SHIRYE-SHIRYE sun yi nisa na fara aikin shirya fim mai dogon zango kan littafin ‘Daƙiƙa Talatin’ na shahararren marubuci kuma jarumi Ado Ahmad Gidan Dabino.
Shekara 11 kamfanin Gidan Dabino International Company ya shafe bai yi aikin fim ba, kuma jagoran kamfanin, Malam Ado Ahmad Gidan Dabino, MON, ya rikiɗe zuwa jarumi a cikin finafinai irin su ‘Juyin Sarauta’ da masu dogon zango irin su ‘Kwana Casa’in’.
A cikin tattaunawar da mujallar Fim ta yi da shi, Gidan Dabino ya bayyana tarihin ƙudirin shirya fim ɗin da inda aka tsaya da kuma inda aka dosa.
Ya ce: “Shi littafin na daɗe da rubutawa, da man asalin littafin na wasan kwaikwayo ne, kuma ana karanta shi tare da nazarin sa a yawancin jami’o’in ƙasar nan da kuma kwalejojin Ilimi kamar BUK, ABU Ɗanfodiyo da sauran su dai, duk za ka ga an shigar da shi a sashen koyon harsuna ana nazarin sa.
“Bayan nan kuma kamar shekaru uku da su ka gabata an samu wani lokaci da ni da Balaraba Ramat, Mustapha Adam Muhammad, Rabi’u Abu Hidaya da Bashir Mudi Yakasai mu ka ɗauki wannan littafi mu ka yi niyyar za mu mayar da shi wasan kwaikwayo wanda zai kasance ‘episode’ goma sha uku, wanda mun rubuta shi a matsayin minti talatin wanda a lokacin har mun samu wata jiha ma za ta ɗauki nauyi kuma matsaloli su ka shiga kafin kuɗin su shiga hannun mu, don haka sai ya zama aikin bai yiwu ba.
“To sai kuma a ƙarshen shekarar 2022, sai mu ka dawo da maganar za mu yi fim ɗin, amma sai mu ka ga a yanzu ba za mu yi shi minti talatin-talatin ba, za mu mayar da shi sa’a ɗai-ɗai ne. Shi ne a yanzu mun kusa kammala rubutun, sai ɗan abin da ya rage daga waje na.”
Da mu ka tambaye shi ko wani kamfani ko wata hukuma sun ɗauki nauyin shirya fim ɗin, sai babban furodusan ya ce, “To, a yanzu dai kamfanin Gidan Dabino ne zai shirya kuma na san mutane abin zai zo musu da bazata, domin rabon da kamfani na ya shirya fim tun shekarar 2011, ko in ce 20009. Kuma mun shirya fim ɗin ‘Sandar Kiwo’ amma bai shiga kasuwa ba saboda wasu cibiyoyi ne, irin su DFID da Bristish Council, su ka tallafa mana wanda fim ne da aka yi shi a kan kare haƙƙin mata da ke Arewa a kan Shari’ar Musulunci, wanda kamfanoni wajen goma su ka samu aikin cikin su har da kamfani na Gidan Dabino International Company wanda kuma bayan na shirya shi na zagaya da shi ƙasashe da yawa ina nuna shi: a London da Holland da sauran su. Kuma an yi masa fassarar Turanci da Faransanci. Kuma daga baya a 2011 mu ka sake shi a kasuwa, wanda kuma tun daga wannan kamfani na bai ƙara yin wani fim nasa na kan sa ba. Sai a yanzu mu ke so mu ke kuma fatan Allah ya ba mu dama a wannan shekarar ta 2023 littafi na mai suna ‘Daƙiƙa Talatin’ za mu mayar da shi fim mai dogon zango a matsayin sa’a ɗai-ɗai inda mun samar da na wata uku kuma duk da yake dai labarin buɗaɗɗe ne za mu iya ƙara shi mu ci gaba, in mun samu yadda mu ke so.”

A game da canzawar lokaci da ita kan ta masana’antar Kannywood ta yi, ko yaya zau ɗauki aikin a wannan sabon yanayi? Amsa: “To babu wani canji da za a ce an samu illa kawai shi wannan fim ne mai dogon zango. In ma akwai wani abu na sauyi da aka samu, sai dai na kayan aikin.
