• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Saturday, June 7, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Tasirin kallon finafinan Hausa ne ya sa na musulunta – Rahma A. Ibrahim

by DAGA MUHAMMAD LAWAN RANO
July 30, 2021
in Labarai
0
Tasirin kallon finafinan Hausa ne ya sa na musulunta – Rahma A. Ibrahim
0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

WATA sabuwar jarumar Kannywood mai suna Rahama A. Ibrahim ta bayyana cewa kallon finafinan Hausa ne ya ba ta sha’awar shiga Musulunta tare da shigowa masana’antar finafinan Hausa don ta bada gudunmawar ta ta hanyar fim.

Matashiyar, ‘yar asalin garin Kumo da ke Jihar Gombe, ta bayyana haka ne a wata hirar bidiyo da aka yi da ita a tashar YouTube mai suna Matashiya.

A guntun bidiyon mai tsawon miti 2:05, wanda mujallar Fim ta wallafa a shafukan ta na Instagram da Facebook, Rahama ta ce kafin ta musulunta ɗin sunan ta Judith A. Ibrahim, kuma ita Kirista ce.

Rahama ta ce yadda masu shirya finafinan Hausa ke nuna yadda tsarin Musulunci ya ke tare da sanya wasu daga cikin ayoyin Alƙur’ani a finafinan shi ne abin da ya ja hankalin ta har ta kai ga ta sauya sheƙa zuwa Musulunci.

Jarumar ta bayyana hanyar da ta bi wajen ganin ta samu rabauta da Musulunci, ta ce, “Na taso a gidan mu wanda mu ke bin addinin Kiristanci. Ba mu taso mu na ba wa irin finafinan Hausa muhimmanci ba, amma duk da haka saboda ina yawan kallon finafinan Hausa, a ciki kuma da yake akwai irin ana ɗauko ayoyi a cikin Ƙur’ani, da yake da man gidan mu malamai ne na addinin Kiristanci, to akwai Ƙur’anin na Hausa da na Turanci, kasancewar babu Ƙur’ani na Larabci domin ba mu jin sa.

“Kasancewar a duk lokacin da aka faɗi wata aya a cikin Ƙur’ani, to kasancewar ina da shi, sai na buɗe na gani, sai na kwatanta shi da abin da ya ke cikin Baibul. 

“A haka ne har ya sa na wa’azantu, abin ya gamsar da ni. 

Rahama A. Ibrahim a cikin bidiyon hirar ta da Matashiya

“Na je na samu wani malami a unguwar mu, na yi masa bayanin ga abin da na ke so na shiga Musulunci, wanda da farko ma bai yarda ba.”

Rahama ta bayyana cewa ta haɗu da ƙalubale bayan shigar ta Musulunci wanda sai da ta kai har ta yi niyyar fita daga Musuluncin. Ta ce lokacin da mahaifiyar ta ta samu labarin cewa ta shiga Musulunci, sai da hankalin ta ya tashi matuƙa, har ta na cewa za ta kashe kan ta idan ɗiyar tata ba ta fita daga sabon addinin nata ba.

Ta ce, “Har na koma wurin malamin da ya musuluntar da ni na ce masa, ‘Malam, zan fita daga cikin addinin Musulunci. Me ake faɗa a fita?’ Sai irin ya yi min tsawatarwa, ya kuma ce min, ‘Wannan shi ne iya abin da za ki iya samu a nan duniya; wannan ƙalubalen shi ne ribar ki.’ Ya ce, ‘Ko da a ce manomi ne, za ki samu ya yi shuka ya yi shuka ruwa bai zo ba, amma kuma ya koma gobe. Shi ne ƙalubalen rayuwa. 

“Idan har Allah bai jarabce ki da wannan abin ba, ta ya za a yi ki gane addinin ya na da muhimmanci kuma ya na da ƙarfi?’ 

“Kuma a lokacin da na shiga cikin Musuluncin ba wai an tara jama’a ba ne. Na ce masa, ‘Ni ban son a tara jama’a saboda abu ne zan yi shi tsakani da Allah’.”

Finafinan da su ka ja hankalin ta har ta kai ga ta shiga Musulunci dai sun haɗa da ‘Ana Muslim’, ‘Ahlil Kitab’, ‘Ga Duhu Ga Haske’ da kuma ‘Asahabul Kahfi’.

Ganin bidiyon inda Rahama ta yi waɗannan bayanai ya faranta ran ‘yan Kannywood da sauran jama’a da dama, ta yadda duk wanda ya kalla sai ya ce, “Masha Allah,” kuma ya yi wa jarumar addu’ar fatan alheri.

Mujallar Fim ta samu labarin cewa uwar ƙungiyar ‘yan Kannywood, wato MOPPAN, ta shirya kiran jarumar domin ta karrama ta saboda wannan ƙwazo da ta nuna na shiga Musulunci tare da yin bayanin dalilin ta na shiga da yadda aka yi ta shiga ɗin ba tare da ta ɓoye gaskiyar al’amarin ba.

Loading

Tags: hausa filmsKannywoodMOPPANRahama A. Ibrahim
Previous Post

Burin Platinum Cinema shi ne ta haɓaka Kannywood – Babatunde Adeniji

Next Post

Ali Bulala Gusau ya koma aiki

Related Posts

An naɗa Shehu Hassan Kano shugaban riƙo na MOPPAN
Labarai

An naɗa Shehu Hassan Kano shugaban riƙo na MOPPAN

June 3, 2025
MOPPAN ta ba gwamnan Kebbi lambar yabo a madadin ‘yan fim
Labarai

MOPPAN ta ba gwamnan Kebbi lambar yabo a madadin ‘yan fim

June 2, 2025
Ƙungiya ta ja kunnen gwamnatin Kano kan dakatar da finafinan Kannywood 22
Labarai

Ƙungiya ta ja kunnen gwamnatin Kano kan dakatar da finafinan Kannywood 22

May 20, 2025
Hukuma ta rufe gidajen gala a Kano har sai bayan Ramadan
Labarai

Gwamnatin Kano ta dakatar da haska finafinan Kannywood 22 a intanet da talbijin 

May 19, 2025
Labarai

Gwamnan Kano ya ɗauki nauyin ‘yan Kannywood 5 zuwa Hajjin bana

April 17, 2025
Sabuwa, matar Ɗanmaraya Jos, ta rasu
Labarai

Sabuwa, matar Ɗanmaraya Jos, ta rasu

March 28, 2025
Next Post
Ali Bulala Gusau ya koma aiki

Ali Bulala Gusau ya koma aiki

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!