• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Thursday, May 14, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Shugabannin Kannywood sun kafa kwamitin tsaftace masana’antar fim

by DAGA MUKHTAR YAKUBU
April 12, 2018
in Labarai
0
Wasu membobin kwamitin bayan an tashi daga taron

Wasu membobin kwamitin bayan an tashi daga taron

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram
WASU manyan masu ruwa da tsaki a masana’antar finafinan Hausa ta Kannywood sun kafa wani ƙaƙƙarfan kwamiti da zai riƙa bincike don gano matsalolin da masana’antar ta ke fuskanta da kuma hanyoyin da za a bi domin magance su.
 
Kwamitin, wanda ya tara masana daga ɓangarori daban-daban daga cikin masu gudanar da sana’ar ta fim, ya na da membobi 28.
 
Malam Bashir Mudi Yakasai ne shugaban kwamitin.
 
Kwamitin ya yi zaman sa na farko a ranar Laraba, 11 ga Afrilu, 2018 a Titin Lamiɗo da ke unguwar Nassarawa a Kano. A wannan zaman, wanda da dama cikin ‘yan kwamitin sun halarta, membobin sun tsara yadda kwamitin nasu zai tafiyar da aikin sa da kuma yadda ‘yan kwamitin za su rinƙa tuntuɓar junan su a duk lokacin da hakan ta taso.
 
Sakataren kwamitin, Malam Ahmad Abubakar, ya shaida wa mujallar Fim cewa, “Mun samar da wannan kwamiti ne domin ganin yadda harkar fim ta ke ci gaba a duniya ta zama wata sana’a mai zaman kan ta. 
 
“Sai dai duk da haka mu idan ka duba ita masana’antar tamu ɗimbin matsaloli sun hana ta ta ci gaba. Don haka ne mu ka samar da wannan kwamiti wanda ya haɗa ƙwararru da masana inda za mu haɗu mu yi aiki tare don ganin mun samar wa masana’antar hanyoyin ci-gaba.
 
“Duk da cewar an daɗe ana samar da hanyoyi na kawo ci-gaba a harkar, amma ina ganin wannan shi ne yunƙuri mafi girma da aka yi, kuma mu na fatan za mu cimma nasarar da mu ke nema a masana’antar.”
 
Da wakilin mu ya tambaye shi ko zuwa wanne lokaci wannan kwamitin zai kammala ya fitar da rahoto, sai ya ce, “To, shi da man kwamiti iri biyu ne: akwai mai lokaci, akwai mai marar lokaci; don haka mu namu ba mai lokaci ba ne. Za mu rinƙa zama ne mu na fitar da matsaya a kan wani ci-gaba ko matsala da ake fuskanta. Don haka aiki ne mu ka ɗauka ba mai ƙayyadajjen lokaci ba. 
 
“Mu na dai fatan samun haɗin kai daga masu gudanar da harkar da kuma masu yi mata fatan alheri.”
 
Mujallar Fim ta samu jerin sunayen ‘ya’yan kwamitin, kamar haka:
 
1. Bashir Mudi Yakasai – Shugaban kwamiti
2. Ahmad Abubakar – Sakataren kwamiti
3. Muhammad Gumel – Ma’ajin kwamiti
4. Ibrahim Mandawari
5. Nasir B. Muhammad
6. Shehu Hassan Kano
7. Bilkisu Yusuf Ali
8. Sani Sule Katsina
9. Habib Barde
10. Salisu Mu’azu
11. Rahama Abdulmajid
12. Al-Amin Ciroma
13. Salisu Muhammed Officer
14. Bala Kufaina
15. Umar Sani UK
16. Ali Jita
17. Sani Rainbow
18. Haruna Talle Maifata
19. Baballe Hayatu
20. Aisha Aliyu Tsamiya
21. Sunusi Oscar
22. Hauwa Waraka
23. A.A. Rasheed
24. Aminu S. Bono
25. Jamila Nagudu
26. Ruƙayya Dawayya
27. Misbahu M. Ahmad
28. Kabiru Shugaba
 
 

Loading

Previous Post

Auren Sadiya Kabala ya zo

Next Post

Mujallar Fim ta watan Afrilu ta fito da zafin ta

Related Posts

Rasuwar dattijon Kannywood, Nura Shareef, ta girgiza ‘yan fim
Labarai

Rasuwar dattijon Kannywood, Nura Shareef, ta girgiza ‘yan fim

February 22, 2026
Daraktar fim ta ƙi karɓar awad saboda kisan gillar da Isra’ila take yi a Gaza
Labarai

Daraktar fim ta ƙi karɓar awad saboda kisan gillar da Isra’ila take yi a Gaza

February 21, 2026
Fitaccen furodusa Kunle Afolayan ya yi haɗin gwiwa da Jamhuriyar Benin kan shirya finafinai
Labarai

Fitaccen furodusa Kunle Afolayan ya yi haɗin gwiwa da Jamhuriyar Benin kan shirya finafinai

February 19, 2026
An naɗa Farfesa Tengya matsayin sabon shugaban Cibiyar Koyon Finafinai ta Ƙasa
Labarai

An naɗa Farfesa Tengya matsayin sabon shugaban Cibiyar Koyon Finafinai ta Ƙasa

February 15, 2026
Alƙali ya ci Samha Inuwa tara ko ta je kurkuku wata 6
Labarai

Alƙali ya ci Samha Inuwa tara ko ta je kurkuku wata 6

February 13, 2026
Hukumar EFCC ta kama jarumar Kannywood, Samha Inuwa, saboda goge majina da takardun naira
Labarai

Hukumar EFCC ta kama jarumar Kannywood, Samha Inuwa, saboda goge majina da takardun naira

February 3, 2026
Next Post
Mujallar Fim ta watan Afrilu ta fito da zafin ta

Mujallar Fim ta watan Afrilu ta fito da zafin ta

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!