SHUGABANNIN masana’antar shirya finafinan Hausa ta Kannywood sun yanke shawarar za su shirya wata bita ta musamman domin wayar wa da ‘yan fim kai da ilimantar da su kan yadda ake amfani da soshiyal midiya da kuma irin haɗurran da ke tattare da ita.
Shugaban Haɗaɗɗiyar Ƙungiyar Masu Shirya Finafinai ta Nijeriya (MOPPAN), wadda ita ce uwar ƙungiyoyin Kannywood, Dakta Ahmad Mohammed Sarari, shi ne ya bayyana haka a daren jiya a Kano a wajen wani taro na musamman da aka yi don a sulhunta fitaccen mawaƙi kuma jarumi a Kannywood, Naziru M. Ahmad (Sarkin Waƙar Sarkin Kano) da Ƙungiyar Matan Kannywood (K-WAN) kan rigimar da ta ɓarke a tsakanin su.
Idan an tuna, Naziru ya wallafa iƙirarin cewa sai an kwanta da mace ake saka ta a fim a Kannywood, su kuma ƙungiyar K-WAN su ka ba shi kwana uku daga jiya da ya janye maganar ko kuma su yi ƙarar sa a kotun Musulunci a kan tuhumar ɓata suna.
A takardar sanarwa ga manema labarai da ya rattaba wa hannu a yau mai taken “Hirar Ladin Cima: MOPPAN Da AFMAN Sun Jagoranci Sulhu Tsakanin Naziru Sarkin Waƙa Da Sauran ‘Yan Fim”, kakakin MOPPAN na ƙasa, Malam Al-Amin Ciroma, ya yi bayani dalla-dalla kan yadda taron sulhun ya gudana da matsayar da aka cimma wa.
A takardar, wadda mujallar Fim ta samu kwafen ta, Ciroma ya yi bayani kamar haka:
“A jiya Litinin, 14 ga Fabrairun 2022 ne ƙungiyar MOPPAN da haɗin gwiwar ƙungiyar AFMAN da kuma Kwamitin Dattawan Kannywood su ka yi zaman sulhu tsakanin ‘ya’yan masana’antar da su ka sami rashin fahimta sakamakon hirar Hajiya Ladin Cima da BBC Hausa ta watsa kwanakin nan.
“Zaman da aka yi a zauren taron ‘Kannywood TV’ da ke Kano, ya samu halartar shugabannin ƙungiyoyin MOPPAN da na AFMAN da shugabannin ƙungiyar mata na ‘K-WAN’ da kuma dattawan Kannywood.

“Daga cikin dattawan da su ka halarci taron akwai Malam Auwalu Marshal, Mai’unguwa Ibrahim Mandawari, Ibrahim Gumel, da Kabiru Maikaba.
“Kai-tsaye, taron ya tattauna abubuwa da dama, wanda daga baya aka yi nasiha da jankunne gami da faɗakarwa daga malamai.
“Haka kuma taron ya yi bayanai na girmamawa ga Hajiya Ladin Cima da irin gudunmawar da ta bayar ga masana’antar fim, da kuma cigaba da lallashin ta da girmama dukkanin dattijan masana’antar da guje wa yin lafazi maras kyau a kan su.
“Shi ma shugaban AFMAN, Alhaji Sani Sule Katsina, ya jaddada kira wajen kauce wa maganganu barkatai a kafafen sadarwar zamani na soshiyal midiya.
“Ya ƙara da cewa, ‘Sai bango ya tsage ƙadangare ke samun wajen shiga.’
“A ganin sa, ‘yan fim ɗin ne ke ba wa ‘yan jarida da mutanen gari damar maganganun da ba su dace ba a kan su.
“An dai yi kira da a samar da bita ta wayarwa da ilimantarwa a kan amfani da soshiyal midiya domin guje wa irin haɗarin da za ta iya samarwa.
“An buƙaci a riƙa yi wa juna uzuri kuma a daina yin magana ko aika saƙonni cikin fushi.
“Bayan bayanai masu ratsa jiki da nasihohi da taron ya samar ne Ƙungiyar matan Kannywood, mai suna ‘K-WAN’, ta janye iƙirarin maka Naziru M. Ahmad (Sarkin Waƙar Sarkin Kano) a kotu, ta kuma nemi a guji yin lafuzzan da su ke taɓa darajar mata a Kannywood.
“Bayan wannan bayanan na ƙungiyar ‘K-WAN’ ɗin ne shi ma Nazir Ahmad ya yi tsokaci bisa rashin fahimtar bayanan sa da ba a yi ba, inda ya bada haƙuri kuma ya nemi a haɗa kai a samar da ƙa’idojin yin magana a kafafen sadarwar zamani.
“Hakan ta sa aka sake yin kira ga duk ‘ya’yan wannan masana’anta da su dakatar da yin duk ‘posting’ da ya ke da alaƙa da wannan saɓanin face bayanin sulhu.

“Shugaban ƙungiyar MOPPAN na ƙasa, Dr. Sarari, ya sanar da mahalarta taron cewa MOPPAN na daf da shirya taron bita domin wayarwa da ‘yan masana’antar da ilimantar da su yadda ake amfani da soshiyal midiya da kuma irin haɗurran da su ke tattare da ita.
“Mahalarta taron su ne:
1. Auwalu Isma’il Marshal
2. Hon. Mustpha Naburaska (S.A. to Kano State Gov. on Kannywood)
3. Mohammad Ibrahim Gumel
4. Salisu Muhammad Officer
5. Hadiza Muhammad
6. Abubakar Bashir Maishadda
7. Hannatu Bashir
8. Hauwa A. Bello
9. Kamal S. Alƙali
10. Mubarak Abba
11. Misbahu M. Ahmad
12. Naziru M. Ahmad
13. Muhammad Kabiru Maikaba
14. Alhaji Ibrahim Mandawari
15. Alhaji Sani Sule Katsina (Shugaban AFMAN na ƙasa)
16. Dr. Ahmad Mohammed Sarari (Shugaban MOPPAN na ƙasa).”


Allah yakara maku zaman lafiya da kaunar junan ku ameeen allah ya karama ku girma da dauka arayuwar ku ameen kuma ina San na din GA bada gudun muwata agareku