Manajan-Darakta na Hukumar Shirya Finafinai ta Nijeriya (NFC), Alhaji Ali Nuhu, ya sama wa ɗaya daga cikin matasan da yake jagoranta da bai wa shawara, Nazifi Baƙo, gurbin aiki a Hukumar Kula da Harkokin Makamashi ta Nijeriya (Energy Commission of Nigeria – ECN).
Samun wannan aiki yana daga cikin nasarorin da ke nuna irin ƙoƙarin da Ali Nuhu yake yi wajen tallafa wa matasa domin su samu damar dogaro da kan su tare da gina kyakkyawar makoma a rayuwa.
Masu sa ido kan harkokin masana’antar Kannywood sun bayyana cewa wannan ba shi ne karo na farko da Ali ya yi amfani da tasirin sa da dangantakar sa wajen taimaka wa matasa samun guraben aiki da sauran damarmakin cigaba ba.
A cewar su, ya daɗe yana taka muhimmiyar rawa wajen buɗe ƙofofin alheri ga matasa da dama a fannoni daban-daban.
A tsawon shekarun sa a masana’antar shirya finafinan Hausa, Ali ya yi fice ba kawai a matsayin jarumi, furodusa da jagora ba, har ma a matsayin mutum mai kishin cigaban matasa.
Hakan ne ya sa mutane da dama suke kallon sa a matsayin uba kuma mai bayar da gudunmawa wajen bunƙasa rayuwar matasa da ƙarfafa musu gwiwa wajen cimma burin su.
Samun aikin Nazifi Bako a ECN ya sake bayyana irin rawar da Alin yake takawa wajen tallafa wa waɗanda ke ƙarƙashin kulawar sa, tare da ƙarfafa musu gwiwa su rungumi ƙwazo, jajircewa da neman ilimi domin samun nasara a rayuwa.
![]()







