A DAREN yau ne gidan rediyon BBC Hausa zai bayyana gwarzuwar gasar rubutun mata ta ‘Hikayata’ ta bana.
A bikin, wanda za a yi a ɗakin taro na Ladi Kwali da ke otal ɗin Sheraton a Abuja, za a fitar da marubuciyar da ta zo ta ɗaya da ta biyu da kuma wadda ta zo ta uku.
Bikin na bana shi ne karo na shida na gasar, wadda aka fara gudanarwa a cikin 2016.
A bikin, a kan yi jawabai tare da cin abinci da ɗaukar hotuna.
Mujallar Fim ta samu labarin cewa a taron za a nishaɗantar da taron da waƙoƙin fitacciyar mawaƙiyar nan da ke tashe, wato Khairat Abdullahi, musamman ma wata waƙa da ta taɓa yi wa BBC Hausa.
Ya zuwa yanzu dai BBC Hausa sun bayyana sunayen mata guda uku waɗanda labaran su su ka yi zarra a bana, kuma a cikin su ne za a bayyana gwarzuwar da masu bi mata.
Matan su ne Zulaihat Alhassan, Nana Aicha Hamissou Abdoulaye da Aishatu Musa Dalil.
Labaran su su ne: ‘Haƙƙi Na’ (a kan fyaɗe) na Aishatu Musa Dalil; ‘Butulci’ na Aicha Hamissou Abdoulaye, da ‘Rahmat’ na Zulaihat Alhassan.
Zulaihat da A’ishatu mazauna garin Kaduna ne, yayin da Nana Aicha ‘yar asalin birnin Maraɗi ce a Jamhuriyar Nijar.
Mujallar Fim ta ruwaito cewa wannan shi ne karo na farko da aka samu wata wadda ba ‘yar Nijeriya ba a cikin matan da su ka yi nasara a gasar.
BBC Hausa sun bayyana a wata sanarwa cewa za a ba wadda ta zo ta ɗaya a gasar kyautar tsabar kuɗi dalar Amurka dubu biyu ($2,000) da lambar yabo; za a ba ta biyu dala dubu ɗaya ($1,000) da lambar yabo, sannan za a ba ta uku kyautar dala ɗari biyar ($500) da lambar yabo.
BBC Hausa sun ce sun samar da gasar ‘Hikayata’ ne don ƙarfafa wa mata marubuta gwiwa da kuma haɓaka rubutu a harshen Hausa.
Malam Aliyu Tanko, shugaban Sashen Hausa na BBC, ya ce, “Gasar ta kasance wata turba ga mata marubuta wurin fito da batutuwan da su ka shafe su da zaƙulo hanyoyin matsalolin da su ke fuskanta. Kuma mu da ma fatan mu kenan.”
Ita kuma jagorar alƙalan gasar ta bana, Dakta Hauwa Bugaje ta Jami’ar Ahmadu Bello, Zariya, ta faɗa wa BBC cewa, “Kullum mata marubuta a ƙasar Hausa ƙara gogewa su ke yi saboda damarmaki irin wannan gasa da ake ba su. A bana mun ga labarai masu nagarta, kuma wannan na nuna cewa kwalliya na biyan kuɗin sabulu.”
Gwarzayen gasar ‘Hikayata’ na shekaru biyar da su ka gabata su ne kamar haka:
2016 – A’isha Mohammed Sabitu
2017 – Maimuna Sani Idris Beli
2018 – Safiyya Jibril Abubakar
2019 – Safiyya Ahmad
2020 – Maryam Umar
Hausawa sun ce ba a san maci tuwo ba sai miya ta ƙare, don haka ba a san wadda za ta lashe gasar ta bana ba sai a daren yau idan Allah ya kai mu.
![]()







