JARUMIN barkwanci, Alhaji Mustapha Badamasi Nabraska, ya bayyana cewa kafa ƙungiyar da ya yi mai suna ‘Shura People’s Party’ (SPP) ba wasa ba ne kamar yadda wasu ke zato, domin su na neman rajista a wajen Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) saboda ta zama cikakkiyar jam’iyyar siyasa.
A cikin ‘yan kwanakin nan an ga ɗan wasan na masana’antar finafinai ta Kannywood ya na wallafa hotunan sa a soshiyal midiya haɗe da tambarin SPP ɗin.
Yayin da wasu ke zaton jam’iyyar gaske ce a cikin tarin jerin jam’iyyun siyasa da ake da su a Nijeriya, wasu sun ɗauki abin a matsayin almara.
To amma kuma an fara ganin abin ya na neman ya zama kamar da gaske, musamman da aka ga Nabraskan ya fito da wasu sababbin motoci na yaƙin neman zaɓe tare da baza hotunan sa da na magoya bayan sa.
A cikin tattaunawar da ya yi da mujallar Fim kan batun, Nabraska ya ce SPP ba wasa ba ce.
Ya ce: “To gaskiya ba da wasa mu ke ba. Duk da ba mu da rajista da INEC, amma mu na fatan mu ma a yi mana domin mu samu a dama da mu a harkar zaɓe.

“Kuma mun sani a yanzu binciken da mu ka yi, babu wata jam’iyyar ‘Shura People’s Party’ da ta ke da rajista, don haka mu na fatan za mu samu nasara.
“Wannan ya sa a yanzu mu ke ta ƙoƙarin yaɗa ta yadda za ta shiga saƙo da lungu a duk faɗin ƙasar nan.”
Jarumin ya bayyana fatan samun damar a yi masu rajista don su samu su shiga zaɓen 2023.
A cewar sa, ya shafe tsawon lokaci ya na gudanar da wasu ayyuka masu manufa irin na wannan jam’iyyar tasa.
“A yanzu na ke so na ɗorar da ita a matsayi na na shugaban ta,” inji shi.
Da wakilin mu ya tambaye shi dalilin da ya sa aka saka mata alamar gidan zama, sai ya amsa da cewa: “Su manufofin wannan ƙungiyar ta ‘Shura People’s Party’ da mu ke so ta zama jam’iyya sun dace da hakan, domin idan mutum tsohon malamin makaranta ne ya gama aiki ya na gidan haya, to idan ya shigo ta zai samu ya mallaki gidan kan sa; idan tsohon gwamna ne, shi ma zai samu ya mallaka.
“Don haka mu na so ne mu kawo cigaba a wannan ƙasar domin mu ma mu samu a dama da mu a harkar cigaban ƙasa.
“Kamar yadda na faɗa, manufar mu raya jama’a da taimaka masu ta kowane ɓangare kamar ɗaukar nauyin marayu da samar da magani ga marasa lafiya. Kuma likitoci su ma shaida ne mu na zuwa asibiti mu na kai magunguna ga marasa lafiya.”
Nabraska ya yi kira ga jama’a da su ba da tasu gudunmawar domin a haɗu a cimma manufar da ya sa a gaba.