• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Tuesday, August 25, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Son rai ne ya sa Kannywood ta taɓarɓare – Mukhtar SS

by DAGA ABBA MUHAMMAD
September 10, 2022
in Tattaunawa
0
Mukhtar SS

Mukhtar SS

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

MUKHTAR SS ba sabon yanka rake ba ne a masana’antar finafinan Hausa. Jarumi necwanda ya daɗe ana gwagwarmaya da shi ta kowane fanni a masana’antar.

Mukhtar, wanda mazaunin Zariya ne a Jihar Kaduna, ya zanta da

mujallar Fim kan da halin da ya ke ciki game da harkar fim da kuma wasu abubuwa muhimmai da su ka shafi harkar.

FIM: Mukhtar SS, an daɗe ba a jin ɗuriyar ka a Kannywood. Ina ka shige ne?

MUKHTAR SS: Ina nan. Ka san ita industiri da ma haka ta ke, wani lokaci ka ga sunan ka ya na ta yawo, wani lokaci kuma ka ga ya na taƙaitawa. 

Ni dai abin da na ɗauka, rayuwar kowane ɗan fim da ya ke cikin harkar ta na iya canzawa a kowane lokaci, amma duk da haka mu na nan mu na ba da gudunmawa jefi-jefi ta ɓangarori da dama a cikin harkar.

FIM: Yanzu wane hali ka ke ciki, musamman ganin kai jarumi ne da ya fito daga garin Zariya?

MUKHTAR SS: Alhamdu lillahi! Duk wani jarumi da ya ke Zariya ya na fuskantar ƙalubale kala-kala. Sana’ar fim harka ce da ta ke da faɗi, kuma harka ce da ta ke da salo kala-kala a cikin ta. 

Mukhtar SS da Adam A. Zango

Wasu lokutan za ka ga wasu jarumai ciki, masu yin aikin ne, masu kuma kwaɗayin sana’ar ne, kuma su na duk wani abu da za su gudanar da wannan harkar. Amma kuma babban abin da ke faru akwai rashin gata na ubangida ko kuma rashin kuɗi da zai sa mutum ya bayyanar da basirar sa. Wannan sai ka ga ya dakusar da duk wani haske na mutum kwata-kwata, ya zama ba a ma san da shi ba.

FIM: Me ya sa ka rage fitowa a finafinai?

MUKHTAR SS: Haka ne. Lokacin da na fara bayyana a cikin fim, da ma irin fitowar da na ke yi har yanzu bai canza ba, sakamakon tun a farko za ka ga yanayin fim, manyan jarumai su su ke haskawa, kai dai za ka ɗauki kan ka ne a matsayin wani mai ruwa da tsaki a wasu ɓangarori na cikin harkar. Ka ga kai ka na ganin ka na ba da gudunmawa irin wanda aka san ka a ciki.

Haka za ka ga ana kiran ka ayyuka ka na fitowa ko da sau ɗaya ko biyu ne a cikin fim, za ka ci gaba da kallon kan ka a matsayin jarumi mai tasowa. A haka za ka kai wani matsayi da za a san cewa lallai kai ma ka ba da babban gudunmawa a cikin harkar.

FIM: A halin yanzu babu wata ƙungiya ta ‘yan fim da ta ke motsi a Jihar Kaduna. Wace hanya ka ke ganin za a bi don a samu gyara?

MUKHTAR SS: Tun kafin mu kawo wannan yanayin, za ka ji ana yawan surutu a kan rashin haɗin kai da sauran su. 

Akwai abubuwa na son rai da kuma abubuwa na son zuciya waɗanda su na daga cikin abubuwan da su ka yi jagoranci wurin taɓarɓarewar shuganci a Jihar Kaduna. Kowa na son a ce shi ne wane. Ba za a zauna a haɗa kai ba don ganin samun mafita da ciyar da harkar gaba ba. Hanyar da za a bi a gyara wannan lamari shi ne a samu haɗin kai, sannan a cire son zuciya da son mulki.

Duk wanda aka ce yau shugaba ne, ya kamata ya san cewa al’umma ya ke jagoranta, ba kan shi ba. 

Don haka dole sai an samu jagorori masu son cigaban harkar, waɗanda ba son mulki ne ya kawo su ba.

FIM: Ya alaƙar ka ta ke da sauran takwarorin ka jarumai na cikin garin Kaduna, Kano, Jos da sauran su?

