SASHEN Nazarin Harshen Hausa na Jami’ar Tarayya ta Dutsin-Ma (FUDMA) ya shirya taron ƙasa da ƙasa na farko kan nazari da bitar ayyukan adabi na shahararren marubuci kuma mawaƙi, Alhaji Aminu Ladan Abubakar (Ala).
Taron, na tsawon kwana huɗu, an fara shi ne a ranar Lahadi, 8 ga Nuwamba, kuma ya kai har jiya Laraba, 11 ga Nuwamba, 2026.
An buɗe shi da gabatar da waƙoƙi, inda Aminu Ala ya jagoranci mawaƙa a ɗakin taro na FCE da ke Katsina daga ƙarfe 7 zuwa 11 na dare. Mawaƙa da dama sun baje kolin waƙoƙin su.


A jawabin sa, Ala ya gode wa Shugaban Jami’ar Tarayya ta Dutsin-Ma, Farfesa M.K. Othman, bisa girmamawar da suka yi masa domin fito da darajar sa a idon duniya. Ya kuma gode wa duk waɗanda suka mara masa baya wajen shirya taron, da mahalarta da masoya baki ɗaya.
Cikin mawaƙan da suka halarta akwai Fati Nijar, Shalelen Zariya, Sa’idu Ja’afar Singa, Fati Khalil, Miftahu da sauran su.
A rana ta biyu, an gudanar da babban taron a ɗakin taro na Hillside Royal Suites da ke cikin garin Katsina. An shirya shi da nufin nazari da tattauna gudunmawar da Ala ya bayar wajen bunƙasa harshen Hausa, adabi da al’adu, tare da duba tasirin ayyukan sa ga al’umma da cigaban harshen Hausa a wannan zamani.
Taron ya haɗa sarakuna, masana, malamai, masu bincike, marubuta da ɗalibai daga sassa daban-daban na ƙasar domin gabatar da ƙasidu da tattaunawa kan fannoni daban-daban na ayyukan adabin Ala.
Tun farko, shugaban jami’ar, Farfesa M.K. Othman, ya gabatar da jawabin maraba ga dukkan mahalarta, tare da bayar da taƙaitaccen tarihin jami’ar da nasarorin da ta samu zuwa yanzu.

![]()







