GALADIMA Yusufu mutane ke so, ba Alu ba. A garin Garko ya ke, kuma a can ya mutu. Kafin rasuwar sa, kowa ya yi amanna da cewa shi ne zai zamo Sarki, amma sai ciwo ya kama shi har ya mutu. Daga nan sai sarakunan bayin Sarki da ‘ya’yan su su ka ce, “Yanzu menene abin yi?”
Sai wasu su ka ce, “Abu ɗaya ya kamata mu yi, mutum ɗaya ne kurum zai iya jagorantar mu zuwa Kano. Shi ne Malam Babba (Alu kenan)”.
Daga nan su ka aika masa da saƙo, sannan su ka ɗora shi a gadon mulkin Yusufu.
Bayan sun yi haka, da dare su ka binne Yusufu da hasken fitilu. Su ka kawo Alu su ka zaunar da shi a kan karagar mulki, su ka yi masa naɗi.
Sai kuma su ka ce wa sauran fadawa kowa ya zo ya yi mubaya’a.
Ka ji yadda Alu ya zamo Sarki. Kuma shi ne dalilin da ya sa da ya ji Turawa na tafe ya tafi Sakkwato domin ziyartar hubbaren Shehu ta yadda Sarkin Musulmi zai amince da zamowar sa Sarki tare da goya masa baya.
Jama’ar gari, mafarauta da maharba ne su ka yi bore ga Sarki Alu a lokacin da Yaƙin Basasa ya ɓarke. Basasa a nan na nufin yaƙin da aka yi don ɗora Alu a kan karagar mulki. An yi shi ne a Ramli shekarar ‘Ba-Sa-Sha’. ‘Sha’ a ilimin Hisabi na nufin 1,000; ‘Sa’ na nufin 300, ‘a’ na nufin 1, yayin da ‘ba’ ke nufin 2. Idan ka haɗa lissafi zai ba ka shekara ta 1303 kenan bayan Hijira (daidai da 1894 miladiyya).
Ana kiran Alu da suna ‘Malam Babba’ (ma’ana babban malami) domin a wurin mu duk wani ɗan sarki Malam ne ko da bai koyi karatu ba. Amma da zarar Sarki ya ba shi wata sarauta sai a daina cewa Malam, a koma kiran sa da wannan sarauta.
Alu ya shiga Kano ranar wata Laraba. A wannan lokacin mutane da yawa sun bar Kano zuwa Kamri wajen Tukur, domin shi aka fi so.
An kashe Tukur ne a Gurum. Kamri da Gurum wasu ƙauyuka ne da ke kusa da juna a ƙasar Katsina. Na ji labarin cewa an ji masa raunuka sannan aka kawo shi gaban Sarki Alu. An ce Sarki Alu ya yi fushi sosai har ya ke cewa don me za su yi wa ɗan’uwan sa na jini haka? Sarki Alu ya ce, “Ku yi maza ku kawo masa ruwa ya sha.” Amma sai Sarki Tukur ya ce, “Kada a kawo min ruwa, azumi na ke yi. Ba zan sha ruwa ba.” A haka kuwa Allah ya amshi ran sa. Allahu Akbar!
A Gurum aka binne Sarki Tukur. Shi ya sa ake kiran sa da ‘Maje-Gurum’ kamar yadda ake kiran Galadima Yusufu ‘Maje-Garko’, kuma ake kiran Sarki Abbas ‘Maje-Nasarawa’.

Marigayi Alhaji Mahmud Ƙoƙi tafinta ne na Turawa, wanda ya kasance ya na cikin birnin Kano a lokacin da Yaƙin Basasa ya tashi, shi ne kuma ya ba mu wannan labari na sama. An rubuta labarin a cikin tarihin sa wanda aka wallafa a cikin 1977.
ASALIN YAƘIN BASASA
Sarkin Kano Abdullahi Maje-Karofi shi ne ɗa na biyu ga Sarkin Kano Ibrahim Dabo. Ya rasu a Karofi ta ƙasar Katsina a wajajen shekara ta 1882 miladiyya a hanyar sa ta zuwa garin Ƙauran Namoda domin ya ziyarci Sarkin Musulmi Umaru ɗan Aliyu da ke zaman Ribaɗi a lokacin a nan Ƙauran Namoda; shi ya sa ake masa laƙabi da ‘Maje-Karofi’. Sai ƙanen sa, Muhammad Bello (shi ma ɗan marigayi Ibrahim Dabo ne), ya hau karagar mulki.
An ce Sarki Muhammad Bello ya riƙa ƙoƙarin karɓe muƙamai daga hannun ‘ya’yan ‘yan’uwan sa ya na dasa ‘ya’yan sa na cikin sa. Sannan ya ƙara yawan jakadu masu tattara haraji, wanda hakan ya yi sanadiyyar jefa talakawa cikin matsi tare da janyo masa baƙin jini.
An ce tun a lokacin ya fara share wa ɗan sa Muhammadu Tukur hanyar zama Sarki idan ya rasu. Ya riƙa aikawa da kyaututtuka zuwa Sakkwato domin neman goyon bayan Sarkin Musulmi.
Shi kuwa Sarkin Kano Muhammadu Tukur, Sarkin Musulmi Abdurrahman (Ɗanyen Kasko) ne ya naɗa shi bayan mutuwar mahaifin Tukur ɗin, watau Sarkin Kano Muhammad Bello. Wasu sun ce bai kai shekaru arba’in ba aka naɗa shi sarauta, wasu kuma sun ce ba shi da karsashin riƙe mulki.
A lokacin, sai ɗan’uwan sa, Galadima Yusuf, wanda ɗa ne ga marigayi Sarkin Kano Abdullahi Maje-Karofi, tare da jama’ar sa su ka gudu zuwa garin Takai wanda ke kudu-maso-gabashin Kano.
Mutuwar Galadima Yusuf a Garko a kan hanyar su ta zuwa Kano tare da ƙwace sarauta ita ce sanadin ɗora Alu a madadin sa. Sannan a hankali su ka riƙa cinye garuruwan gabashin Kano da yaƙi, su na ƙarfafa rundunar su. A haka har sai da rundunar su ta yi ƙarfi, su ka shigo Kano a ranar wata Laraba, 19 ga Agusta, 1894, ana buga tambura na sarauta bayan ya samu nasara a kan Sarki Tukur, wanda ya gudu ya bar Kano don gudun zubar jinin mutanen Kano idan har za a buga yaƙi ya na cikin birnin.
Alu ya ci gaba da sarautar Kano har lokacin da Turawa su ka karɓe iko da ita tare da damƙa sarauta ga ɗan’uwan sa, Abbas.
Da fatan Allah ya jiƙan su duka, kuma da fatan za mu amfanu da darussan wannan labari, amin.
![]()







Sarki Kano Alu ya samo sunan malam Babba ne daga kakan sa,na sokoto, saboda sunan sa yaci