• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Saturday, June 7, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

‘Yan Kannywood sun farfaɗo da gidauniyar tallafa wa iyalan mamata a wurin taron addu’ar Bintu ta ‘Daɗin Kowa’

* Irin jinyar da ta yi, daga bakin kawun ta * Zan rinƙa tuna ta a kowane lokaci, cewar ɗan ta Abdullahi

by MUKHTAR YAKUBU
February 19, 2024
in Labarai
0
‘Yan Kannywood sun farfaɗo da gidauniyar tallafa wa iyalan mamata a wurin taron addu’ar Bintu ta ‘Daɗin Kowa’
0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

AƘALLA an tara kuɗi sama N60,000 domin tallafa wa iyalai da ‘yan’uwan jarumar Kannywood, marigayiya Fatima Sa’id (Bintu Daɗin Kowa) a wajen taron addu’ar cikar ta kwana bakwai da rasuwa.

Ƙungiyar Masu Shirya Finafinai ta Nijeriya (MOPPAN), reshen Jihar Kano, ita ce ta shirya taron a jiya Lahadi a Majalisar Matasa ta Tarauni da ke unguwar Gyaɗi-Gyaɗi a cikin garin Kano.

Tun da farko da ya ke bayani a game da taron, darakta Ahmad S. Alkanawy, ya bayyana manufar taron da cewa an shirya shi ne “don yin addu’a ga wannan ‘yar’uwa tamu, Fatima Sa’id, da Allah ya yi mata rasuwa da kuma sauran ‘yan’uwan mu da su ka rasu tun daga farkon kafuwar masana’antar zuwa yanzu.”

Ya ƙara da cewa: “Haka nan za mu yi addu’a ga marasa lafiyar mu da mu kan mu da kuma halin da ake ciki a wannan ƙasar.

Marigayiya Fatima Sa’id

“Sannan kuma sai gidauniya ko haɗa gudunmawar da mu ke yi domin bayar da tallafi ga iyalan mamata da kuma marasa lafiyar da mu ke da su a wannan masana’antar.

“Mu na fatan Allah ya jiƙan mamatan mu, waɗanda ba su da lafiya Allah ya tashi kafaɗun su.”

Shi ma a nasa jawabin, Farfesa Abdalla Uba Adamu ya jinjina wa ‘yan fim dangane da dawo da gidauniyar tallafawa iyalan mamata da marasa lafiyar da su ka yi, saboda abu ne mai kyau da aka samar da shi tun tsawon shekaru da su ka gabata.

Farfesa Abdalla Uba Adamu, Malam Ado Ahmad Gidan Dabino da sauran jama’a

Ya ce: “Gidauniyar tallafa wa iyalan mamata da marasa lafiyar ta fara ne tun a 2001 aka kafa ta; aka fara tafiya kamar da gaske, amma daga baya aka nemi gidauniyar da kuɗin da aka tara aka rasa. Wannan ya sa tafiyar ba ta je ko’ina ba.

“Amma a yanzu da aka dawo dai ita, ya kamata a yi mata tsarin da ba za a sake maimaita abin da ya faru a baya ba.
‘Don haka wannan gidauniyar a faɗaɗa ta ta yadda za a rinƙa samar da tallafi daga waje kamar ɓangaren gwamnati da kuma ƙungiyoyin bayar da tallafi na duniya.

Sashen mata a taron

“Kuma ya zama an bayar da kula da gidauniyar ga waɗanda za su tafiyar da abin cikin tsari ba tare da an koma gidan jiya ba.

“Kuma wannan taron da ake yi a ci gaba da yi, a ƙarfafa shi ta yadda zai zama abubuwan da aka tattauna a wajen a tabbatar an yi aiki da su ba wai kawai a yi taron a watse ba.

“Don haka a yanzu na bayar da gudunmawar N70,000 domin tallafawa: N20,000 ga iyalan Fatima Sa’id, N50,000 kuma ga gidauniyar domin ɗorewar ta.”

Shi kuwa Malam Bala Adamu, wanda ƙane ne ga mahaifiyar marigayiya Fatima, ya yi wa mujallar Fim bayani a game da tarihin rayuwar ta da rashin lafiyar ta da kuma yadda rasuwar ta ta kasance, inda ya ce: “Ita dai Fatima Sa’id shekarun ta 28. Ta yi aure, ta na da yaro guda ɗaya. Kuma a haɗarin da aka yi na aikin Hajji a shekarun baya a nan Allah ya yi wa mijin ta rasuwa, kuma tun da ya rasu Allah bai sa ta ƙara yin wani aure ba, daga nan sai kuma ta zo ta shiga harkar fim har zuwa wannan lokacin da Allah ya yi mata rasuwa.”

