwa ne in je in samu wancan ɗin, sai in je in same shi in yi masa magana, in ce ‘ba ka kyauta ba, ka yi kaza, ka yi kaza.’ Kamar yadda shi ma ake ɗauko kes in wata matsala ta samu a zo a same shi a kawo masa ƙara, har sai ya warware. 

“In taƙaice maka, a wannan mutuwar da aka yi ta Nura, na rantse maka da Allah mutanen da ba su magana da juna sun kai kala takwas, duk sun shirya saboda mutuwar Nura, saboda mutuncin Nura da su ke gani da alkhairan da ya yaɗa a bayan ƙasa. Ni kai na akwai wadda ba ta magana da ni, ta zo ta ce mani in yi haƙuri, ta yi haƙuri ita ma. Na ce ‘babu komai da ma ni ban riƙe ki ba’. 

“Ka ga duk irin waɗannan abubuwan, in da shi mamacin bai shuka alkhairi ba, ko kuma ba a ga wasu abubuwa da ya yi masu kyau da ya bari ba, duk hakan ba za su faru ba, kuma duk ta sanadiyyar sa ne. 

“Wallahi mutane da dama sun bar wasu abubuwa da dama ta sanadiyyar rasuwar Nura saboda ta zamar mana izina, ta zamar mana darasi. Babu abin da ba ta zame mana ba.” 

A game da daɗewar tarayyar sa da daraktan, Lawan ya ce, “Gaskiya mun daɗe da shi, amma dai ba wani aiki mu ke yi da shi ba. Aƙalla mun kai kusan shekara bakwai zuwa takwas da Nura. Mun taɓa yin wani aiki da shi, sunan fim ɗin ‘A Sa Ni A Fosta’, sai mu ka yi wani aiki da shi amma na manta sunan fim ɗin. 

“Bayan wannan ba mu ƙara yin aiki da shi ba tsawon shekaru, sai kuma a cikin shekaru biyun nan mu ka fara ‘Izzar So’, shi kenan kuma Allah ya haɗa jinin mu, ya kuma haɗa kan mu da shi mu ka ci gaba da yi, ina ɗaukar nauyi, shi kuma ya na rubutawa, ya ba da umarni.”

Mutane da dama su na tunanin makomar ‘Izzar So’ bayan rasuwar Nura. Shin ko an samu giɓin da zai yi barazana ga cigaban fitowar shirin? Sai furodusan ya ce, “Ni a gani na gaskiya ba a samu giɓi ba, tunda aiki ne na Ubangiji. Aikin nan da ma Allah ke tafiyar da shi, kuma mun sha zama idan mu ka ga wata matsala za ta tunkaro, sai kuma Allah ya warware ta a cikin ɗan taƙaitaccen lokaci. Saboda haka rasuwar Nura, ni a gani na, babu wani giɓi da zai samu a cikin ‘Izzar So’. Saboda misali in Nura rubutawa ya ke yi, ya bada umarni, ni kuma na ke ɗaukar nauyi, kuma mu yi shekara biyu mu na irin wannan abu, ai ya kamata a ce na koyi wani abu ko ya ya ke a wurin shi, wanda ni ma a irin tunani na da iya basirar da Allah ya ba ni, da kuma irin yadda labarin ya ke zan iya kamantawa in ci gaba da ‘Izzar So’.

Nura Mustapha Waye tare da Ali Nuhu

“Kuma a zuciya ta ko ɗar ba ni ji ko dalilin da zai sa mu daina ‘Izzar So’ saboda Nura ya rasu. Saboda shi ma ya na kwance a kabarin sa, zai ji daɗin ci gaba da ‘Izzar So’ da mu ka yi. Domin ya ɗauko wani abu, Allah ya ɗauki rayuwar sa mu kuma mun ci gaba. Kuma zai yi alfahari da mu ko da a ranar tashin alƙiyama. 

“Kuma ko da a ce mun yi tunanin daina yin ‘Izzar So’, dole mu ci gaba da yi saboda mun ga irin tasirin da ya yi a kan sa, wanda ‘legacy’ ne babba, wanda kowa zai so a matsayin sa na Musulmi ya bar irin wannan tarihin. Wannan shi ne. Nura sai dai mu yi masa addu’a.”

Loading

Tags: daraktaIzzar SojarumiLawan AhmedmutuwaNura Mustapha Waye
Previous Post

Arafa: Mawaƙi Rarara na so masu hali su taimaki marasa galihu

Next Post

Rasheeda Maisa’a, Mansurah da Muhibbat sun yi wa K-WAN kishiya, sun kafa ƙungiyar mata ‘yan fim

Related Posts

An naɗa Shehu Hassan Kano shugaban riƙo na MOPPAN
Labarai

An naɗa Shehu Hassan Kano shugaban riƙo na MOPPAN

June 3, 2025
MOPPAN ta ba gwamnan Kebbi lambar yabo a madadin ‘yan fim
Labarai

MOPPAN ta ba gwamnan Kebbi lambar yabo a madadin ‘yan fim

June 2, 2025
Ƙungiya ta ja kunnen gwamnatin Kano kan dakatar da finafinan Kannywood 22
Labarai

Ƙungiya ta ja kunnen gwamnatin Kano kan dakatar da finafinan Kannywood 22

May 20, 2025
Hukuma ta rufe gidajen gala a Kano har sai bayan Ramadan
Labarai

Gwamnatin Kano ta dakatar da haska finafinan Kannywood 22 a intanet da talbijin 

May 19, 2025
Labarai

Gwamnan Kano ya ɗauki nauyin ‘yan Kannywood 5 zuwa Hajjin bana

April 17, 2025
Sabuwa, matar Ɗanmaraya Jos, ta rasu
Labarai

Sabuwa, matar Ɗanmaraya Jos, ta rasu

March 28, 2025
Next Post
Wasu daga cikin shugabannin AKAFA lokacin da su ka gudanar da taro a gidan Mansurah Isah da ke Unguwar Badawa Layaout a Kano

Rasheeda Maisa'a, Mansurah da Muhibbat sun yi wa K-WAN kishiya, sun kafa ƙungiyar mata 'yan fim

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!