“Sai kuma wancan fim ɗin mutum ɗaya ne ya rubuta shi, wannan kuma mutane shida ne, duk da yake da man akwai labarin, na yi shi, amma buɗa shi ya zama labari dogo, to shi ne mutane su ka taru su ka yi shi. To shi ma akwai bambanci da za a ce wancan rubutun mutum ɗaya ne da kuma wannan na mutane shida ne.
“Don haka ba mamaki a samu ɗan bambanci saboda an ce hannu da yawa maganin ƙazamar miya.”
To ta fuskar jarumi ko su ma za a samar da wani canji? Sai ya ce: “A yanzu dai zan iya cewa a kan aikin ƙarƙare labarin mu ke, don haka ba zan ce ga yadda tsarin jaruman zai kasance ba. Amma dai abin da na sani, jarumar mace ce, don haka duk wacce za ta ja labarin sai mun tantance ta ko da ba za a ce sai mun yi gayya mun yaɗa a duniya cewa a zo taron tantancewar ba, za mu iya yi ta hanyar yadda ake aiko da saƙo, sai mu kira waɗanda mu ke ganin sun yi ƙoƙari, mu gwada su. Don haka zan bar masu aikin su samar da abin da ya dace; ba zan ce don kamfani na ya shirya fim ɗin sai yadda na tsara ba.
“Kuma ko ni a yanzu ba ni da tabbas a kan zan fito a fim ɗin ko ba zan fito ba. Kuma idan ka duba, tun da ake yin finafinai a kamfanin Gidan Dabino International Company, guda ɗaya na taɓa fitowa a matsayin jarumi, shi ne ‘In Da So Da Ƙauna’. Amma duk wanda za ka gani, ina yin fitowa ta musamman ne. Don haka ko da zan fito a cikin ‘Daƙiƙa Talatin’, to ba a matsayin babban jarumi ba kamar yadda a ‘Kwana Casa’in’ na fito ba, saboda labarin na yara ne, don haka jaruman za su kasance samari da ‘yan mata.
“Don haka masu ganin za a yi tuwo-na-mai-na ko cinye-du, abin ba zai zama hakan ba. Sai dai tunda abu ne na mutane da yawa ta yiwu a ɗan rakaɓa ni, don haka na ke yi duk finafinan da na yi a kamfani na guda goma sha takwas; ban taɓa fitowa a matsayin jarumi ba sai a ‘In Da So Da Ƙauna’ wanda shi kuma mun yi shi ne a 1994. Ka ga lokacin ma wasu jaruman ba a haife su ba. A yanzu sai waɗanda su ka shiga shafin YouTube channel na Gidan Dabino za su gani.
“Kuma abin da na ke so na faɗa, a yanzu, tunda yayi ake yi na finafinai masu dogon zango, ba za mu yi gaggawa ba, don an fahimci Kamfanin Gidan Dabino ya na yin aiki mai kyau, don haka za mu yi ƙoƙarin yin aiki mai ingaci wanda zai bayar da ma’ana wajen faɗakarwa da ilmantarwa da kuma nishaɗantarwa.
“Kuma in-sha Allah mu na fatan masu kallon da za su kalle mu ya zama kwalliya ta biya kuɗin sabulu. Su ma kamfanoni da za mu nemi tallace-tallace a wajen su wajen aikin da za mu gudanar, mu na da tabbas za su samu abin da su ke buƙata wajen samun sakamako mai kyau. Don haka mu na fatan su ba mu haɗin kai wajen ci gaba da gudanar da aikin har zuwa na gaba, saboda za mu nemi manyan tashoshi ne da ake saka finafinai mu yi tsarin da za su rinƙa haska mana, ba wai burin mu mu kai musu su saya ba.”
Idan masu karatu sun tuna, mujallar Fim dai ta buga sharhin ‘Daƙiƙa Talatin’ a wannan gidan yanar nata a ranar 2 ga Agusta, 2019.
Munajin daɗin Labaranku Allah yayi jagora