Malam Bala Adamu, kawun Fatima

Dangane da rashin lafiyar ta da rasuwar ta kuwa, cewa ya yi: “Gaskiya dai abin da ta yi ta fama da shi dai shi ne taifot da basir, wanda ta shafe kamar wata huɗu ta na rashin lafiyar kafin Allah ya karɓi ran ta.

“Kuma tsawon lokacin da ta yi ta na rashin lafiya mun kai ta Asibitin Zana, daga nan mu ka kai ta Asibitin Murtala.
“Mun zauna mun yi jinya, daga nan mu ka koma gida mu na tunanin ta samu lafiya saboda jiki ya nuna ta warke sosai, don ko a ranar Asabar na ke tambayar ta me ya ke damun ta? Ta ce ta warke sosai ta samu lafiya, sauƙi ya zo, kuma cikin daren Lahadin Allah ya yi mata rasuwa.

Dandazon jama’a a wurin taron

“Don haka mun ji alhinin wannan rasuwa, mun shiga damuwa. Amma kuma mun san iko ne na Allah, kowane mai rai sai ya ɗanɗana zafin mutuwa.

“Kuma alhamdu lillahi da ‘yan’uwa da abokan arziki da waɗanda su ke harkar fim tare kowa yabon ta ya ke yi. Mu ma a matsayin mu na iyayen ta yabon ta mu ke yi saboda babu abin da za mu ce da ita sai dai Allah ya yi mata rahama.

“Kuma abin da ya kawo mu wannan waje da mu ka ji an ce za a yi taro na yi mata addu’a, don haka aka sanar da mu, mu ka zo. Kuma da mu ka zo sai mu ka ga baya ga addu’a har da wata ƙwarya-ƙwaryar gidauniya da su ka samar.

“Sannan kuma yabon ta da su ka rinƙa yi bayan addu’ar ya ƙarfafa mana gwiwa, mun ji daɗi. Allah ya sa wannan yabon ya same ta.”

Abdullahi Sulaiman, ɗa ɗaya da marigayiya Fatima ta haifa

Shi ma Abdullahi Sulaiman, ɗan shekara 12, wanda ya ke ɗa ne ga marigayiya Fatima Sa’id, ya shaida mana irin halin da ya shiga na rasuwar mahaifiyar sa. Ya ce: “Tun ta na rashin lafiya na shiga wani hali na damuwa kuma ga shi yanzu Allah ya karɓi ran ta. Don haka zan rinƙa tuna ta a kowane lokaci a matsayin ta na uwa a gare ni.”

An dai yi jawabai masu ratsa jiki tare addu’o’i a wajen. Sannan an tara gudunmawa ta sama da N60,000 ga iyalan Fatima Sa’id. Sai kuma kuɗaɗen da aka ci gaba da tattarawa na gidauniyar da aka farfaɗo da ita, inda nan ma aka tara kuɗaɗe masu yawan gaske.

Allah ya jiƙan Bintu da rahama, amin.

Wani sashe na mahalartan taron

Loading

Tags: Bintu Daɗin KowaFatima Sa'id YakasaiGidauniyar Kannywoodrasuwataron addu'a
Previous Post

Gwamnatin Tinubu ta fito da tsare-tsaren bunƙasa tattalin arziki da samar da ayyukan yi, inji minista

Next Post

Raddin minista ga gwamnonin PDP: An ƙi wayon! Tinubu ba zai yi murabus ba

Related Posts

An naɗa Shehu Hassan Kano shugaban riƙo na MOPPAN
Labarai

An naɗa Shehu Hassan Kano shugaban riƙo na MOPPAN

June 3, 2025
MOPPAN ta ba gwamnan Kebbi lambar yabo a madadin ‘yan fim
Labarai

MOPPAN ta ba gwamnan Kebbi lambar yabo a madadin ‘yan fim

June 2, 2025
Ƙungiya ta ja kunnen gwamnatin Kano kan dakatar da finafinan Kannywood 22
Labarai

Ƙungiya ta ja kunnen gwamnatin Kano kan dakatar da finafinan Kannywood 22

May 20, 2025
Hukuma ta rufe gidajen gala a Kano har sai bayan Ramadan
Labarai

Gwamnatin Kano ta dakatar da haska finafinan Kannywood 22 a intanet da talbijin 

May 19, 2025
Labarai

Gwamnan Kano ya ɗauki nauyin ‘yan Kannywood 5 zuwa Hajjin bana

April 17, 2025
Sabuwa, matar Ɗanmaraya Jos, ta rasu
Labarai

Sabuwa, matar Ɗanmaraya Jos, ta rasu

March 28, 2025
Next Post
Duk da matsalolin da ake ciki, Nijeriya za ta ci gaba da bunƙasa – Minista Idris

Raddin minista ga gwamnonin PDP: An ƙi wayon! Tinubu ba zai yi murabus ba

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!