• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Monday, October 12, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

‘Yar tsohuwar jaruma a Kannywood, Fati Ladan, Raliya ta cika shekara ɗaya

by ABBA MUHAMMAD
November 8, 2025
in Ranar Murna
0
‘Yar tsohuwar jaruma a Kannywood, Fati Ladan, Raliya ta cika shekara ɗaya

Daga hagu: Fati Ladan riƙe da Ihsan a wurin bikin. A dama: Raliya Shettima (Ihsan)

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

DA yammacin shekaranjiya, Alhamis, 6 ga Nuwamba, 2025, tsohuwar jaruma a Kannywood, Hajiya Fati Ladan ta shiryawa ƙaramar ‘yar ta Raliya (Ihsan) bikin murnar zagayowar ranar haihuwar ta, inda ta cika shekara ɗaya a duniya.

An gudanar da bikin ne a farfajiyar gidan su da ke Yerima Close, kan Titin Jinya, daura da Titin Kanta, Kaduna.

Bikin, wanda aka fara da misalin ƙarfe 5:00 na yamma, ya samu halartar ƙawayen Fati da kuma matan abokan mijin ta, Alhaji Yerima Shettima da ‘ya’yan su.

Fati riƙe da Ihsan tare da sauran yara mahalarta bikin kafin a yanka kek

Da ya ke bikin na yara ne, mai gabatarwa, wato kakakin magana (MC), Ibrahim Alhassan ya gabatar da gasar rawa a tsakanin yaran. Inda za a kira namiji ɗaya, mace ɗaya a saka masu waƙa su yi rawa, wanda ya fi iya wa, shi ne wanda lashe gasar. Sai dai fa, mata sun ba maraɗa kunya, domin su ne suka lashe gasar da kusan kaso 95, ciki har da babbar ‘yar Fati, Humaira.

Bayan nan, sai kuma aka shiga fagen goge wuya, cin maƙulashe, inda kowa ya ci gasasshen naman rago da sauran abubuwan sha.

Daga nan kuma sai aka yanka kek tare da yin hotuna Ihsan da mahaifiyar, yara da kuma iyayen su.

Yara suna cashewa da rawa

Bayan kammala hotunan ne, sai Fati Ladan ta yi jawabin godiya ga dukkan mahalarta taron. Inda ta ce, “Ina godiya matuƙa da irin ƙaunar da ku ke nuna min. A duk lokacin da zan yi abu, ku na ƙoƙarin halarta. Na gode sosai. Allah ya maida kowa gidan sa lafiya.

Iyayen yara da yara sun nuna farin cikin su da wannan bikin, domin sun cashe sosai.

Mujallar Fim ta ruwaito cewa, an haifi Raliya a ranar Talata, 5 ga Nuwamba, 2024, a asibitin sojojin sama (Air Force Base), Mando, Kaduna.

Allah ya raya Raliya, ya kuma albarkaci rayuwar ta.

Loading

Tags: birthdayFati LadanRaliyazagayowar ranar haihuwa
Previous Post

Yadda CBN ke tallabe da tattalin arzikin Nijeriya, yayin sa farashin ɗanyen mai ke faɗuwar-‘yan-bori a kasuwa

Next Post

Mahaifiyar darakta Hafizu Bello, Gwaggo Hasiya, ta rasu ɗazu

Related Posts

Bikin auren Ibrahim Nuhu Gudaji da Zainab Adamu (Najlah): Marubuta sun yi wa Hadiza Nuhu Gudaji da Lubabatu Ya’u kara
Ranar Murna

Bikin auren Ibrahim Nuhu Gudaji da Zainab Adamu (Najlah): Marubuta sun yi wa Hadiza Nuhu Gudaji da Lubabatu Ya’u kara

October 10, 2026
Furodusan ‘Wata Shida’, Hayatuddeen Yakubu ya sake aure wata 7 bayan rasuwar matar sa
Ranar Murna

Furodusan ‘Wata Shida’, Hayatuddeen Yakubu ya sake aure wata 7 bayan rasuwar matar sa

September 28, 2026
An ɗaura auren Faɗima ‘yar furodusan Kannywood marigayi Nura Shariff
Ranar Murna

An ɗaura auren Faɗima ‘yar furodusan Kannywood marigayi Nura Shariff

September 7, 2026
Farha, ‘yar tsohuwar jaruma Halima Atete, ta cika shekara ɗaya
Ranar Murna

Farha, ‘yar tsohuwar jaruma Halima Atete, ta cika shekara ɗaya

September 5, 2026
Mawaƙi Abdool-Gaya ya samu ƙaruwar ɗa namiji
Ranar Murna

Mawaƙi Abdool-Gaya ya samu ƙaruwar ɗa namiji

August 24, 2026
An ɗaura auren mawaƙi Kawu Ɗan Sarki
Ranar Murna

An ɗaura auren mawaƙi Kawu Ɗan Sarki

August 23, 2026
Next Post
Mahaifiyar darakta Hafizu Bello, Gwaggo Hasiya, ta rasu ɗazu

Mahaifiyar darakta Hafizu Bello, Gwaggo Hasiya, ta rasu ɗazu

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!