• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Tuesday, October 13, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Jarumar Kannywood, Hadiza Kabara ta yi taron tarewa a sabon katafaren gidan ta a Kano

by MUKHTAR YAKUBU
June 10, 2026
in Ranar Murna
0
Jarumar Kannywood, Hadiza Kabara ta yi taron tarewa a sabon katafaren gidan ta a Kano

Hadiza Kabara tare da ɗimbin jaruman da suka je domin taya ta murna

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

FITACCIYAR jarumar Kannywood, Hadiza Kabara, wadda aka fi sani da Lantana a cikin shirin ‘Daɗin Kowa,’ ko kuma Hauwa Adahama a cikin shirin ‘Gidan Badamasi,’ ta bi sahun manyan jaruman masana’antar da suka mallaki gidaje na alfarma.

Bayan shafe lokaci mai tsawo tana gudanar da aikin ginin gidan, jarumar ta samu nasarar kammala shi tare da ƙawata shi da kayayyakin zamani da na alatu domin samun ingantacciyar rayuwa.

A ranar Lahadi, 7 ga Yuni, 2026, ne aka gudanar da taron tarewar a sabon gidan nata da ke unguwar Fanshekara a Ƙaramar Hukumar Kumbotso ta Jihar Kano.

Taron ya gudana cikin annashuwa da nishaɗi, inda aka riƙa kunna tsofaffin waƙoƙin jaruman Kannywood da suka yi fice a zamanin su, lamarin da ya sa mahalarta taron suka yi ta rawa da walwala cikin farin ciki.

Hadiza Kabara a cikin sabon gidan ta da ta tare

Bayan haka, an shirya liyafar cin abinci ta musamman tare da gudanar da addu’o’i domin neman albarka, zaman lafiya da kariya daga dukkan wani sharri ga sabon gidan.

Haka kuma an yi wa Hadiza Kabara fatan alheri tare da taya ta murnar kammala ginin da kuma samun damar tarewa a cikin sa.

Daga cikin manyan jaruman da suka halarci taron akwai Mansurah Isah, Hadizan Saima, Yahanasu Sani, Fati Bararoji, Aisha Yola, Fati Sulaiman, Saddiqa Jibril, Ladidi Tubless, Aina’u Ade, Raihan Imam (Ƙamshi), Rahama Sirace, da sauran su.

An dai gudanar da taron cikin kwanciyar hankali da lumana, inda kowa ya watse zuwa gidan sa cikin farin ciki da murnar wannan babban cigaba da jarumar ta samu a rayuwar ta.

Loading

Tags: Hadiza Kabarasabon gidataya murna
Previous Post

Ali Nuhu ya sama wa yaron sa Nazifi Baƙo aiki a Gwamnatin Tarayya

Next Post

Hotuna: Taron taya Hadiza Kabara murnar tarewa a sabon gidan ta a Kano

Related Posts

Bikin auren Ibrahim Nuhu Gudaji da Zainab Adamu (Najlah): Marubuta sun yi wa Hadiza Nuhu Gudaji da Lubabatu Ya’u kara
Ranar Murna

Bikin auren Ibrahim Nuhu Gudaji da Zainab Adamu (Najlah): Marubuta sun yi wa Hadiza Nuhu Gudaji da Lubabatu Ya’u kara

October 10, 2026
Furodusan ‘Wata Shida’, Hayatuddeen Yakubu ya sake aure wata 7 bayan rasuwar matar sa
Ranar Murna

Furodusan ‘Wata Shida’, Hayatuddeen Yakubu ya sake aure wata 7 bayan rasuwar matar sa

September 28, 2026
An ɗaura auren Faɗima ‘yar furodusan Kannywood marigayi Nura Shariff
Ranar Murna

An ɗaura auren Faɗima ‘yar furodusan Kannywood marigayi Nura Shariff

September 7, 2026
Farha, ‘yar tsohuwar jaruma Halima Atete, ta cika shekara ɗaya
Ranar Murna

Farha, ‘yar tsohuwar jaruma Halima Atete, ta cika shekara ɗaya

September 5, 2026
Mawaƙi Abdool-Gaya ya samu ƙaruwar ɗa namiji
Ranar Murna

Mawaƙi Abdool-Gaya ya samu ƙaruwar ɗa namiji

August 24, 2026
An ɗaura auren mawaƙi Kawu Ɗan Sarki
Ranar Murna

An ɗaura auren mawaƙi Kawu Ɗan Sarki

August 23, 2026
Next Post
Hotuna: Taron taya Hadiza Kabara murnar tarewa a sabon gidan ta a Kano

Hotuna: Taron taya Hadiza Kabara murnar tarewa a sabon gidan ta a Kano

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!