MUKHTAR SS: Gaskiya ina da kyakkyawar alaƙa da kowane jarumi. Mun ɗauki kan mu ‘yan’uwan juna, mu na girmama juna matuƙa. In aka haɗu wuri ɗaya ba mu nuna wani bambanci a tsakanin mu. Mu na ƙaunar junan mu sosai. Sai dai mu ƙara yi wa Allah godiya. 

Amma kuma babu wani jarumi da na ke da alaƙa da shi na ƙut da ƙut kamar Ali Nuhu saboda ya na da kyawawan ɗabi’u, kuma ya jajirce wurin taimaka wa matasa don ganin su ma sun zama wani abu.

FIM: Kowa ya san ka ne a matsayin jarumi. Ko yanzu ka na shirya finafinai na kan ka?

MUKHTAR SS: E, ina shirya fim yanzu.

FIM: Aƙalla ka shirya finafinai kamar guda nawa yanzu?

MUKHTAR SS: Na shirya finafinai za su kai kamar biyar. A cikin su akwai ‘Matar Jarabi’, ‘Kafinta’ da dai sauran su.

FIM: Mecece shawarar ka ga ‘yan fim gaba baki ɗaya?

MUKHTAR SS: Shawarar ita ce mu ɗauka wannan sana’ar sana’a ce da za ta zama mana wata madogara da za mu taimaki kan mu. Duk wata sana’a ko aiki da za ka yi ita ma wannan harka za ta iya ba ka dukkan abin da ka ke nema idan ka kwantar da hankali. 

Mukhtar SS (a dama) tare da jarumi Nura Gangara

Sannan mu riƙe wannan harka hannu biyu ba da wasa ba. Haka kuma ya kamata a zaƙulo masu ilimi a cikin mu da za su taimaka wurin wayar wa da mutane kai wurin gane muhimmancin wannan sana’a da gudunmawar da ta ke badawa a cikin al’umma. Kuma ya kamata mu riƙa shirya taron wayar da kai da ƙara wa juna sani. Wannan zai taimake matuƙa.

FIM: Me za ka ce wa masoyan ka?

MUKHTAR SS: Ina godiya ga masoya da irin goyon baya da su ke ba ni da kuma addu’o’in da su ke yi min. Allah ya ƙara mana ƙaunar juna. Na gode.

Loading

Tags: Ali NuhujarumaiKannywoodMukhtar SSshugabanciZariya
Previous Post

Mata ‘yan fim da ke gidajen aure sun fi waɗanda su ka yi aure su ka fito yawa, cewar jaruma Zakiyya Ibrahim

Next Post

Ɗan Musa Gombe da Salmah Abdulazeez Chado sun saki hotunan kafin aure ba rungume-rungume

Related Posts

Abin da ya sa zan shirya fim mai dogon zango – Kabiru Jammaje
Tattaunawa

Abin da ya sa zan shirya fim mai dogon zango – Kabiru Jammaje

December 14, 2025
Abin da ya sa na fi shaƙuwa da marigayiya Hauwa Lawan Maiturare a duk aminai na – Bilkisu Yusuf Ali
Tattaunawa

Abin da ya sa na fi shaƙuwa da marigayiya Hauwa Lawan Maiturare a duk aminai na – Bilkisu Yusuf Ali

October 13, 2025
Tarbiyya a Kannywood: Bai kamata laifin wasu ya rinƙa shafar wasu ba – Maryam CTV
Tattaunawa

Tarbiyya a Kannywood: Bai kamata laifin wasu ya rinƙa shafar wasu ba – Maryam CTV

September 29, 2025
Rashin tsayayyen ubangida ke hana wasu jarumai yin suna – Mama Siddiqa
Tattaunawa

Rashin tsayayyen ubangida ke hana wasu jarumai yin suna – Mama Siddiqa

September 14, 2025
Bayan damfarar kuɗin magani: Halin da jaruma Halisa Muhammad take ciki yanzu
Tattaunawa

Bayan damfarar kuɗin magani: Halin da jaruma Halisa Muhammad take ciki yanzu

September 1, 2025
MOPPAN: Za mu haɗa kai da ‘yan siyasa don kawo cigaban Kannywood – Shehu Hassan Kano
Tattaunawa

MOPPAN: Za mu haɗa kai da ‘yan siyasa don kawo cigaban Kannywood – Shehu Hassan Kano

June 30, 2025
Next Post

Ɗan Musa Gombe da Salmah Abdulazeez Chado sun saki hotunan kafin aure ba rungume-rungume

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!