SHUGABAN kwamitin zaɓen da majalisar gudanarwa ta Ƙungiyar Masu Shirya Finafinai ta Nijeriya (MOPPAN) ta zaɓa a ranar Lahadi, 8 ga Satumba, 2024 ya yi murabus.
Alhaji Bala Mu’azu Kufaina ya yi murabus ne a jiya Litinin ya yi wani taron gaggawa ta yanar gizo.
Haka kuma majalisar gudanarwar ƙungiyar ta yi gyare-gyare a cikin kwamitin zaɓen, bayan ta amince da murabus ɗin shugaban kwamitin.
Kakakin ƙungiyar, Malam Al-Amin Ciroma, ya ba da sanarwar haka a cikin wata takardar manema labarai da ya fitar a jiya.
Takardar ta ce, “Tsohon shugaban kwamitin, Alhaji Bala ya bayyana wasu dalilan da ba zai iya ci gaba da jagorantar kwamitin ba, kuma ya yi murabus bisa raɗin kan sa tun ba a yi nisa ba.”
“Yayin taron gaggawa da shugaban MOPPAN na ƙasa, Alhaji Habibu Mohammed Barde, ya kira ta yanar gizo, shugabannin na ƙasa sun yi nazarin bayanai da ƙalubale da tsohon shugaban kwamitin ya bayyana ya na fuskanta a lokacin taron, hukumar zartarwar ta ba shi izinin yin murabus ɗin, bisa la’akari da murabus na tsohon shugaban.”
Taron ya amince da cimma buƙatar kawo gyara da rage yawan membobin kwamitin zaɓen daga membobi 13 zuwa bakwai kacal, duba da cewa wataƙila yawan membobin 13 na farko zai iya ƙara jefa kwamitin zaɓen cikin waɗansu ƙalubale nan gaba idan ba a rage su ba.”
A ƙarshe, ‘yan majalisar gudanarwar sun zaɓi Alhaji Bello Achida (daga Sokoto) mai riƙe da muƙamin babban mai binciken kuɗi (National Auditor) a matsayin sabon shugaban kwamitin na zaɓe, a yayin da aka zaɓi Malam Ibrahim L. Ibrahim (daga Jihar Nasarawa) mai riƙe da muƙamin mataimakin shugaba a shiyyar Arewa-maso-tsakiya a matsayin sakataren kwamitin zaɓen.
Sauran membobin gyarararren kwamitin sun haɗa da wakilan industiri, kamar haka: Alhaji Abdul Amart (wakilin furodusoshi) da Hajiya Hadiza Mohammed (wakiliyar ‘yan wasa).
Sai kuma aka zaɓi shugabannin jihohi a kowace shiyya ta Arewa kamar haka: Alhaji Ado Ahmad Gidan Dabino, MON, shugaban MOPPAN (daga North-West); sai kuma shugaban MOPPAN na Jihar Yobe, Malam Khalifa (daga Arewa-maso-gabas); da kuma Alhaji Murtala Yakubu, shugaban MOPPAN na Jihar Binuwai (daga Arewa-ta-Tsakiya).
Kafin a rufe taron dai, shugabannin sun cimma matsaya cewa sauran membobin tsohon kwamitin da ragewar ta shafa za su kasance cikin keɓaɓɓun membobin da za su taka muhimmiyar rawa a lokacin zaɓen a matsayin membobin kwamitoci na musamman, waɗanda za su taimaka matuƙa wajen samun nasarar zaɓen.
MOPPAN ta ƙasa ta yi wa sabon kwamitin na zaɓe fatan alheri, tare da yin godiya ga sauran membobin tsohon kwamiti saboda da himma da jajircewar da su ka fara nunawa wajen gudanar da ayyukan zaɓen.
![]()







